7&8

507 35 2
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
   _Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce ❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

            
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Wannan page din naku ne Sansanin yar'mutan kankia fan's group da Real Jameey Fan's one and two kuyi yanda kuke so dashi, dan naji dadin comments dinku sosai, much love💔❣️💃🏼*

Page _7-8

"Mama sannu da hutawa."..."yauwa Rumaisa sannu Andawo lfy."? Sai da ta zauna sannan tace."Lafiya lau, Mama , gaskiya Mama na fara gajiya da abunda su Halimai ke yi man a gidan, yanzun fa daga shigowa ta wai nayi mata kallon banza."ji tayi Babanta yace."Rumaisa."waigowa tayi dan bata lura da Baban mata ba tace."Naam Baba"cikin fushi da bacin rai yace."daga yanzun duk wanda ya sake yi maki a cikin gidan nan bance ki raga mashi ba, ko wanene ni na baki dama."cewa Mama tayi."haba Babanta, ai bai ka mata kace mata haka ba, hakuri zamu cigaba yi mana."wani irin kallo Baban Rumaisa yayi ma Mama sannna yace."wani hakuri? na lura mutanan gidan nan basu san hakuri ba, ko daya dan haka duk wanda yayi maki ki rama ni na saki, tashi kije kici abincin ki kwanta bacci kinji yar albarka."cewa Rumaisa tayi."To Baba." bayan ta gama cin wata shinkaface yau Mama ta dafa masu, jollof din shinkafa da wake tayi masu, tana gama ci ta tashi tayi sallah sannan tayi karatu ta kwanta bacci, itace bata tashi ba sai 3:00am, tayi sallah,  asuba nayi tashi tayi asuba, sannan ta cigaba da yin azakar, tana gama azakar ta tashi ta shiga wanka, bayan ta fito wanka suka yi breakfast, kosai ne da koko, tana gama yin breakfast ta tafi gidan aiki.
"Aunty ina kwana."..  "Lafia  lau,ya gajiyar jiya da kuma."? Murmushi tayi sannan tace."Aa Aunty ai ba wani aiki bane mai wahala ba, Fadila fa."Hajiya Maryama tana jindadin zama da Rumaisa dan tarbiyar Rumaisa tayi mata cewa tayi. "tana dakinta tana baccin da ta saba."tashi Rumaisa tayi sannnan tace."to shikenan bari na fara aikin kafin ta tashi nagama, dan yau tace zanyi mata karin quri'an."cewa Umma tayi"To Rumaisa a gama lafiya."
Bayan Rumaisa ta gama yin aiki, tayi komai harta mopping duk tayi ta gama, nan ta shiga kitchen ta taya Hajiya Maryam aikin abinci, coconut rice su kayi da miyar kwai, bayan sun gama yin abinci ta wanke duk abunda suka bata, sannan tayi mopping din kitchen din again sannnan taje room din Fadila, dan zata yi mata karin karatun alqurani mai girma.
"Kawata, ai nasa har yanzun baki tashi bacci ba."? Cewa Fadila tayi."Rufaman asiri kawata, tun dazun na tashi, kawai na tsaya karatun wani novel mai suna *SANADIN LINK* , wanda *jameelah jameey* *Yar'mutan kankia* tayi shi, gaskiya *NOVEL* din akwai shi da Ilimantarwa, dan gaskiya naji tsoro, dan novel din ya Nishad'antar sosai, kuma ta farka da mata daga dogon baccin da suke yi especially mata masu bala'in bin *LINK* din tsiya."Numafasawa Rumaisa tayi sannna tace."Ohni kawata dama ace ina da waya da kin turoman wannan *NOVEL* na karanta, daman naji ana maganar *NOVEL* din *jameelah jameey* *yar'mutan kankia*, na karanta novel dinta daya, da wayar wata kawata a Isilamiya *NANA* *JAWAHEER* , shima yayi man dadi."Fadila tace."eh nima na karanta *NANA* *JAWAHEER* harda ma *GIMBIYA HAKIMA da IZZA KO MULKI* dan ko shi Izza ko Mulki na kudi ne tayi haka, dadin da yayi man nasa kudina na saya, ai ni gaskiya duk *NOVEL* din da *jameelah jameey* *Yar'mutan kankia* za tayi bani yarda ya wuce ni gaskiya, saboda duk novel dinta suna da ma'ana, yanzun in mun gama Karin karatun, zan baki ki karanta tunda ba wani yawa ne da shi ba *SHORT STORY* ne."cikin jindadi Rumaisa tace."to shikenan ngd."dan taji dadi sosai da Fadila zata bata ta karanta Sanadin link, dan taji ana labarinshi a isilamiyarsu.
Bayan sun gama yin karatun suka je yin lunch harda Rumaisa, domin Hajiya Maryam ta dauki Rumaisa kamar diyarta Fadila, sunyi lunch kowa ya kama gabansa, nan Rumaisa ta ansa wayar Fadila ta karanta *SANADIN LINK,* sannan ta ansa abinci ta wuce gida.
Tafiya Halimai take cikin sanɗa, samu tayi ta shiga kitchen ta bude tukunyar sauwar Lami ta fara ebar mata abinci, tana cikin haka sai ji tayi ana salati."Innalillahi, mai zan gani haka ni Hindatu? Yanzun Halimai daman ke keyi mana satar Abinci a gidan nan."cikin tsorata Halimai ta juyo, ji tayi hankalinta ya kwanta tunda Hindatu ta ganta ba Lami ba, cewa ta fara yi."To ni yanzun ya zanyi Hindatu, kinsan idan Lami ta gane na dibarmata abincin  sai ta gayama wannan jarabanban mijin nata, ya zo ya wulakantani, kuma ni idan ban dibarma yarana ba bansan ya zanyi ba.", kallonta Hindatu tayi sannan tace."to nima Halimai bansan ya zaki yi ba, nidai ba ruwana, duk abu na da wulakanci na a cikin gidan nan to walllahi  bani yarda da yin sata ba, saboda ita sata bakin fantine, kuma kina yin sana'ar wankin ki, mai zai ja maki sata?  nida nike yin kitso da kunshi banyi sata ba sai ke Halimai."?cewa Halimai tayi."Ai Hindatu, ba laifi na bane."cewa Hindatu tayi."laifin waye."?kallon Hindatu Halimai tayi sannan tace."Laifin Barau ne, kinga idan Barau ya kama hanya tun safe ya fita ya wonshi, bai dawowa sai in zai kwanta bacci, shi bai barmana komai ba muda yara wanda zamu sumu muci abinci  yace baya da kudi, to ya ake so nayi Hindatu? Kuma wankau yanzun ba kullum nike samu ba, bani samun kudi sosai ga yara sun damai ni da kukan yunwa, kinga ai dole na ringa dibarmaku abinci ina ba yarana."cewa Hindatu tayi."To kedai Halimai ki samu ki chanza hali dan Allah, dan sata ba hali bane mai kyau, kuma Tunda plate daya kika diba nasan Lami baza yi maki magana ba."
"Mama kina jin su Hindatu ko? "Eh ina jinsu Rumaisa, Allah ya ra bamu da buduwar zuciya."Rumaisa tace."Amin Mama, yanzun shi Barau a haka yake so Allah ya bude mashi, bayan ya tauye hakin iyalinshi."? Cikin jimami na rashin jindadi Mama tace. "Kin dai gani Rumaisa, ita kuma mata zuciya ta mutu da bakin ciki da hassada, shiya basu ganin cigaba, saboda mutun bashi yaba kanshi rufun asiri ba, Allah ya bashi,Allah dai ya sa su gane."itama cewa tayi. "Amin Mama, ni sai da safe.".. "Allah ya kaimu Lafiya.''
Kwantawa tayi, tana mamakin hali irin nasu Halimai, kuma ta wani wajen Halimai ta bata tausayi sosai, ba yanda za'ayi ace mijinta bai bata ko sisi, ga yara to taya zata cinyar dasu?  ai dole watarana tayi sata, dan Halimai sana'arta d'aya wato sana'ar Wanki, kuma ba kullun ake kawo mata wanki ba, ga Allah ya hada ta da dan iskan miji, wanda baisan darajar ta ba.
Ace mutum idan ya fita tun safe bai dawowa sai dare kuma bai bada kudin cefane, gaskiya Barau baida imani, ko daya, dan wannan  hali bana mutane masu imani bane.
Addu'ar  ta d'aya, Allah yasa gobe karda suyi fada da Lami, dan Lami watarana ba mutunci bane da ita, duk da tafi Halimai kyaun hali, komai take Halimai ke zugata.

