43&44

270 19 1
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan  kankia ce❣️*

            

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wannan page din naku ne A GIDAN HAYA FAN'S GROUP kuyi yanda kuke so dashi, dan comment dinku yana sani farinciki🥰❣️*

Page_43&44

Washe bayan Fadil ya tashi, shiryawa yayi ya wuce part din Umma, bayan sun gama breakfast ya kalli Umma sannan yace."Umma."kallonshi Hajiya Maryam tayi, dan ta lura akwai magana a bakin ɗa'n nata, maida hankalinta tayi wajen shi sannan tace."Naam Fadil,wani abu naga kamar ba lafiya."? Ɗukar da kanshi yayi kasa, sannan yace."da man ina son nayi maki wata magana ne."murmushi Umma, dan tasan maganar da Fadil zaiyi mata, cewa tayi."wace magana ce haka Fadil? Ina sauraranka." ɗago kanshi yayi yana kallonta sannan yace."Da man, da man."tararshi Umma tayi sannan tace."da man mai Fadil."!? Dakewa yayi sannan yace."Eh Umma, da man nace wai maiyasa Rumaisa yau bata zo aiki ba."?

Shiru Umma tayi tana kallon  Fadil, dan tana mamakin yanda Fadil yake da zurfin ciki har haka, yana cikin damuwa amman zurfin ciki ya hanashi ya gaya mata, ce mashi tayi."Eh ta tambaye ni zata yi hutu ga wannan weekend."saurin ɗago kanshi yayi yana kallon Umma sannnan yace."week end kuma Umma."? Cewa tayi."Eh haka nace,wai lafiyarka, ka sani gaba kana yi man tambaya akan rashin zuwan Rumaisa."? Hawaye da suka zubo mashi yayi sauri ya goge dan karda Umma ta gani, sannan yace."Umma akwai matsala gaskiya."dafe kirji Umma tayi sannan tace."Subuhanalillah, matsala fa kace Fadil."!? Ƙara matsowa yayi kusa da ita, yana daura kanshi bisa cinyar Umma yana cewa."Eh Umma matsala ma babba, wanda take barazanar na rasa rayuwata."shafa kanshi Umma tayi alamun lailashi sannan tace."Ikon Allah, gaya man wannnan matsalar Fadil, Allah yasa bata fi karfin mu ba."juyowa yayi da kanshi daga bisa cinyar Umma, yana cewa."Umma bama tafi karfinki ba, insha Allah."shiru yayi na wani lokaci sannan yace."Umma, Rumaisa ce matsalar."murmushi Umma tayi sannan tace."Rumaisa kuma, ko wani abu tayi maka, da man naga satin nan bata zuwa aiki kan lokaci, kuma da wuri take tafiya gida."? girgiza kai yayi, sannna ya sauke kanshi da kan ciyar Umma, yana gyara zamanshi sosai, kallonta yayi sanan yace."Aah, ba abunda tayi man, sai dai na gaya mata inasonta yau kwana 8 kenan, tunda ga ranar ban sake ganinta,  kuma Umma wayarta kullun switch off."
Harararshi Umma tayi sannan tace."To ba sai kaje gidan su ba."? Kuka ya fara yi mata yana cewa."Umma naje gidan su har sau nawa, ko naje bata fitowa ansa daya ce bata nan, ina take zuwa Umma? Nidai na san bata zuwa ko ina daga nan gidan sai Isilamiya."share mashi hawayenshi Umma ta fara yi tana cewa."daina kuka Fadil musan mafita."girgiza kai kawai yayi sannan yace."to Umma nayi."sake cewa Umma tayi."to yanzun ya za'a yi Fadil."?da sauri ya dago kanshi sannan yace."Ai shiyasa na gaya maki dan ki sa ma man mafita, dan wallahi ji nike na kusa mutuwa." ya fadi ya kuka bisa cinyar Umma, dan komawa yayi ya kwanta, ji yayi zaman baya daukarshi, dan kuka yake sosai kamar ƙaramin yaro. Cewa Umma tayi."Subuhanalillah, Fadil kuka fa kake, saboda mace."?kallon Umma yayi sannan yace."Umma ina iya yin komai saboda Rumaisa, Umma ban san wani kallar so nike ma Rumaisa ba, Allah ya jarabeni da masifar sonta, Umma dan Allah ki taimaki rayuwa pls Umma na." cewa Umma tayi."To shikenan, tashi muyi magana."tashi yayi yana cewa."to ina jinki Umma."kallonshi tayi tta fidda wasa a fuskarta sannan tace."ka tabbata ka son Rumaisa da gaske? Dan na san ka kai wani kallar mutun ne, ba'a gane gabanka balle kanka."cewa yayi." Eh Umma ina son Rumaisa sosai, ki yarda dani Umma."numfasawa Umma tayi, sannan tace."to na san gobe zata Isilamiya ka bita hanyar Isilamiyar sai ka samu ka tare ta kaji Fadil."murmushi yayi yana share hawaye yace."eh Umma zanyi haka Insha Allah."ce mashi Umma tayi."komai kuka yi da ita ka gaya man."cewa yayi."To shikenan Umma."cewa Umma tayi."yauwa tashi ka tafi kayi sallah lokacin sallah yayi."tashi yayi yana cewa."to ni daga masallaci zan wuce gidan su Abdullah.".."to Fadil."

