💖💫RUDANI💖💫 41

135 26 21
                                    


_Nnamdi Azikiwe International Airport_

"I thought you were not coming... oh that's because am your husband now" yayi saurin amending, murmushi tayi hakan yasa yaja hanunta suka karisa mota, ganin driver'n beyi hanyan gidan Ba'a ba batayi mamaki ba, daga ido tayi ta kalli Anwaar kaman yasan tana kallonshi shima ya hakan yasa kawae tayi murmushi, ah haka suka karisa wani katon gida, babbane sosai dan banbancin sa da gidan Baa kadan ne, Anwaar yasan yanda take admiring gidan Baa so be it, gidan bene ne, ita ta rasa hadin en family'n su da storey building "Wow" ta furta, she will at least feel at home, zataji kaman gidan Baa take "Anwaar thanks for everything" har zatayi hugging nasa ta fasa tayi murmushin dole, is a remote control gate, tunda ganin haka tasan Anwaar will just make her live his private life, banda haka ba gateman koh daya, shiru dai tayi har suka karasa parking space. Mota daya ne wajen that's his MM, no blames yanzu ya dawo tasan yanzu duk motocin nasa ma zasu dawo. Ah hankali ta fito yanda wannan motan kuma yace ah sashi ah garage, basu shiga ta main door ba sai ya rike hanunta suka zaga ta chan wani kofa "This is too much Anwaar" ta fada ganin all the house keepers are men ga wannan kofan kuma fingerprint, kallonta yayi alamun what? "Tell me you are not anti-social" ta tambaya tana kallonsa, baice mata komai ba ya k'arasa setting abunda yakeyi yasa one of her finger. Budewa kofan yayi finally revealing one of the big living rooms, the color and everything just match Ilhaam's personalities, wabce hanunta tayi jin tayi masa magana ya shareta, bai ce mata komai ba yayi wani hanyan, ganin ya barta tsaye tabi bayansa dan kanta zuwa cikin wani living room in again, daga nan yayi sama, ita dai binsa kawae take ya nuna mata dakinta ta kwanta, parlor uku k'asa biyu sama so far dai suka wuce before finally arriving to one of the biggest bedrooms, koh bai fada ba tasan this is his room, dan wannan dakin ya mata girma and glass wall can never be her own. Yea it's not a complete glass wall gefe ne kadai amma dukda haka ita wannan dakin ya mata kama dana maza "I want to sleep" ta fada ganin bai kulata ba "Sleep here" ya bata amsa, bata sake ce komai ba ta zauna bakin gadon, towel ya dauka ya shige bathroom, adakin nashi ta zauna tanata game kasancewar batada abunyi dama karya take ba wani baccin da zatayi kawae sai ga conference call na Ashphert, kwanciya tayi kafin ta amsa "Lalle Ilhaam kinsan abunda Ummi ke shirin yi kuwa? Aure takeso Anwaar ya kara kuma da Teemerh fa, Ilhaam har yaushe kikayi auren da Ummi zata miki haka? Wannan mugunta kawae ba wani abu ba, dama chan ita da kanta kadai ta damu, kenan dama ita ta dade tanaso ta hada auren nasu. She's Shuwa and Teemerh's Mum also, dole dai sai anyi k'abilanci" Ashphert ta cigaba "Ni bazan taba bari Yayana ya aureta ba" Xeenerh tace "Aifa am not in support gaskia" jin sun fara Ilhaam tace "You guys should please calm down, nasan komai Ashphert, Ummi ta kirani ta fadamun karku sake hurting ina da zancen".... "Kinsani kuma still kika yarda mata?" Xeenerh ta tambayeta cike da k'in yarda "Toh Xeenerh Ummi ta nuna tanasan abun nan, nidai abunda nasani shine bazan taba iya zama da Teemerh ba, ta rabani da komai and now Anwaar?".... "Ki