31&32

287 32 3
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
  _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar
da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
___________________________________

      
            
*am back nagode sosai da addu'oinku, sannan kuma jiki da sauki Alhmdulh, karku manta yanzun muka fara wasan ku cigaba da biyoni a cikin a gidan haya kuma kuna surburbuɗo man ruwan comment💃❣️*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_31&32

"Haka mukai ta rayuwa hankalinmu kwance, ba abunda ke damun mu, kuma kullun sai Babba ya  kai balance din ci nikin da yayi wajen Alhaji Sanusi."
"Ina primary 5,mama ta haifaman kani, ranar Suna Yaro yaci sunan KHAMIS."
"Khamis sunan yayen Babane, aka sa mashi , wanda suka tafi suka barshi shi daya, bayan anyi sunan khamis da kamar wata biyu, sai Mamana ta fahimci khamis bai da lafiyar kai, nan ne fa hankinta ya fara tashi."
"Saboda taga kullun kai shi girma yake yi, nan suka fara zuwa chemist, aka bashi paracetamol na yara, nan aka fara bashi magani, aga ko za'adace."
"Khamis yana da wata shidda a duniya , amman bai fara zama ba, balle akai da sa ran rarrafe, ga kuma kanshi sai girma yake."
"Don ba'a goya shi da zane daya sai biyu ake goya shi, daya ake tare kanshi sai dayan kuma a goya shi."
Kallon Fadil Rumaisa tayi sannan tace."Yaya Fadil lokacin sallah yayi."shiru yayi na wani dan lokaci sannnan yace."to Ruma, muje muyi sallah ki cigaba ko."?murmushi tayi tana wasa da zoben hannunta sannan tace."Aah sai gobe indan Allah ya kaimu."cewa yayi."A'ah Ruma please ki ida man yau mana."cewa tayi"Yi hakuri Yayq Fadil, amman ya dace ace na koma gida yanzun, Mama nacan tana jirana dan Allah ka bari dai sai goben."cewa yayi."to shikenan Allah ya kaimu, ammam ba dan naso ba zaki tafi Ruma, dan kawai Mama itama tana bukatar ki shiyasa zan barki ki tafi."cewa tayi."hakan ma ai nagode sosai."kallonta yayi sosai yakejin tausayinta balle yanzun da ya fara jin labarinta cewa yayi."gaskiya labarin ki yana da ban tausayi, Allah ya kaimu goben ki iya da bani labarin, ina san naji  ina khamis yake, don banji kina kiranshi ba."cewa tayi tana mai miƙewa tsaye."Allah ya kaimu zaka ji yanda komai yake, sai da safe."cewa yayi."To shikenan, amman bari na dawo mosque sai na kai ki gida."cewa tayi."to shikenan, kafin kadawo nima nayi sallah."
Bayan Fadil ya dawo daga mosque ya dauki Rumaisa ya kai ta, yace ta gaida mashi Mama, sannan kuma zasu yi waya.
Tana shiga cikin gida ta tadda Mama tana jin redio, zaune ita ɗaya zaunawa tayi kusa da Mama sannan tace."Mama yau bacci nike ji sosai, gashi Baba bai shigo ba har yanzun."kallonta Mama tayi sannnan tace."ai kin bari ayi isha'i sannan ki kwanta ko kasa uwar yan bacci."? Sunburo baki tayi sannann tace."Mama ai cewa nayi na gaji shiyasa zani kwanta, kuma ba naji ana kiran sallahar ba."murmushi Mama tayi sannan ta kalleta tace."tashi kiyi sallahr to, tunda baki cin abinci sai ai ta bacci."tashi tayi tana cewa."na koshi naci abinci a gidan Mami."tafiya tayi tayo alwallah sannan ta dawo tayi sallah, kallonta Mama tayi sannan tace."je kiyi baccin ki Rumaisa, ba yanzun Babanki zai shigo ba."cewa tayi taba mai tashi tsaye."to Mama sai da safe."har ta fara tafiya taji Mama na cewa."Au Rumaisa na manta ban gaya maki ba, gobe Maman A'I zasu tashi su koma gidan su na kansu."dawowa tayi ta zauna cikin nuna farin ciki tace."Masha Allah, gaskiya ina taya ta murna, sunyi gidan kansu, su huta da zaman GIDAN HAYA, Muma Allah ya nuna mana randa zamu yi gidan kaimu."cikin murmushi Mama tace."Amin Rumaisa."tashi tayi tana cewa."bari na kwanta Mama, gobe nayi mata murna."cewa Mama tayi."to sai Allah ya kaimu."..."Allah ya kaimu."
"Washe gari, bayan Rumaisa ta gama shirya wa ta biya tayi ma Maman A'I murna, ta wuce gidan aikinta...
Bayan sun gama yin komai ita da Fadila, suka kira Fadil suka ci abinci suka maida komai ma zauninsa, sannan ta wuce part din Fadil...
Sai da ta gama gyara part din tas, dan harda bedsheets ta chanza ma duka beds din da suke cikin part din nashi, ta wuce kitchen ta hada mashi tea ta juye a flask, ji tayi yana cewa."Ruma don Allah ki ajiye wannan aikin ki zo ki cigaba da bani labarin, baki san yanda na kosa ba."cewa tayi, tana mai tahowa."to gani nan, fara shan tea din mana sai mu cigaba."kallonta yayi yana murmushi kashe mata ido ɗaya yayi sannan yace."to bani nasha, amman Ruma kin iya haɗa komai kedai aa duniya."ajiye cup din hannunta tayi sannan tace."rufaman asiri, badai komai ba, Yaya Fadil duk santin ne kenan."dariya yayi yana ajiye nashi shima dan ya gama sha, yace."ai dole nayi santi, kedai komai naki daban yake Ruma, kin iya komai da komai."murmushi kawai tayi bace komai ba sannan ta cigaba da bashi labarin.
"Yauwa yaya Fadil, bayan ciwon khamis yayi tsanani, tunda baya zama sai dai kwanciya, nan fa aka fara kai shi asibiti GENARAL HOSPITAL, munyi kamar zuwa biyu su kayi discarded din mu zuwa AMINU KANO TEACHING HOSPITAL."
"Haka muka koma Aminu kano, aka bamu gado, amman shi gadon sai an bada kudin har dubu hamsin, sannan za'a bamu gadon da Khamis zai kwanta a asibiti."
"Ba inda Baba bai je ba, amman bai samu kudin ba, sai dai Mama ta sai da wani dan marakin sa din ta wanda ta gada wajen Babanta, aka biya kudin gado....

*karku manta ina kan bakana yawan comment yawan typing ❣️, much love uh all my fans*


*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now