33&34

265 27 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
  _Jameelah jameey_

*Yar'mutan Kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

            

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page_33&34

"Haka aka bamu gado,  nan aka fara yi ma khamis wankin kai, saboda sunce ruwa ne a cikin kanshi sosai."
"Sai da mu kayi kwana hudu a Aminu kano, a na yi ma khamis aikin kai, sai kawai watarana a kace mana mu bada DUBU DARI DA HAMSIM, za'ayi ma khamis aiki."
"Ba yanda ba'a yi ba su rage kudin aikin, amman suka ce haka zasu yi shi, shiyasa muka hado kayan mu muka dawo gida...
"Baba ya cigaba da neman kudi, ita kuma Mama ta fara aikatau  gidan Alhaji Sanusi."
"A na haka Allah yayi ma Ba'ba Rumaisa rasuwa, Baba yayi kuka kamar ba gobe, ga jikin khamis da sai gaba yake ba sauki sai wurin Allah."
"Watarana muna gidan Alhaji Sanusi, muka ji ana ihu cikin unguwa, muna leƙawa, muka ga wuta ta tashi gidan da muke haya."
"Allah yaso ba kowa a gidan, sanadin wutar nepa wutar ta tashi a gidanmu, munyi kuka sosai,dan ko komai namu sai da ya ƙone, haka muka barma Allah, lamarinshi muka anshi kaddaramu hannu biyu."
"Alhaji Sanusi ya bamu wani shago a kofar gidan shi yace ya bamu sati biyu mu zauna kafin mu samu wani gidan haya, saboda bai dace ba a ce muna kwana  a shago ba."
"A hankali muka samu wani sabon GIDAN HAYA, a cikin Kurna amman bayan airpot, haka muka had a kaya muka koma."
"Kullun nida Mama sai munzo aiki tunda uwar safiya a kasa da kafafunmu, dan ni makaranta nike wuce wa dan yanzun na kai jss2 a Secondary school."
"Haka muke ta rayuwarmu, Baba yana neman kudin aikin da za'a yi ma Khamis."
"Ciwon Khamis ya tashi abun ba kyaun gani, dole ta sa muka koma Aminu Kano, Likitoci sun ce aiki za'a yi mashi, kuma ba'ason aikin ya wuce yau zuwa gobe."
"Mun dun aikin ya wuce ranar sai dai Muyi hakuri da shi, nan hankalin kowa ya tashi, Baba ya je ya kwaso kudin da ya tara harda wanda ita ma Mama ta samu ta tara."
"Baba ya kwaso kudin baki daya, da aka lissafa duka kudin dubu saba'in ne, ba inda Baba bai shiga ba neman bashi amman bai samu ba,  haka ya hakura ya dawo asibitin...
"Ya gaya ma Mama baisamo ciko ba, nan Mama ta kwashe duk kayan dakinta ta sayar da su dubu  talatin, da aka hada kudi suka cike dubu dari."
"Saura dubu hamsin, muke nema cikon kudin aiki, ga khamis nan muna gani kwance babu kudin aiki, sai Alhaji Sanusi ya ba Baba kyautar dubu hamsin, nan aka hada aka bada sannann aka shiga da shi aiki...
"Bayan angama aiki lafiya, roba ce aka samai daga cikin kai zuwa wajen fitsarin shi, sun ce zai ringa fito ruwan da kai cikin kan shi a hankali har kan ya koma kamar na kowa."
"Bayan anyi aiki da shekara ukku, dan ba inda Khamis baya zuwa har magana duk nayi, watarana muka waye gari Khamis ya ce ga garinku, Allah yayi ma Khamis rasuwa😭😭."
"Munyi kuka, domin maganar gaskiya mutuwar khamis munji ta sosai, dan yana saurin shiga cikin zuciya, gashi nayi bala'in saba wa da shi , lokacin ina SS1 a secondary school."
"Bayan na gama secondary school ina da 18yrs, lokacin nayi saukar gur'ani mai girma, bayan nayi candy mai gidan da muke zaune na Kurna yazo shima ya ta damu."
"Yace mu barma shi gida, zai gyra shi, zai sa amaryarsa a cikin gidan, dan haka ya bamu sati biyu, cikin sati biyu Allah yasa muka samu gida a nan cikin unguwarku."
"Nasarawa, mun samu GIDAN HAYA MAI SUNAN DAKI GOMA, nan muka yi sallama da abokan Arziki, kafin mu tafi Alhaji Sanusi ya siya ma Baba KEKA NAPE, ace ya ringa kawo mashi  balance har ta zama tashi."
"Haka ko a kayi yanzun nape ta zama ta Baba, tunda muka dawo zaman gidan su Halimai bai da dadi, dan bamu san maiyasa su Halimai suka tsani rayuwarmu ba, dan duk zaman mu a GIDAN HAYA bamu zama da mutane sai wannan."
"Maman A'i ita tayi man hanyar aiki gidan ku."



"Kaji labarin RUMAISA FADIL MUHAMMAD."

my dear's Fan's dan Allah kuyi hakuri da wannan ina busy ne wlh.

*Yar'mutan Kankia ce❣*




Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now