💖💫RUDANI💖💫 17

220 43 8
                                    




Ammaah ke zaune ita da wata mata, nan fa ta aika ha kira mata su Ilhaam dan su gaisa da wannan mata, bada jimawa ba kuwa sai gasu sun sauko, Ilhaam ta ganeta dan kuwa last zuwan su da Yaa Abu da suka zo gaishe da Ammaah taga matan wajen ta "Ina yini" ta fada ah nitse sannan ta karasa wajen matan "Lafiya qlau Ilhaam, Ya su Aliyu da matan sa?", "Suna lafiya" ta fada a nitse nan both Ash da Xeenerh suk gaisheta ah nitse suma, suna cikin gaisawan Aameer ya shigo "Girls yau zamu koma fa" yayi maganan kenan yaga matan, nan ya dan karasa ya gaisheta "Lafiya qlau Aameer ta amsa da fara'a, dan kallon ta yayi dan beyi zaton tasan sunan sa ba, gane hakan da tayi ne yasa tace "Ae duk Ammaah ta nuna mun pictures naku, nakan shigo na tayata hira ae" ta fada tana murmushi "Kuma ae ah gida na ma suna bin cases naka, magazines naka are everywhere" ta fada da murmushi "Toh bazaki ce su shiga ayi hidiman biki dasu ba wai gashi har yau zasu tafi?" Ammaah ta fada cikin Kanuri, dan kallonta Aameer yayi sannin wannan mata akwae fitina, banda fitina suna shirin tafiya tace wai zasuje biki "Zaku shigo koh? Bamu da nisa da ita Ammaah ae, we are neighbors, yanzu ma ganin na kwana biyu ban shigo bane ana hidima yasa nace barin leqo, yau za'a kawo amarya ma" ta fada tana murmushin ta na kullum "Aunty we in a hurry, next time please" Aameer ya fada ah takaice "Call me Mum, haka yarana ke kirana, kuma ae koh ah tsaye ya kamata ku shiga" ta fad'a jin wai sauri suke "Ki barni dasu, yanzu in sun tafi ae sai na gansu, basu san zuwa Borno koh kadan" Ammaah ta fada harda dan bata rai "Sweetheart, fushi bayi suiting naki" Aameer ya fada yana kallonta "Ae bani auren yanzu kam, na chanza miji, wancan mey shegen jiji da kan dai dashi za'ayi tunda shi bazai fito da mata ba" ta fada da Kanuri, wai fa Anwaar take nufi, gane hakan da sukayi ne ya sasu dariya "Mum, zamu zo bayan biki da yardan Allah" Aameer yayi assuring nata, dadi sosae taji yanda ya kirata da Mum kaman yanda ta bukata "Shikenan, Allah ya nuna mana lokacin" da Amiin suka amsa duka "Get ready please" ya fada sannan ya mike ya fita, itama Mum sallama tayi musu ta koma gida dan kuwa tabar mutane a gidan, tashi sukayi duk zuwa sama domin shiryawa, da yamma suka koma Abuja

