3&4 Ina gdy masoyana bni da bkin da zan mku gdy sai dai nce Allah ya bar kauna

746 68 4
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
           _Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce ❣️*

            

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar
da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA NAMTARY UMMYN ABBA ALLAH YA JiKANKI YASA MUTUWA TAZAMO HUTU A GAREKI, ALLAH YABA MIJINKI DA YARANKI DA DUK WANNI MAKUSANTANKI HAKURI DA JURINYAR RASHINKI😭🙏🏻'''


Page_3-4

"Rumaisa.".. "Naam Baba, ina kwana."?  "lafiya lau, kin tashi lafiya"? "Lafiya lau Baba, "yauwa da man magana nike so nayi dake, jiya Mamanki ta gaya man yanda ki kayi fada da mutanan gidan, to daga yau karki yarda na sake ji, Kuma ba tarbiyar da muka baki ba kenan, bani son naga karami Yana raina na gaba da shi kinji."?cewa tayi. "Eh Baba, naji." cewa yayi."To Allah yayi maki albarka." "Amin Baba."
"To Maman Rumaisa ni zan wuce neman kudi, da akwai abunda kuke bukata."?  Cewa tayi."Eh ba sauran magi ya kare yau."murmushi Baban Rumaisa yayi sannan yace."Shi Kadai ya kare babu komai."? Cewa itama tayi tana murmushi. "Eh Shi kadai ya kare gaskiya."cewa yayi."To ga wata Naira dari biyu nan kun sawo magin, ni na wuce sai na dawo."ansa tayi tana cewa. "To angode, adawo lfy."cikin jindadi yace."Allah yasa, Amin."
"Mama bari nasamu na dan kwanta kafin gari ya ida yin haske."cewa Mama tayi. "Aah tashi dai mutashi mu shiga wanka, kafin mutanan gidan su tashi bacci."cewa tayi. "To shikenan Mama, na tashi mu wuce ko."?.. "to daman Babanki ya jawo mana ruwan wankan har dafa mana Shi yayi mu tafi kar ma ya huce."
Rumaisa ta fara shiga wankan tana fitowa ta tsarema Mama itama ta shiga, suna fitowa suka yi wanke wankensu duk abunda suka san nasune sai da suka kaudashi, suka kai shi daki, suka kulle dakinsu suka yi kwanciyarsu suna basu tashi ba sai karfe 9 na safe, Rumaisa ta shirya ta tafi gidan aiki...
Sallama Alaikum, Aunty ina kwna? Kin gani yau Kuma sai yanzun."cewa Hajiya Maryam tayi."aiko dai yanzun Fadila ta gama tambayar ki, zaki raka ta wai kunshi, ta gaji da jiranki, sai Yayansu yayi dropping din ta ya wuce wajen aiki."cewa tayi."ayya banji dadi ba, ai da na raka ko mike kafafu nayi tunda yau babu Isilamiya yau, ai shiyasa ban zo da wuri ba."
"Nikom nace Rumaisa yaushe zan baki waka kiyi man awara, kinsan Fadil yana bala'in san awara, gashi yau na ida soya mashi ta cikin freeze, nasan gobe dan Ubanshi sai munyi fada da Shi in yaji babu awarar.".. Murmushi tayi sannan tace."Shi dai Yaya Fadil yana son awara naga Alama, bakomai Aunty bari na ida aiki yanzun naje nayi maki ita zuwa anjima nagama insha Allah."
"Bani takura maki ba dai ko Rumaisa."?...cewa tayi."haba Aunty wata kallar takura, ai kifi karfin komai a guna.".. "To nagode Rumaisa, bari na tashi ya dibo wankan kafin ki gama."cewa tayi."To Aunty a fito lafiya."..  "Allah yasa."
Bayan Rumaisa ta gama yin aikin gida, ta ansa waken ta wuce gida, tana mamakin yanda Fadil yake da halinshi, shide haka Allah yayo Shi cewa tayi."ni Rumaisa ai tunda nike ban taba ganin dariyarshi ba, gaskiya Fadila tana hakuri da Allah ya hada ta da Yaya mai halin Fadil ace mutum baya dariya kullum fuskar shi tamau sai kace an aiko mashi da sakon mutuwa."haka ta kama maganar ta cikin zuciya har ta isa gida, dan tayi alkwarin baza ta sake yi masu sallama ba, in ba dai su Maman A'i ta iske ba a tsakar gidan wannan zata yi mata sallama har ta gaidata domin Maman A'i mace mai hankali da wayau...