Bayan Fadil ya dawo daga masallaci, yayi wanka ya shirya, ya wuce gidan su Abdullah, yana shiga ya wuce part din Addan su Abdullah, dukawa yayi ta fara gaidata."Adda, ina wuni."?cewa tayi."Lafiya lau Fadil, ya gida da Ummarka."?....."Lafiya lau, Adda, na samaiku lafiya."?.... "Lafiya lau." nan Fadil ya wuce part din Abdullah, yana shiga Abdullah yace." Mr's Rumaisa, har ka iso kenan."? Zama yayi yana cewa."Ba dole ba Abdullah, tunda ina neman mafita ba."dariya Abdullah yayi sannan yace."to yanzun ya kuka yi da Umma."? Cewa Fadil yayi sannan yace."Hmmm, Umma tace man, gobe naje Isilamiyarsu na tarai ta a hanya."harararshi Abdullah yayi sannan yace."wai da kasan tana zuwa Isilamiya ka tsaya ba kanka wahala."?murmushi Fadil yayi sannan yace. "Hmmm ni na manta Ruma tana zuwa Isilamiya wallahi, sai da Umma ta fadi sannan."
Nan dai suka shirya yanda zai yi shine bai bar gidan su Abdullah ba sai bayan isha'i, bayan sunyi sallah ya hau motarshi ya wuce gida, yana shiga yayi ma su Umma sai da safe ya wuce part din shi....
Washe gari tunda safe Fadil ya tashi ya shirya yayi duk abunda yake, yaje ya gaida Umma ko breakfast bai tsaya yayi ba,  dan  ji yake kamar yayi fiffike ya ganshi gun Isilamiyar.

