27&28

322 27 2
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

       _STORY AND WRITING_ _BY_
  _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
            

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*wallahi rashin bani ruwan comments sosai, zai sa na maida A GIDAN HAYA na kudi, dan haka sai ku gyra naga ruwan comment har yana jiƙani🥺*

Page_27&28

Ko kallon inda su Lami suke Rumaisa batayi ba, sai ma wucewarta da tayi gidan aikinta, dan tayi ma kanta alkwarin ba zata sake biyema su Lami ba, suje ma suji da matsalar da tayi masu yawa, sannan su sama wasu ido, aikin banza kawai.
Haka Rumaisa ta isa inda zata sallama tayi ta zauna ta fara gaida Umma."Umma ina kwana."?..."Lafiya lau Rumaisa, ya mamanki."?cewa tayi. "Lafiya lau, tana gaisheki.""ina ansawa."Hajiya Maryam tace tana gyara kunba, tashi Rumaisa tayi sanann tace."Umma na wuce na fara aiki."kallonta Hajiya Maryam tayi tana murmushi sannnan tace."to Rumaisa."nan Rumaisa ta fara aiki bayan ta gama, ta tambayi abunda zasu dafa, nan suka shiga kitchen ita da Fadila, suka dafa jallof din taliya, da taji naman cikin rago, da kuma mango juice, nan suka jera a dinning, suka kira Fadil, nan suka ci abincin, suna gama cin abincin Fadil ya kaisu salon, nan aka gyara masu kansu, suka taho gida, ita Fadila ta tsaya gun Abdullah, ita kuma Rumaisa tabi Fadil part din shi, suna cikin labari bacci ya kwashe Rumaisa...
nan fa Fadil ya rude saboda masifar kyaun da  tayi, baccin yayi mata kyau sosai,  bai san sanda ya fara daukar ta hoto ba kala-kala, sai da yayi mai isarsa sannan ya tsaya, sai a wannnan lokacin ya samun damar yi ma ta kallon kyau...
ita dai Rumaisa chocolate colour ce, tana da hancinta dai dashi, ga fararen idanunta manya-manya dasu lulu eyes, dan bakinta dai dai kiss dashi ga pink libs dinta sun kara ma fuskarta kyau, hips gareta da boobs sosai, ga bakin gashin ta har gadon baya, ita dai Rumaisa tana kama da ROSHINI ta KING OF HEART, sai dai ita roshini ta fi Rumaisa hasken fata, dan Rumaisa ba fara bace sosai. 
Sai da Fadil ya gama kare  ma Rumaisa kallon san ranshi sannan ya tashi ya shiga wanka, yana shiga wanka Rumaisa na tashi daga bacci tayi mamakin baccin ta data yi har haka, fitowarshi kenan yaga ta tashi, kallonta yayi yaga babu alamun da zai nuna tayi bacci, kuma bacci tayi sosai, ce mata yayi."Ruma har kin tashi."? Shagwaɓe fuska tayi sanann tace."Eh Yaya Fadil, gida zani,bansan sanda nayi bacci ba."murmushi yayi sannan yace."to ki bari na shirya sai na maidaki gida ko."? Kwantawa da tayi tana cewa."to shikenan yaya Fadil, ina jiranka fa."bai ce mata komai ba ya shiga ciki dan ya shirya, cikin bua shadda ya shirya sannan ya murza hula yar'maiduguri, yabi jikinshi da turare masu kamshi, sosai Fadil yayi kyau kamar ba shi ba, sai kace wani sabon ango haka ya fito sai aika mata da sakon ne yake kala kala, yana murmushi, kallonshi ta tsaya yi, dan yayi mata kyau sosai dan bata san ya iso wajen ta ba sai ji tayi yace."Madam tashi mu tafi to,ai ban dade ba ko."? Sunɓura dan karamin bakinta tayi, sannna tace."ni Yaya Fadil ka dade mana, wajen wata zaka shiyasa kayi kwaliya haka ko."? Kallonta  ya tsaya yi, yana mamakin yanda ta nuna kishinta a fili, sosai yaji dadin haka, dan hakan ya nuna Ruma ta fara sonshi kamar yanda shima yake dakon sonta, murmushi yayi sannan yace."Ruma ban isa naje wajen budurwa nace inasonta ba."? Sai da yayi mata wannan tambayar sanann taji kunya ta kamata, dan bata san sanda tace ma wajen wata zata ba, dabarbarcewa tayi, ta kasa magana, murmushi yayi yace."mu tafi, karkisa yau Auntynki ta kulle ma Yayanki kofa."kallonta yayi yaga reaction dinta, kuma ya gani, cewa tayi."yauwa yaya Fadil,mu tafi to."yanda yaga ta nuna bata damu ba, sai yaji ba dadi, kasa daurewa yayi har sai da yace mata."Ruma saurin mai kike yi har haka, kina murna zaki tafi gida ko? Baki jin ba dadi zaki tafi ki barni ni daya."