49&50

293 21 2
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      

            

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_49&50

Washe gari tun da safe, Rumaisa ta tashi, ta shirya sannan ta wuce gidan aiki..
Bayan taje, ta gama yin komai part din Umma suka shiga kitchen suka yi white rice with kayan lambu...

'''shinkafa,  carrot,green beans (pies''' )

_Yanda ake hadawa__

'''Da farko zaki samu tukunyarki mai tsata, ki daura a saman gas, sai kisa ruwanka wada tace, indan ya tafasa sai ki wanke shinkafarki sosai ta wanku, ki zuba a cikin takuya, kafin ta dahu ki samu carrot dinki ki yanka shi kanana sai ki wanke shi sosai, ana sauran bai fi 30min ki sauke shinkafar ba, sai ki zuba carrot din da green beans dinki, sai ki juya su yanda zasu hade da junansu sosai, in sun yi kamar 20min sai ki yi per boiling din shinkafan,  Kinyi per boiling water din da kamar 5min sai sauke ki sa a cikin cooler...
'''
Sai tayi miya....


'''tittasai (pepper),tarigu,albasa,curry,thyme,seasoning,kayan dan'dano
Mai,  jan Nama,  garlic (tafarnuwa)'''

'''Da farko dai uwar gida zaki wanke namanki ki sa  a tukunyarki, sai ki daura tukunyar a kan gas, ki dan sa kayan dan dano kadan da albasa da garlic da yar citta kadan(kun san dai citta tana fidda karnin nama), sai kisa dan ki shirinki shima kadan....'''

'''uwargida, zaki samu pepper dinki ki gyara shi sosai,  shima tarigun ki gyara shi sosai, albasa ma ki gyara ta, ki hadasu ki wanke su sosai, sai ki yanka su kananu ki zuba a cikin blender dinki ki blending su sosai, ki samu container din ki ki zuba shi markaden kayan miyar..
'''
'''Sai ki dauko tukunyarki ki daura a gas dinki, ki sa mai dinki ya dan soyu kisa yar albasa kadan gun soya man, sannan kin dauko kayan miyar da kika blending ki sa a cikin tukunyar,  in kayan miyar sun fara soyuwa, sai ki dauko dan'danonki ki zuba, ki gyara garlic din ki kasa a ciki, sannan ki yanka albasarki itama ki zuba, ki dauko tafashen namanki shima ki zuba, da roman tafashen da ki ida miyarki, inta dahu sai a sauke..

'''

Bayan ta gama yin shinkafa sai tayi lemun cucumber da danyar citta

_Abubuwan hadawa_

'''Kukumba (3) Citta (4), Suga,Lemun tsami (5),

Yanda ake hadawa'''

'''Da farko zaki sami kukumbarki ki wanke ki yanka kisa a blender.
Sai ki wanke cittarki ki goga da abin goga kubewa ko ki yanka kisa a blender ki hada da kukumba ki markada.
Sannan sai ki tace ki sa suga da lemun tsami.
Daga karshe, sai ki sa a firinji ko kisa kankara'''
Bayan ta gama hada komai ta kanshi a dining lokacin 1:00pm tayi, sallah taje dakin Fadila tayi, sannan suka fito, suka zauna aka kira Fadil yazo suka yi lunch  din...
Bayan sun gama yin lunch , Umma ta tashi tace ita ta tafi gidan su Rumaisa zasu yi magana da Mama, bayan tafiyar Umma, Fadil ya kalli Rumaisa sannan yace."Princess." Kallonshi tayi sannan tace."Naam prince." Dafe zuciyarshi yayi, dan sosai maganarta ta soki kagon zuciyarshi, murmushi yayi sanann yace."tashi ki shiga room din Fadila ki shirya kaya nan can na bata tun da safe, zamu tafi shan ice cream." Cikin salo mai tafiya da imani tayi magana,tace."to shikenan prince bari naje na shiyar tom." Kallonta yayi sannan yace."Princess kinsan me."!? Girgiza kai tayi sannan tace."Aa princes sai ka fadi." Matsowa yayi kusa da ita sannan yace."muryarki tana da dadin saurare, yanda kikasan ana busa sarewa dan dadi, ilove you Princess." Cikin dadi tace." Hakima samun masoyin gaskiya yana da wahalar gaske, ni kuma Rumaisa ba tare da nasha wuya ba Allah ya bani, Prince ina sonka nima kuma ina kaunarka." Tashi Fadil yayi yana hura mata iskan kiss, dafe kirji Rumaisa tayi alamun sakon kiss din Fadil ya iso gareta, itama maida mashi tayi da zanan heart bisa iska, rufe idanu Fadil yayi shima sakon ya iso, sannan yace."iluv uh will all my heart." Wucewa suka yi dan su shirya, Rumaisa shiga room din Fadila tayi tana cewa."Fadila, muga kayan da princes ya baki,ki bani."cire wayar kunnanta Fadila tayi sannan tace."ok ga sucen, red laces ne, shiga kiyi wankan ki fito na ta ya ki shirya wa."

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now