Ba kowa gidan, sai Aameer dake zaune, Diva Vodka kadai ke kan accent table saidai ba shan yakeyi ba, da alamu dai shirin sha yakeyi. Da sallama Anwaar ya shiga amma dake hankalin Aameer yayi gaba baiko jiba, saurin karasawa yayi ya ture ya zube ah kasa, saurin matsawa Aameer yayi tareda dagowa dan sauran kadan yaji masa ciwo "How dare you?" Ya fada cikin bacin rai "Aure kake shirin yi amma ba cigaba?" Anwaar ya jefo masa tambaya, girgiza kai yayi sanin Anwaar ya iya wargaza masa plan, how on earth bazai barsa yayi rayuwa yanda yakeso ba kawae danshi Doctor "You are talking to Aameer, just don't cross the line" dan murmushi Anwaar ya masa kafin ya zauna "This is not good for your health-" kafin ya karasa magana Aameer ya tsaidasa cikin fushi "Doctor Anwaar is not the only Doctor, I can change you anytime I want" Anwaar bai sake ce masa komai ba jin abunda yace, dan kanshi ya sauko yace "Fatima called" kallon da Anwaar ya masa yasa ne ya gane bai fahimci wacece ba "Fatima nawa ka sani Doctor?" Anwaar yace "Many of course", "That Ilhaam's friend...oh sorry... I mean Fatima Shettima" yayi saurin gyara zancen sa, jin Anwaar yayi shiru yasa yacigaba "Tace you are not answering her calls" nan Anwaar yace "Yea, I was busy, and Ilhaam was there lokacin data kira, I can't answer it a gabanta, kuka zata fara mana, you knw how she is" dariya Aameer ya fara jin yanda Anwaar ke maganan "Kai kuma bakaso tana kuka ryt?" Ya fad'a still yana dariya dan yanda Anwaar ke nuna I don't care attitudes towards Ilhaam ke sa sa dariya dan yasan fa sarai Anwaar nasan Ilhaam, but he loves her as well, abunda yake tunawa kenan, kawae dai ya k'asa yarda da cewan Anwaar ya fisa santa "Doctor, I don't know how, but I fall in love with her tremendously" ya fad'a bayan ya gama dariyan nasa "You can't be there for two or more people, it's either Ashphert or Ilhaam, Sarah or Yesmin" shiru Aameer yayi kaman mey tunanin dan gaskia Anwaar yake fad'a, Toh amma mey ya kawo Yesmin cikin wannan magana "How is Mami's case going?" Anwaar ya tambaye sa jin yayi shiru "I am getting married, an closing case in kuma saboda ba wani strong evidence, but in some months za'a sake budewa" ya fad'a yana d'aga broken glass bottle da Anwaar ya fasa dan yasan Maa Laure ta dawo ta gani saita fara wa'azi, halan ma ta fadawa Ummi, Ummi kuwa is not the kind that is tolerating some kind of sh*t, zata masa ba d'adi, Anwaar na kallonsa koh tayasa baiyi ba har ya gama gyara wajen, dake ma bottle in ba babba bane