? Kallon shi tayi, sannan tace a zuciyarta."kaji mutun, kaida kake ta rawar kafa zaka waje budurwa, dan ni nayi rawar kafa zani wajen Mama har na yi laifi, dan son zuciya."amman sai tace mai a fili."Ai yaya Fadil gobe zani dawo ko."murmushi yayi, dan yaji abunda tace, amman tasa baiji ba? Ce mata yayi."eh nasan ai gobe zaki dawo."daga nan ba wanda ya sake magana har suka isa gaban mota sannan yace."shiga mu tati kar Umma ta ganki tayi fada, tace har yanzun baki tafi gida ba."shiga kawai tayi, shima ya shiga ya tada motar suka tafi, shiru motar tayi kowa da abunda yake tunani a zuciyarshi, har suka iso gida sannan yace."Ruma mun iso, ki gaida man da Mama anjima munyi waya."fitowa tayi tana cewa. "to yaya Fadil, sai da safe."..."Allah ya kaimu Ruma,yauwa Ruma gobe Insha Allah inason ki bani labarinki, amman yanda kika gani Ruma."shiru tayi na dan wani lokaci sannan tace."to shikenan yaya Fadil, Allah ya kaimu goben Allah.".. "Amin ya Allah Ruma."
Sannan ya juya hancin motarshi ya koma gida, itama tana komawa tayi sallah, taje tayi ma Maman A'i karin karatu, tana yin sallahr isha'i ta kwanta, amman sai da Fadil ya kirata sukayi waya.
Washe gari, bayan Rumaisa ta gama yin aikin Mama, sannnann ta shirya ta wuce gidan aiki, bayan ta gama yin aiki da komai da komai, sannan ta Wuce part din Fadil...
Ta fara yin aiki a part din Fadil, Fadil ya shigo ya yana cewa."yau ba rannar aiki ba bace Ruma sarkin aiki."cewa tayi."to yaya Fadil, Amman bari ko da tea ne na hada maka ko."?cewa yayi."Ohk ina jiranki."Fadil ji yayi shirun yayi yawa sannnan yace."Nace ba."daga ciki tace."naam Yaya."cewa yayi."ko nazo na taya ki ne."?cewa tayi."Aah na hutar da kai yaya yanzun zan fito."..."ok shikenan Ruma am waiting...
Nan dai Rumaisa ta gama hada masu tea sannan ta kawo masu suka sha suna dan labari, cewa yayi."Nifa Ruma na kosa ki fara bani labarin ki fa."cewa tayi.to yanzun kuwa, amman ai kaga lokacin sallah yayi, bari muyi sallah sannan mu zauna."cewa yayi."ok nima bari na wuce, nayi alwalla a can mosque din, ke ma ki tsaya nan kiyi harta sallahr pls Ruma."cewa tayo."to shikenan ka dawo lafiya..
Bayan ta gama sallah ta kunna kallo, arewa24 tana kallon DADIN KOWA, nan fa Fadil ya shigo shima ya zauna, cewa yayi."to Rumaisa ina saurarenki."sai ta dago ta kalleshi da taji ya anbaci full name dinta, taji sunan yayi mata dadi sosai."murmushi yayi sannan yace."Ruma ya da kallo kuma, kodai kodai."? Ya faɗa yana dage mata gira daya."murmushi tayi sannan tace."bakomai kawai hakanan nayi shiru ma."dariya yayi sannan yace."are you sure."?.. "Yes, to yaya Fadil yau zakaji asalina kasan  wacece RUMAISA FADIL MUHAMMAD."
Kallonta yayi sosai, yaji tace sunan Babanta Fadil, ta gane kallon da yake mata sai tace."Ni Sunana RUMAISA FADIL MUHAMMAD, mahaifina dan nan asalin garin Kano ne, mahaifiya ta kuma yar Jigawa ce wata rugar fulani da ke karamar hukumar ha deja.   
"Mahaifina ya auri Mama a shekarar 1996,sunyi auren soyayya, babana ba wani mai kudi bane, asali ma shi sana'ar GA RUWA yake yi nan cikin birnin Kano...



*zan sake maimata maku makaranta novel din a gidan haya, mudun baku yin Comments zan maida a gidan haya paid book, dan ko yanzun muka fara wasan, wasa farin girki kenan, idan kuna son ku gama karanta shi a free book, nagga ruwan comments dinku sosai sannan*

*yar'mutan kankia ce ❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAΌπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα