29&30

295 26 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

       _STORY AND WRITING_ _BY_
   _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_29&30

Numfasawa Rumaisa tayi sannan ta cigabaa da cewa."Mahaifina, ya fara kama GIDAN HAYA, a nann rijiyar lemu, nan ne farkon fara zamanshi a gidan haya."
"Iyayena suna zaune cike da soyayyar juna, duk da Babana  ba wani mai hali bane, amman bai ta barin Mamana tayi kukan takauci ba, dan gidanshi ba'a kwana da yunwa, sannan duk satin duniya sai sunci NAMA ko KIFI, dan Babana mutun ne mai neman na kanshi bai dogara da wani ba, yasan dai Allah yana tare dashi."
"Haka suka zauna cikin Soyayya, Babana bai yarda wani abu ya samu Mamana ba, in ko tana bukatar wani abu sai inda karfin shi ya kare dan sai ya samarma ta, duk da na wata sana'a yake mai karfi ba, sana'ar ga ruwa yake a cikin garin Kano, amman bai yarda wani abu ya samu Mamana ba."
"A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah, Allah yaba Mamana ciki, sunyi murna sosai, haka suka reni cikin, cikin kauna da jindadi."
"Ranar Lahadi 8/8/1999, Mamana ta haifeni, iyayena sunyi murna da samuna, sunyi ma Allah godiya da ya azarta su da samun ƙa ruwa, dan ko Babana har kuka sai da yayi dan murna."
"Ranar sunan naci sunan kanwar kakana RUMAISA, saboda itace ta rike Babana tun yana dan shekara goma a duniya, bai da kowa sai ita,shiyasa ana haihuwata ta mani sunanta wato Rumaisa."
"Babana tun yana dan shekara goma a duniya, ya rasa mahaifanshi kuma ba mutuwa su kayi ba ya wayi gari ya tashi babu su babu dalilin su, suda Yayan shi, suka barshi shi daya shine Ba'ba Rumaisa ta rike shi har tayi mashi aure."
"Na taso cikin gata da kaunar iyaye, ban san  wani abu ba wai shi talauci, duk da ba wani bane Babana, amman duk abunda ake sawo ma Yaro yayi wasa nima Babana ya siya man, har ma da wanda ban sani ba, duk yana saya man."
"Watarana  mai gidan da muke haya yazo shida wasu matasa majiya karfi, suka kama fiddo mana da kayan tsakar unguwa suna watsi dasu a kan santa."
"Mamana, tana kuka tana tambayar Alhaji Mala tace."lafiya Alhaji kuke zubda mana kaya cikin unguwa ko kudin kune bai biya ku ba."? Wani matsiyacin kallo yayi ma Mamana sannan yace."Lafiya lau, jiya ya kawo mani kudin ma, ga kudin nan in ya dawo ki bashi kice ni Alhaji Mala nace, na gaji da zaman ku cikin gidana, dan haka bani makullin gida."
"Kuka Mama ta fashe dashi tana neman alfarma wajen Alhaji Mala, amman yayi uwar shigu da ita, haka Mamana ta bashi makuli tana kuka, nan Alhaji Mala, ya tafi ya barmu a kofar gida munata kuka nida Mama."
"Sai dare Baba ya dawo ya tadda mu cikin wannan bakin hali, haka ya kwashemu ya kaimu gidan Ba'ba Rumaisa muka kwana."
"Itama gidan haya ne, dan haka mu ukku muka kwanan cikin dakin ta nida Mama da ita Ba'ba  Rumaisa, shi kuma Baba ya kwana a soron gida."
"Washe gari Baba ya fita neman GIDAN HAYA a cikin garin Kano, amman ba inda bai je ba bai samu gida ba, haka ya dawo jiki duk a sanyaya, sai da Ba'ba Rumaisa tayi mai fada sannan ya saki jikinshi."
"Haka ma washe gari, ya sake fita neman GIDAN HAYA, amman bai samu ba, sai washe gari Allah yasa aka dace da wani gida a Kurna."
"Nan muka hada kaya muka koma Kurna da zama, mun tashi daga rijiyar lemu, mun koma Kurna."
"Mun cigaba da rayuwarmu a Kurna hankalin mu kwance, sai dai mu Kaima Ba'ba Rumaisa ziyara duk randa babu Isilamiya don na shiga Isilamiya a nan Kurna."
"Na shiga primary school,Lokacin Babana ya bar sana'ar Ruwa, ya koma hayar machine, wani Alhaji  sanusi ya siya mashi, yana bashi balance, tun rana...








*yawan comment yawan typing, dan gsky ba zan dunga yi maku typing mai tsawo ba, ku bakuyin comment dan haka ga wannan*



*Yar'mutan Kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now