Ummi na zaune sai Ilhaam gefenta Anwaar ya shigo, shi duk bai zata tana wajen ba, dan karamin tsaki yayi tunawa da indai Ummi na waje toh wannan yarinyan koh wajen su Ashphert in ba'a fiye ganinta ba dole sai wajen Ummi, kaman zai juya kuma ya fasa ya karasa "Ummi am starving" ya fada tare da zama k'asa kan rug "Ga abincin Aya ta kasaci, sai kaci ae" ta masa nuni da plate na Ilhaam dake gefe ah rufe, kallonta yayi yaga bata ma kallonsa balle abun ya dameta, tashi yayi zai fita Ummi ta tsaidashi "Abincin fa?" Sai lokacin Ilhaam ta kallesa, saida ya harareta kafin ya dawo ya dauki plate in "Ke kun gaisa kuwa?" Ummi ta tambaye ta ganin bata gaishesa ba "Mun gaisa dazu ah waje" ta mata karya, tari ya fara da sauri ya zuba ruwa cikin cup ya fara sha jin karyan da Ilhaam ta zuba, yaushe ma ta gansa d'azun, shigowan sa wajen Ummi kenan gabadaya yau "Aci ah nitse dai" Ummi ta fada tana cigaba da packaging boxes in "Ka gama ka kawo mata magani wae kanta ke ciwo tun dazu" kallon Ilhaam yayi, yasan yanzu wani abun ke damunta tama Ummi karyan ciwon kai harda k'in cin abinci, jin yayi shiru Ummi ta maimaita masa "Baka jiba koh?" Yace "Aa, naji Ummi" Ummi na tashi Ilhaam tayi saurin mikewa itama har ta kusa fad'i "Kiyi ah hankali kar ki fadi" Ummi tayi saurin rike ta "Ki koma ki huta, keda kanki yake ciwo ina zakije?" Tace "Erm.. zansha ruwa-" tunawa da tayi da fridge in dake wajen tayi saurin rike baki "Aa, zanyi lalle ne... Aa kitso" duk ta daburce ta rasa wani karya zatayi, tsayawa kallonta Ummi tayi jin shirmen da take mata "Kan naki yabar ciwo ne zakiyi kitso?" Ta tambaya sanin sarai Ilhaam fa basan kitso take ba, ga kuma ciwon kai, jin tayi shiru Ummi tace "Toh koma ki kwanta" dakai ta amsa sannan ta koma Ummi kuma ta fice da boxes guda biyu "Nasan karya kika mata, kanki bayi ciwo" ya fad'a kaman an aike sa, shiru ta masa taki cewa komai, karamin tsaki yayi jin ta share sa, shifa zai iya share mutane amma shi kar yayi magana aki kulasa, ita kuma da gangan ta masa shiru tasan ba abunda ya isa ya mata Ummi na nan, so koh mey zata masa bazai damesa ba, banging kofan Aameer yayi har saida ta razana, zatasa ihu taga ya shigo ta koma gefe tana rufe baki "Sorry, I didn't mean to startled you" ya fada ganin yanda ta razana, sai lokacin ya kula da Anwaar, sake squeezing eyes nasa yayi ya tabbatar shine dagaske "What a day, Anwaar da Ilhaam suna zaune waje daya ba fad'a, dama haka kukeyi, amma baza kuyi ba" ji tayi kaman tasa musu ihu, mutanen da take avoiding yanzu duk sun hadu mata waje daya, jin sallaman Ummi yasa ta sauke ajiyan zuciya at least abubuwa sun ragu "Ummi gani" Aameer ya fada sannan ya zauna daga k'asa "Kaci abinci?" Kai ya gyada mata alamun Eh "Ina Al'ameen?" Ta tambaya dan bata gansa ba "He is on the way" ya amsa ah nitse, bata sake cewa komai ba saida Aameen ya karaso, cikin nutsuwa ya shigo da sallama sai coffee cup in dake hanun sa, gaisheta yayi ya zauna kusa da Aameer "I am not going to say much, saboda haka shidai aure Ibada ne kaman yanda kuka sani, sannan matan nan amana za'a baku su, ku rike amana, communicate before rushing to solutions, ah ringa hakuri sannan ah rage yawan fushi. "It was narrated by Ibn 'Abbas that: the Prophet said: The best of you is the one who is best to his wife, and I am the best of you to my wives." , "In Shaa Allah" suka amsa in unison "Ah kuma cigaba da haquri" ta maimaita musu maganan haquri" nan ma sunyi assuring nata zasu kiyaye, tashi Anwaar yayyi ya fice dan ya gama abunda yakeyi, Ilhaam kuwa na chan karshen gado ta kwanta "Yaa Ateekah tace za'a basu gifts" Aameen yayi maganan "Eh toh mey ya dace ku basu?" Ta tambaya "A carr" Aameer ya amsa da sauri, dan hararan sa tayi "Hope ba wancan manyan motan naka da kake hawa ba?" Dan murmushi yayi dan har yau baiga better car than Jeep ba "Sai ah basu wani daban" Aameen ya bata amsa "Toh duk yanda kukayi deciding" ta matsa tana t'aba tempreture na Ilhaam "Is she sick?" Suka tambaya ah tare ah tare hakan yasa suka juya suka kalli juna sannan back to Ummi "Ciwon kai, amma jikinta ba zafi" ta basu amsa, da sauri Aameer ya tashi ya fita, neman Anwaar ya fara jin akan wani dalili Ilhaam batada lafiya bazai bata magani ba, yana fita ya same sa parking space yana kokarin shiga mota, ganin Aameer yasa ya tsaya "What's it?" Ya tambaya ganin Aameer ya karaso "Kasan Ilhaam batada lafiya?" Kallon sa Anwaar yayi baice komai ba "Am asking" ya maimaita "Ba ko wani ciwo ake shawa magani ba, stress ne, tana hutawa shknn" ya bashi calm amsa, Aameer zai sake magana Anwaar ya tsaidashi da sauri "Why do think kanada ikon kulawa da ita? Let her live a free life" hakan yasa Aameer dariya "Thank God, bani kadai ne banda iko kanta ba, harda kai" murmushi kadai Anwaar ya masa ya shige mota abunsa





#RDN🤍

💖💫RUDANI💖💫Donde viven las historias. Descúbrelo ahora