Tun karfe 11am yake zaune bakin Isilamiya, da yake ba da motarshi yaje ba, da motar Abdullah ya je gun, kan idonshi yaga Rumaisa ta wuce da nikaq a fuskarta, sai kash🤦‍♀️Rumaisa bata son tsiyuwarta kawai Fadil yana gane wa balle ta fiya ma😁...
Yayi dariya sosai, wai shi Ruma tasa ma nikaq dan kawai kar ya ganta, haka Fadil yai ta zama har aka  taso su Rumaisa daga Isilamiya, tana cikin tafiya taje ance mata...
"Hello pretty kin gama boye fuskar ko."?
Wai gowar da Rumaisa zata yi suka yi ido da ido da Fadil,wani wawan Kallo tayi mashi sannan tace. "lafiya malan? Zaka wani tsada mutun kan hanya."murmushi yayi sannan yace."Ruma ni ne fa, kike yi ma haka."numfasawa yayi na wani dan lokaci yanajin yanda kirjinshi yake mashi zafi akan abunda Ruma take mashi, cewa yayi."Ruma gaya man laifin da nayi maki kike yin man kalar wannan hukuncin."? Tsaki tayi marar sauti, sannan tace."Ni ba laifin da kayi man."matsowa yayi kusa da Ita sannan yace."Kuma shine kike yi man haka."?  matsawa tayi, tana kallon shi sannan tace."Eh Fadil nayi maka haka, to tsaya kaji, daga yau bani bakai."da sauri ya kamo hannunta yana cewa."Ruma amma.."dakata malan, karka sake kasake zo mana gida, nima zan bar zuwa gidan ku, dan haka bani *SONKA* , kaje ka samu dai dai dakai badai ni ba."Rumaisa tace haka tana fisge hannunta daga rikon da yayi mata, tana mashi kallon baka isa ba, hawaye yake yana cewa."Ruuuuuuma, plssssssss, karkiyi man haka, karkice baki sona plssssss,kiyi man ko wani hukunci amman karki ce baki sona,wallahi inasonki sosai ki daure ki anshi soyayya ta."cikin fushi Rumaisa tace."haba wai kai wani kallar mutun ne nace maka *BANI SONKA, BANI* *SONKA* , haba *ANA SO* *DOLE NE...*"?
Nan take Fadil ya fadi kasa yana kiran sunan Ruma yana cewa. dan Allah ki taimaka man.. Bai ida maganar ba  sai kuma ya fara aman jini yana kiran Rumaisa dan Allah ki tausaya man ki soni.
Rumaisa ta kama ihu tana neman agajin mutane wani Malamin su ta gane ta fara cewa."Malan dan Allah ka taimaka man.'Cewa yayi."yi shiru baiwar Allah yanzun zamu kai shi asibiti kinji."nan suka taimaka aka sa shi a mota, Rumaisa ta shiga tana kuka, tana cewa..
"Fadil dan Allah karka mutu kabarni, ka tausaya ma zuciya ta Fadil, ban shirya rasaka ba dan yanzun,na boni ni Rumaisa, yanzun banda sauran wani masoyi na gaskiya, ya zan ce ma Umma, wayyo Allah."
Nan suka iso asibiti, aka anshe shi emergency, nan likitoci suka runkuɓa a kanshi dan su ceto rayuwarshi."cikin wanda suka kawo Fadil asibiti yace ma Rumaisa."Baiwar Allah ba kuka zaki yi ba, addu'a zaki yi mashi, yanzun bani wayarshi a kira Mamanshi ko."? Miƙa mashi kawai tayi bayan ta fidda password.

Haka aka Kira Umma aka gaya mata halin da Fadil yake cike yanzun haka yana asibiti, aman jini yay, cewa Umma tayi cikin tashin hankali."Dan Allah kuna wani asibitin."?cewa yayi. "Muna DOCTOR MARYAM PRIVATE HOSPITAL....
Cikin tashin hankali Umma ta dauki hanyar hospital dinta, tana salati tana addu'a tana cewa Allah ya kare mata Fadil dinta.. 
Tana zuwa ta tadda Rumaisa zaune tana kuka,kallon Rumaisa tayi sannan tace."Rumaisa mai ya samu Fadil? Ki gaya man mai yasa mu Yayanku."?
Da gudu ta rumgume Umma cikin Kuka take cewa."Umma dan nace ya kyaleni bani son shi shine kawai ya fadi yana aman jini."shafa bayanta Umma tayi sannan tace."To yi shiru kinji Rumaisa, bari na shiga naga ya ake cikin yanzun."Girgiza kai Rumaisa tayi sannan tace."Umma dan Allah  karda ya mutu, wallahi ina son shi, ki taimake ni dan girman Allah Umma."fahimtar da Umma tayi Rumaisa bata cikin haiyacinta, cema Fadila tayi."
Fadila zauna da ita bata cikin hankalinta yanzun."cewa tayi."To shikenan Umma, kawata  dan Allah kiyi shiru,insah Allah ba abunda zai samu yaya Fadil, kiyi shiru pls....



*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now