daina ganin laifin Teemerh Ilhaam, Ummi ita taja miki komai" Ashphert ta fada cike da tsanar abunda Ummi tayi "Bazan taba yafewa Ummi akan abunda tayi miki ba Ilhaam" ta fadi abunda ke ranta "Ashphert manners please", tsaki Ashphert taja jin abunda Ilhasm tace "Ke bansan wata iri bace Ilhaam, Ashphert na miki magana akan rayuwan aurenki kinaso ki gwada mata Ummi ta fita gaskia, idan har Anwaar ya auro yarinyar nan zakiyi nadaman komai, I repeat wallahi sai kinyi nadama" Xeenerh ta fada very disturbed "Ta turawa Yaa Humainah invitation card ita kuma ta saka a group, ashe baifi saura 3wks ba auren kina zaune saboda shirme ya miki yawa am out" Xeenerh tayi hanging sai din-din sukaji "Sai anjima Ilhaam sai kiyi tunanin abunda ya dace, idan har baki amince ba Anwaar bazai miki dole ba I trust his love bye, I love you" nan Ashphert ta kashe, jefar da wayan tayi yayi daidai lokacin da Anwaar ya fito ganin Ilhaam a dakin yasha mamaki, abun bey zama gaskia b a sai da yaga hawayen da takeyi "What's wrong?" Ya tambaya yana goge gashin kansa da towel in dake wuyanshi amma tsatsan tashin hankali koh lura da tattoo nasa batayi ba "Ashe aure zaka kara?" Ta fada da murmushin karfin hali tana share hawayen karya gani "Ban kai na sani ba kenan koh Anwaar?" Ta fada kukan na kokarin dawowa "Oh My Gosh" ya dafe kai, yau yasan abubuwa will be hard "No Ilhaam ba abunda kike tunani bane".... "Nasan komai Anwaar no need ka tsaya yimun bayani auren ka sauran 3 weeks right?" Yace "Ilhaam ki tsaya ki-" interrupting tayi "Ka amsa ni please Yes or No?" Yace "Yes sauran sati uku" ya amsa bitterly "Allah ya sanya alkhairi" tana fada ta tashi tabar mishi dakin, dan dama so takeyi taji daga bakinsa, yana kiranta taki juyowa "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'oun" kawae yake furtawa, Ilhaam kuwa hallway in tabi ganin wani daki kawae ta bude ta shiga abunta, sai da ya shirya tsaf yaje ya fara nemanta, bai sha wahala ba dan dakin data shiga baida nisa da nashi, tana kwance sai dai ba bacci take ba "Zamuyi magana please" ya fada bayan ya zauna gefe da ita "Ba wani maganan da zamuyi Anwaar, am not against ur marriage na amince da auren ka tun randa Ummi ta sanar dani so you don't have to worry" ta fada tana gyara kwanciya, karasawa kusa da ita yayi ya zauna tare da d'agota, tana kokarin komawa ya riketa "Wait" ya tsaidata "Ni ka barni bacci nakeji" ta wani bata rai "I promise you Ilhaam indai bakiso bazan yiba" saurin gyara zaman tayi jin abunda ya fada "Anwaar why Teemerh? Duk matan duniyan nan ka rasa wa zakace zaka aura sai Teemerh saboda kuci mun mutunci koh? Banga soyyayyan ku ba ae dole ka aureta na zama witness koh?" Shifa in Ilhaam ta fara shirmen ta kan Fatima k'asa magana yakeyi, inda tasan bayisan Fatima koh kadan toh data kwantar da hankalinta "Kinci abinci ne?" Sai da ta gama b'ata lokaci kafin tace "Banajin yunwa ka barni".... "Bawae zanyi aure dan na wulaqanta ki bane, you know I love you bazan taba yin abunda zai cutar dake ba" shiru tayi jin abunda yace, tunawa tayi ita fa yanzu bama matansa bane amma ta dake take masa ihu haka, toh in baiyi aure ba haka takeso ya zauna mata ba aure, ji tayi bata kyauta ba inta hana Anwaar yin aure "Nasani Im just afraid I might lose you, ina tsoro Anwaar" tayi maganan tana girgiza kai "And why? I love you