Page one and two

2K 89 4
                                    


🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce ❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

    
            

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI INAFATAN ALLAH YA TEMAKENI YABANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI DANA DAKKO BA AKAN WANI KO WATABA KAGAGGEN LABARINE INAFATAN ALLAH UBANGIJI YABANI IKON YINSA CIKIN AMINCI KUBIYONI DAN KUGA IRIN SALON DAYAZO DASHI*

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA NAMTARY UMMYN ABBA ALLAH YA JiKANKI YASA MUTUWA TAZAMO HUTU A GAREKI, ALLAH YABA8 MIJINKI DA YARANKI DA DUK WANNI MAKUSANTANKI HAKURI DA JURINYAR RASHINKI😭🙏🏻'''

Page 1-2


Yanzun ta samu ta gama azakar tana son ta koma baccin safe koda na minti goma ne, amman ina hayaniya mutanan gidan su ba zasu barta tayi wanann bacci ba gashi tana jin kanta nayi mata ciwo rabon ta da bacci tun jiya karfe ukun dare da ta tashi sallahr dare..

"Ohni Rumaisa, har sai yaushe mutanan gidan nan zasu san ba kyau shiga hakin mutum, mtsssss ina anfani ace gida baya yin shiru har sai in kowa ya kwanta sannan zaka ji gidan shiru, sai ka Aku haba, ni dai abun ya fara damuna wallahi."

"Aaha Rumaisa ke da wa Kuma,  naji kina ta maganganun? "Mama nida mutanan gidan nan mana, "To Rumaisa in ba hakuri mai za muyi, ai matsalar *GIDAN HAYA* kenan, yanzun fa fada ake da Lami da Halimai, wai Lami taga Halimai tana dibar mata abinci, Kuma ita abincin mijinta ta ajiye ma nashi,  kinji asalin fadan."

"Kai gaskiya Halimai bata da hali Mama,daga ita har mijinta, ni shiyasa bani son zaman tsakar  gidan nan, duk wata gulma daga jikinsu take fitowa, daga Halimain har ita Lami din, yau dai tasu ta hada su shiyasa aka jisu a cikin gidan nan."

"To ya zamu yi Rumaisa ai sai hakuri, shiyasa Babanki shima baya san yaga muna zama cikinsu, yace halinsu bai ye mashi ba."....cewa Rumaisa tayi."ai Mama basu da hali ko daya, sun sama kowa ido a gidan nan, bayan gidan nan gidan mutane ne, daki goma ne a cikin gidan Kuma kowane daki akwai Wanda suke zaune cikin su, ai dole ko wace gulma a unguwar nan ta fito daga gidan nan."

"Gidan nan Mama kinga sana'a akeyi kala kala, da masu kitso da masu kunshi da masu wankau, harda dai basu yin abinci sai dawa ba dole ayi gulma ba a gidan nan."

Itada Mama bata ce komai ba, tana tunanin halin yan gidan nasu.

Niko nace ai *GIDAN HAYAR* kenan Mama, tana cikin tinanin taji Rumaisa na yi mata magana.

"Yauwa Mama yau da wuri zani tafi gidan aiki na, saboda ina son nadawo da wuri na wuce Isilamiya, bari ma na tashi kawai na shiga wanka, Mama zo ki duba man kar wani ya shigo man ina cikin wanka kinsan dabi'ar gidan nan ce, bayan mutun yasa ba shi daya ke da gida ba."... Cewa Mama tayi."Yo ko kai daya ke da gida ai kace akwai kowa in ba kowa sannan kashiga, balle wannan gida ba naka ba *GIDAN* *HAYA*, ai Rumaisa hakuri zamuyi da halin yan gidan nan, tashi mu tatafi ki samu ki shiga kina fitowa nima na shiga, daman Babanki Shi tunda asuba yake wankashi."..."To Mama."

Haka su Rumaisa suka tashi, suka fita tsakar gidan, suka ebi ruwa a rijiya sannan suka kama hanyar kewaye, amman kafin su ida shiga Lami ta taso wai ta rigasu niyar shiga zuwa tayi ta nemo buta, haka su Rumaisa suka kyaleta basu kulata ba, ita ko Lami taso su biye mata suyi fada tunda uwar safiya sai kace suma kalar tane..

Bayan Lami ta  fito, Rumaisa ta fara shiga sannan Mama ta shiga suna gama wa suka koma dakinsu Rumaisa ta shirya cikin wata yar atamfarta tasa hijab dinta ta kama hanyar zuwa gidan aikinta..

"Assalama Alaikum."

"Amin wa'alaikumus Sallama."... "Aunty ina kwana."! ?..."Lafiya lau Rumaisa, Antashi lafiya."!?..."Lafiya lau Alhmdulh.".."ya Mamarki take."!?.."Duk suna lafiya Aunty."..."To Alhmdulh, Amman yau Rumaisa kin zo da wuri.".... "eh Aunty inason nagama da wuri zanyi wanki sanann na wuce Isilamiya."..."ok Allah sarki, Allah ya taimaka."..."Amin Aunty."