Dawowar Rumaisa gida kenan tace."Mama ga aiki awara nan zamu sake yi ma Aunty Maryam." murmushi Mama tayi tace."A'a to bari na fito daman zaman banza nike yi bani da abun yi."nan fa Mama ta fito cikin some minute suka tsinke wankan, nan Rumaisa tasa hijab takai markade, tana dawowa suka daura sanwar awararsu, suna fira da Maman A'i, nan Hindatu ta fito tana yi masu wannan kallo sanann tace."Allah ka rabamu da matatsiyar zuciya, in ba rashin zuciya ba, mutane sai dan banzar kwakwa, in ba kwakwa ba ace duk sanda za'ayi awara kuke yinta dan ku samu na dare."
Maman A'i tace."Ai Hindatu kasan ance *NEMAN NA KAI,*  *HALAK NE,* dan haka ba ruwanki da lamarinsu, ya ka mata ku chanza hali, haba Hindatu mutanan nan basu tsarema ku komai ba amman duk kunbi ku sa masu ido, Kuma ku ke da abun da ido."ɗaga ma Maman A'i hannu Hindatu tayi tana cewa."dakata malama, au ashe yar iya Andawo?  yanzun za'a fara yin shigar sugula, inba shigar sugula ba wa ya saki cikin wannan maganar yar'nema."? Cewa Maman A'i tayi."Ban sani ba sai naji bugu sannan."Maman Rumaisa ce ta fara ba Maman A'i hakuri dan taga ranta ya fara ɓaci yanzun zata biye masu suyi fada cewa tayi."Dan Allah Maman A'i kiyi hakuri, karda ki biye mata, duka duka maiye duniyar, da za'abiye Anita bata lokaci gurin fada, kinga ma awarar ta kusa yi muna gama soyawa sai mu shiga daki ba shikenan ba." cikin raina da jin zafi da hassada Hindatu tace."da ya fi maku ma kwakwata banza da ku."Maman A'i tace."ke dai kije ji da shi, mundai yi gaba sai dai a bimu da ido."
"Maman A'i dan Allah kibar biye masu, mutanan nan ba hankali ne dasu ba." Cewa Maman A'i tayi."wallahi Maman Rumaisa, indai su kayi bisa idona sai na yi magana, yo ina dalili mutane ba ku hada miji ba, amman sunbi sun sa maka ido suna kishi dakai, ai wannan kishi ne da hassada, haka zasu kare a wulakance, mu Kuma insha Allah yanzun muka fara yin gaba, dan munyi masu nisa fidtinkau, dan ba yabon kai ba baki daya gidan nan mazajenmu sunfi sauran nasu, ai Alhmdulh ko nan aka tsaya."cewa Maman Rumaisa tayi."Allah yasa dai mu dace, "Amin Maman Rumaisa...
Bayan sun gama yin awarar, Rumaisa taje ta kaima Hajiya Maryam, nan suka dan yi hira sannan tayi mata sallama ta dawo gida direct dakinsu ta wuce, daman tsakar gidan su Lami ya iske suna zaman banza, zaman gulma...
"Rumaisa har kin dawo? "Eh Mama wallahi yau duk na gaji sosai, "ai dole, tashi kici abinci ba sai kin tsaya jiran Babanki ba, "To Mama." bayan ta gama cin abinci ta samu ta kwanta cikin bacci taji ana fada da mijin Halimai da na Lami, suna ta fada sai kace yara kanana,  wai abunda ya hada su, shi mijin Lami yace ma mijin Halimai yayi ma Halimai tsakani da matarshi dan ya lura ita take koya ma Lami zaman gulma da kirbibi, shi kuma mijin Halimai yace suna koya ma juna dai, dan matarshi ba ma gulmaciya bace, da kyal da jibin koshi su Baban Rumaisa suka raba wanann bala'i...
"Na boni ni Rumaisa, wai har sai yaushe mutanan gidan zasuyi hankali."Rumaisa tace tana mamaki dan  tunda suka zaune a gidan nan bata taba ganin rana ta zo ta koma ba, ba'ayi fada a cikin gidan ba sai kace antara karnika a cikin gida, haba Allah ya sawaka ya yaye masu wannan masifar da ke damunsu....

*Tabbas naga ruwan comments dinku sosai, sai kash abunda baiyi man dadi ba😩, sansanin yar'mutan kankia, bakuyi comments ba, haka real jameey fans  one and two comments dinku yayi man kadan gsky😏, Mudun baku gyara ba zan daina yi maku posting 🤷🏻‍♀️😂*

*Yar'mutan kankia ce❣️*





Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now