21&22

366 22 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
   _Jameelah jameey_

*yar'mutan kankia ce❣️*       

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar
da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wannnan page din naki ne Auntyna, Wato BINTA UMAR ABBALE, Allah yabar kaunar da zuminci, Allah ya kara nisan kwana Aunty Bintu🥰*


Page_21&22

Har yanzun jikin Rumaisa sai dai addu'a dan tana dan jin jiki ba laifi, kwance take sai ga Mama ta shigo tace."Tashi mu tafi Rumaisa, ayi maki wannan allura ko mun dawo."kallon Mama tayi sannan tace."Wayyo Mama wallahi ban son wannan allura nike ba, dan Allah kayi hakuri kice ma Baba anyi mani kawai kinga daman ai naji sauki sosai."wani kallon banza Mama tayi mata, tana mamakin yanda Rumaisa bata san allura da magani cewa Mama tay."To bada ni za'ayi wannan rashin hankalin ba, inke baki da hankali ni inada hankali, a haka zamu sama maki ido baki lafiya amman muki baki magani, ai duk da sauki na gun Allah, amman Allah yace in baku lafiya kunsha maganin."sannan cigaba da cewa mama tayi."Dan haka tashi mu tafi tun muna mu biyu, kafin raina ya baci, Allah sai na bata maki rai."cikin irin tausayin nan Rumaisa tayi duk dan Mama taji tausayinta tace."Yi hakuri Mama yanzun zan tashi mu tafi, amman nidai tsoro nike ji sosai, bani son  wannan allura ko kadan Allah."hijab dinta Mama ta dauka ta bata sannan itama tasa tata hijab tana cema Rumaisa." Kinji dashi yar'nema, ke dai Rumaisa mijinki zai sa fama, ace mutum bai shan kagani kuma bai son allura, sai dai kawai aka ce mashi sannu ya ansawa, to ni Hadiza ba haka nike ba, dan haka tashi maza mu tafi wallahi na kusa sa maki bulala Rumaisa."tashi Rumaisa tayi tana cewa."yi hakuri na tashi mu tafi Mama."nan suka fito a tsakar gida, nan Mama tace ma yan mutan gida."To  mutan gidan nan mun tafi chemist sai mun dawo, za'ayi ma Rumaisa allura bata jin dadin jikin ta."cewa Mama A'I tayi."Ayyya Rumaisa Allah ya baki lafiya."cewa Mama tayi tana murmusi."Amin ya Allah Maman A'I."cigaba da cewa Maman A'I tayi."To Maman Rumaisa, adawo lfy."cewa Mama tayi."Allah yasa Maman A'i, A'i abincin ake ci ba'a bani, mun wuce."
Shewa Halimai tayi tana dariya tace."Allah yasa dai ba abun kunya aka dauko mana a cikin gida ba."dariya Lami tayi sannan tace." Amin Halimai nima abunda nike  tunani kenan, dan jiya cikin kunnena naji tana amai da dare, Allah ya kara ma."Hindatu ta bushe da dariya sannan tace."sai ku gaya man, bari mu fara tara kudin raggon suna, da kayan mai jego."kallon su Maman A'I tayi tana mamakin mugun hali iri na su Halimai sannan tace masu."Yanzun ku wai maiyasa baku gyale Yaya Hadiza ita da Rumaisa su sha numfashi a gabanku?Ace mutun shi kullun ba alkwari a cikin zuciyarshi sai Shari, ku baku yi mata ya mai jiki ba, amman kun sama mata ido cikin gida, kuma baku hada komai dasu ba *GIDAN* *HAYA NE* ya hadu amman kuna kishi da baiwar Allah."wata rin ashar Halimai tayi sanna tace."Wai Maman A'i maiyasa kike shiga abunda bai shafeki ba."?Lami ce ta ansa maganar tana cewa."Ke dai kyaleta Halimai, abun nan yana bani haushi sosai, ke dai bamu Sanyo ki ba cikin hidamarmu ba,amman kin sama ido a gida, wallahi ki fita a harkarmu Maman A'i muna ganin girman ki."Hindatu tace."kin dai gaya nata Lami, na lura Maman A'i tana son shiga hancinmu da gudundune, dan haka kiyi harkarki muma muyi tamu cikin gidan tunda nagadai gida ba na mijin kowa bane a cikin mu, gida dai naga *GIDAN* *HAYA NE*."kallon su Maman A'i tayi, taga yanda duk suka tadda jijiyojin wuya cewa tayi."Allah ya baku hakuri, bansan zaiyi maku zafi har haka ba da bansa maku baki ba, amman insha Allah daga yau na daina, kuma Insha Allah watarana zaku daina."cewa Halimai tayi."Wannan kuma ke kika san shi, hakuri ba, baki san mu ba mu san wata kalma wai ita hakuri ba, yau muka fara jin ta kuma daga cikin bakin ki muka ji ta, mudai kawai zaman lafiya a gidan nan shine ki fita a idonmu mu kulle."tashi Maman A'i tayi bata ce masu komai ba ta wuce dakinta,suko Rumaisa tunda suka tafi take hawaye dan tana tsoran Allura sosai, koda akayi mata allurar kuka ta tashe dashi sosai Mama ce tace."Rauguwar banza, ke da kike mace, watarana haihuwa zaki yi fa Rumaisa, amman kike yi ma allura wannan ihun sai kace wanda aka cika ma wuka a wuya, Allah ya kiyaye dan wannan rauganci ba Kara in mamaki kika bani ba."cewa tayi tana goge hawaye."Allah Mama baki ji yanda nike ji ba, gashi allurar shegin zafi ne da ita, ni nasa ma na mutu."tsaki Mama tayi sannan tace."Eh kin mutu dawowa kika yi yar'nema, yanzun allurar ita ake cema wa kamar an mutu, duka minti nawa ne akeyi, Allah dai ya sawaka maki."cewa tayi." Amin Mama ni nama samu sauki, gobe zani koma bakin aiki  na, dan nagaji da kwanciya har jikinka yayi ciwo."kallon Mama tayi sannan tace."Allah ya kaimu lafiya, amman dan kar a kuma yi maki allura shiyasa zaki koma aiki." Cewa tayi."Amin Mama, kinsan nayi missing din Fadila sosai, itama tana can tana missing dinna."cewa Mama tayi."kudai keda Fadila Allah ne ya hada ku."murmushi Rumaisa tayi sannan tace."hakane ko Mama."haka suka kama labari har suka iso gida suka shige room din su.

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now