Nan dai Rumaisa ta fara yin moping din main parlour, sannan tayi na dakin Hajiya Maryam, ta wuce ta gyara kitchen, sai tayi wanke wanke, tana gama wa, ta taya Hajiya Maryam sauwar abincin rana,suka jerashi a dining sannan Hajiya ta sawa Rumaisa nasa ta, tayi mata godia ta wuce gida, tana jin dadin aiki gidan Hajiya Maryam, dan ita Hajiya mutun ce mai mutunci bata da wulakanta Dan  Adam, duk dukiyar mijinta da yake da ita  haka baisa ta ji warin tallkaba...

"Sallama Alama Alaikum, Sannunku da hutawa mutanan gidan nan."... Cewar Rumaisa da dawowarta kenan daga gidan aiki.

Ai Lami cewa tayi."ahaiye mun de mungode Allah bamu zuwa gidajen mutane zalamar Abinci, ko Hindatu."?.... Itaam Hindatu cikin wulakanci ta fara dariya tana cewa"aiko dai Lami, yo Allah ya bamu wadatar zuci,  mai zamuyi gidan wasu kwakwa, Halimai."?.... Ta jefa ma Halimai tambayar taba dariya raini, itama Halimai cewa tayi."Uhmmm kedai tayani gani Hindatu wai shine aka kira da *ANKI CIN BIRI* , *ANCI DILA* , hahahaha, yo ni  Halimai Allah ya sawaka man da zuwa kwakwa gidan mutane, ai na gwanma ce na kwana banci komai ba."... Ta karasa maganar itama tana kallon Rumaisa tana dariya.

Cewa Rumaisa tayi cikin ɓacin rai."Eh ai shiyasa naji ku yau da safe kuna fada a kan abinci, nagode ma Allah ni *Rumaisa* da nike zuwa kwakwa gidan mutane, Alhmdulh tunda bani satar abun wani, kin ga ko da *MUGUWAR RAWA,* *GWAMMA KIN* *TASHI* "

"Kam ubancan, ubawa kike gayama magana haka"? Cikin kukuwa da ɓacin rai tace."Wanda ya tsargu da kashi baki ji masu karin magana na cewa *IYA GANI, IYA KYALEWA,BA* dan haka in dan zaku yi abun ku karda ku sake ku sanyo ni, domin ni ba kyaleku zanyi ba kunji nagayama maku, baku iya komai ba sai *ZAMAN* *BANZA* da *SA* *IDO* aikin kenan an dai ji kunya wallahi."

"Ke Rumaisa, wai maiye haka?  bana ce maki karda na sake jin kin biye ma su ba?  kuna cece kace, sai kace wasu abokanki?  baki san dai kiga bakina yayi shiru ko."!?... Cikin firgici tace."Aah Mama ba haka bane, amman dan Allah kiyi hakuri ba zan Kuma ba."... Cewa Mama tayi."bani zaki ba hakuri ba su zaki ba hakuri, su da kika dage kina ta gaya masu magana san rainki sai kace wasu kawayenki, ai ko ba komai sun girmaiki, maza basu hakuri kafin raina ya baci."

"Su Lami dan Allah kuyi hakuri ba zan Kuma ba.".... Cikin fada Lami tace."da hakurin ya mutu sarakar nawa kika bada? fitsaraira marar kunya kawai."... ita dai Rumaisa bata ce komai ba ta shiga warta daki ta barsu tsakar gida sunata aikin jaraba..

"Rumaisa."... "naam Mama."... "daga yau itace rana ta karshe da zan maki magana a kan fadan da kike da su Halimai, taya zaki tsaya kina biye masu? Kuma kin san sarai mutanan nan ba wani tunani ga resu ba?  dan da kowa ma fada suke tunda suke yi da mazajensu dan haka daga yau kar na sake ji.".. "insha Allah Mama bazaki sake ji ba, bari na tashi nayi Wannnan wanki kafin lokacin Isilamiya yayi."

"To shikenan Allah yayi maki albarka, ya baki miji na gari."... "Amin Mama."

Bayan Rumaisa ta gama yin wanki, ta shirya ta wucewarta Isilamiya tana dawo wa ta tadda Mama tana aikin Tuwan dare, nan ta cire hijab taje ta kama ma Mama aiki, suna gama tuwo da miya, suka diba suka bama mutanan gidan sannan suka kwashe tuwansu suka ajiye a daki, suna jiran Baban Rumaisa ya dawo suci abincin, da yake tare suke cin abinci dare, bayan ya dawo suka ci abinci sukayi sallah kowa ya kwanta yayi bacci....



*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now