Ilhaam har yaushe zaki gane hakan?" Rike hanunsa tayi "Anwaar kayi haquri nayi kokonto akan ka amma nasan kanason Teemerh" kallonta yayi baice komai ba dan komey ya fada ba yarda zatayi ba "I love you" ya fada sincerely "I love you too Anwaar" ta fada ah nitse, jawota yayi ba musu ta matsa kusa dashi ganin yana kokarin kissing nata tayi mishi wayo ta gudu, ba aure yanzu tsakanin su better ta kiyaye "Ilhaam am just trying to-" saurin cutting nasa tayi "To be romantic koh?" Ta karasa masa, girgiza kai yayi "Toh zo ki zauna bazan miki komai ba".... "Promise?"..... yace "Yea" batace komai ba ta koma kusa dashi saida kafin ta zauna hulan dake kanta ya fadi sai gashinta ya sauko, ba abunda yakeyi sai kamshi, tashi tayi da sauri ta dauki hulan zata mayar ya kwace "Ke wannan gashin naki baki yi masa kitso ne?"... "Toh ae cewa ake yayi yawa wae bazai kitsu ba" ta masa karya dan baso take ah tab'a ba, "Wancan yarinyan batasan kitso itama, amma tayi lokacin zatayi aure" kallonsa tayi jin wai sunan Ashphert in ke masa wuyan kira koh miye ohon sa "Ash ne wancan?" maida mata hulan yayi bece komai ba ya kama hanunta zuwa gaban vanity, sake cire hulan yayi "Mey zakayi kuma?" Yace "Kitso zan miki" dariya ta fara jin abunda ya fada, so kawae yake yasa mata kai ciwo "Toh ae baka iya ba" yace "Who told you ban iya ba? Bari kiga kedai kawae kiyi shiru" yanda yace haka tayi shiru ya dunga murda mata kai, "Ouchh" ta fada jin yanda yake mata zafi, da sauri ya sake kan nata "Ya ka bari toh?" Ta tambaya tana dariya "Kinaso kimun kuka, kuma kinsan baniso kina kuka" tace "Ni ba kuka zanyi ba yunwa nakeji" kaman ba ita tace batajin yunwa ba "Toh muje kici abinci" daga ido tayi tana kallonshi, tanasan ce masa batayi girki ba, saidai ba musu ta maida hularta ta bi bayanshi, nan ta hango abinci kan dining tuni tayi wajen ta zauna saidai kafin ta fara chi taga tarin akwatuna lodi guda a gefe, kallon Anwaar tayi ta sake kallon akwatin "Wannan fa?" Ta tambaya dan kuwa taga akwatunan aurenta ah daki "Erm..sorry Ilhaam, na fadan kishiya ne, haka dai Yaa Ateekah tace" dariya ma maganan nasa yaso bata, gane bey na san na miye ba, bey sani ba kuma dan Ummi ne tace ya kawo mata, saboda an aika kaya masu yawa gidan su Teemerh wanda yafi wanda akawa Ilhaam na biki, wai su Shuwa komai sai anyi ba lissafi "Amma auren mu koh wata beyi ba kuma ka mun fa, meyasa kayi wannan?" Ta tambaya dan ita abun ba burgeta yayi ba "Just to tell you how much I love you, kici abinci", tace wow "I can't imagine life without you" ta fada da murmushi, abun na damunta amma ta kasa nuna masa "Same here" ya bata amsa tare da jan kujera ya zauna "So karka sake ordering abinci daga yau ni zan nayi" tayi maganan bata ma kallon sa "Ke kin iya girki ne daman?" Ya fada saboda neman tsokana dan shi baisan fa bata iya ba, shi gani yake ba wani excuse da mace zata bada, tunda Yesmin ta iya girki toh kowa ta iya kawai, jin abunda ya fad'a yasa ta fara tunanin rayuwanta, full of regrets. Ta kare rayuwa zuwa boko da Islamiya, bayan wannan in an tambayeta rayuwanta na farko bata yi komai ba, inda yanda ta biyewa Teemerh da Ashphert haka ta biyewa Xeenerh da halan ta iya dan duk cikin su ba wacce taba rayuwanta mahimmanci kaman Xeenerh, let say Ashphert here ta tsalle ke but that doesn't mean Ilhaam da Teemerh zasuyi abunda ransu keso, shiru ta masa kafin tace bata iya ba su fara d'iban en kallo dan koh sama da kasa zasu hade Anwaar bazai dauki maid mace ba, ya gwammace ya shiga kitchen da kansa, tana kai abincin bakinta taji amai da sauri ta tura gefe, har zata tsaya cikin basin ta fasa, da gudu tayi toilet, binta yayi yaje ya riketa saida ta gama ya wanke mata baki suka fito, kan gado ya kaita ya kwantar da ita tareda zama a gefenta ya rige hanunta, kokarin kwace hanun tayi saidai bey sake ba "You're sick shine baki fadamun ba?".... "Lafiya na qalau" tayi mishi karya kuka na kokarin zuwa ta daure dai "But you look sick Im a doctor kin manta? Zan gane in bakida lafiya" dauke idonta tayi a kanshi tana kokarin kwace hanunta daga rikon da yayi mata dan baso takeyi suja maganan ba, kin sakewa yayi still "I'm your husband laifi ne in na rike hanun ki?".... "Ni baniso ana tabani ne shiyasa" ta fada kaman zatayi kuka "This is strange" ya fada a hankali, sake hanun nata yayi, blaming no one but Aameer, she is traumatized, dole bazata so ana rike ta ba, she might think everyone will take advantage of her "Okay don't cry huh? in kawo miki abincin nan?".... "Ni na koshi yanzu madara zan sha" kallon mamaki ya bita dashi "Milk?" Ya maimaita dan yasan Ilhaam prefer chocolate thousand times kan milk "Eh" ta amsa "Ilhaam are you...?" Sai kuma yayi shiru be k'arasa ba, dan bata ma jisa ba "Ilhaam must be pregnant" ya fada a ranshi saboda yasan Ilhaam bata shan madara sai anyi dagaske "Anwaar mana" Ta dawo dashi daga duniyan tunanin shi "Ok" ya tashi ya sauka kitchen domin dauko mata madaran, saidai kafin ya dawo har tayi bacci, rufewa yayi ya ajiye ya karasa wajenta ya ja mata blanket, yakai 30secs yana starring innocent and cute face nata dake glowing saboda gyaran da jikinta yasha, saida ya rage lights zuwa amber dim light kafin ya wuce dakin sa, wanka ya shiga yayi yazo ya kwanta, har ya fara bacci Ilhaam ta shigo ta kunna masa lights hakan yasa ya bude ido, ganin Ilhaam ya tashi ya zauna "A-a- Anwaar can I sleep here? I have a nightmare" tayi stuttering, duk ta daburce tana bi tana goge hawayen nata "Yea, sure" ya amsa yana mamakin wani irin mafarki tayi "You can sleep here" ya mata nuni da kan gadon sannan ya koma kan sleeper chair, hawayen ta cigaba da sharewa ta karasa kan gadon bayan tace Thank you, baccin kirki bai yisa ba ranan sai asuba koh da ya tashi mamaki ya sakeyi saboda Ilhaam batanan unlike dazu da dare, dama chan fa mafarki tayi ta razana shiyasa tazo dakin nasa, alwala ya shiga yayi sannan ya tafi masallaci yana dawowa daga masallaci ya wuce dakinta, akan abun sallah ya sameta kanta na jingine ajikin gado ta fara bacci, dagata yayi ya sata akan gado sai a lokacin ta bude idon da suka cika da bacci ta daura masa su, "Good morning my girl", murmushi tayi shima ya mayar mata da murmushin "How're you feeling?" Tace "Better" Nuni ta mishi da gefenta "Ka kwanta koh baka jin bacci?" Sanin jiya baiyi bacci ba, duk motsi in tayi sai yace how are you feeling? "Toh barin zo" tashi yayi ya fita sai gani tayi ya rage kayan jikinsa, wajen data nuna mishin yazo ya kwanta, tana ganin ya kwanta ta dauki waya, karban wayan nata yayi ya ajiye a gefe "Let's take a nap" tace "Toh dan bani kayi haquri, Yaa Atee ce dama nace mata ka dawo kuma yau mukeso mu dubasu duka zanji koh tana nan".... "Zaki iya fita yau ne?"...."Yeah why not nifa lafiyata kalau"...."Toh naji kiyi bacci zamuje In Shaa Allah" yasata baccin dole, cikekken 6mins batayi ba bacci ya dauketa bayan ta yanke shawaran fada ma Anwaar gaskia game da cikin ta, Anwaar kam beyi bacci ba, toh wai ina yaci na bacci Ilhaam is not his wife, bai tabbatar tanada ciki badai amma duk alamu sun nuna fa, bacci sosai Ilhaam tasha dan sai 8:56am ta tashi tayi wanka dan already Anwaar bayi dakin, bayan ta fito ta shirya tsaf tana kokarin fita saiga Anwaar dauke da breakfast nata kaman yasan ta tashi "Aww you are so sweet" ta taimaka masa "Anything for you" ya fada yana murmushi, zama tayi da niyyan ci dan kamshin ya mata sosai amma tana kaiwa baki sai amai da sauri ta tashi yana biye da ita sukayi toilet in, duk tausayinta ya kamasa saida ta gama ya wanke mata baki suka fito, kan gado ya kaita ya kwantar da ita tareda zama a gefenta ya rike hanunta, kokarin kwace hanun tayi saidai bey sake ba, zai tashi tayi saurin rike hanunsa "Am sorry Anwaar" sai kuma ta tashi ta zauna "I can't hide it from you anymore nasan zaka gane koba yau ba!" Kallonta yayi cike da tausayi "What are you trying to say? Ya tambaye ta ah nitse "I'm.....am pre...am pregnant Anwaar" saida taji hawaye ya sauko mata, saidai to her surprise beyi mamaki ba koh kadan, sai kallonta yake yana smiling "Bakaji abunda nace ba?" Ta tambaya ah tsorace "Naji" ya fada sincerely "So we're becoming parent soon?" Kallon mamaki ta masa jin abunda yace "Amma kasan...." Sai kuma tayi shiru "Amma dai kasan ba cikinka ban.." kafin ta karasa ya rufe mata baki "What're you trying to say Ilhaam? Your Baby is not mine or what?".... "Aa Anwaar baka fahimta ba wannan cikin na Aameer neeeee!" Ta fada kukanta na kara tsananta, saurin hugging nata yayi yana bata haquri ganin taki yin shiru yace "Ilhaam nasan komai, you don't have to worry trying to explain yourself, I trust you and your morals, nasan bazaki taba abu irin haka ba" Dago kai tayi tana kallonsa da mamaki "Ka sani kuma still ka aureni? Anwaar I've no pride?".... "Shhhhh and sleep Ilhaam you need rest" girgiza kai tayi tasan wayo yakeso ya mata ya sata bacci "Auren mu fa?" Tayi tambayan kaman bata san yi "No one will know about this Ilhaam, I promise you and I will stand by you, I love you so create time for something not crying" kwace hanun ta tayi jin abunda ya fada zata bar gadon yayi saurin riketa "Let go of my hand" ta fada tana jin haushi, shifa baisan koh ya fadi abunda ba daidai ba "Ilhaam na fadi abunda ba daidai bane?" Shiru ta masa daga farko ganin shirun baida amfani ta bude baki "Saboda zakaje ka auri Teemerh ae dole ma kace haka. You love her kuma gashi ka sameta nikam ae bakada damuwa dani. Ummi ce ta aura maka ni forcibly" tayi maganan da ba komai cikin sa sai kishi, shiru yayi yama rasa mey zaice ta yarda dashi "Dole kayi shiru ae kasan bakada wani abun fad'a" sannan ta juya ta kwanta sai tunani takeyi, yanzu ya gane dalilin ihun da take masa, she is pregnant, ganin tayi bacci ne ya tashi yayi daki, missed call na Ummi ya gani hakan yasa ya kirata, nan ta shaida masa lalle yaje gidan su Fatima, tunda ae biki ya matso koh akwae abunda take bukata, bashi ya tashi zuwa gidan su Fatima ba sai dare
***


💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now