*Ga fa dama ta samu masoyana ina masu bukatar karanta Izzah ko mulki complete, to nisa ta zo kusa dan yar'mutan kankia ta gama izza ko mulki idan kina bukata, maza gwarzayo kiyi ma wannan numbers din magana 08160508316 ko 07034464517, sister karki sake abarki a baya fa😁*

***************************

'''Niko nace Allah ya rabamu da miji mai hali irin na Barau, idan kuma Allah ya baki, tom Allah ya shirya maki shi, ya maidoshi hanya madaidaiciya, dan ko ana fuskantar wannan Marsalar, kaga mutun ya fita ya bar matarshi da yaranshi bai barmasu ko gishiri ba, kuma bai dawowa sai dare😏, idan kace ya bada kudi ko gari a saya sai yace babu🙄, idan ta matsa da tambaya sai yace bari yaje ya saida shekaransa ya sawo gari ☹️, babu ma magana maidadi da zata sa matar ta danji sanyi😬, watan watarana ke uwa kina ji kina gani kike barin dan'ki yana bara gidan mutane 🤦‍♀️, ko kuma ya zama dan aikin unguwa dan kawai ya samo maku abunda zaku ci😭, a haka kai kuma uba kake so Allah ya bude maka hanyar samu kana tauyema Iyalanka hakinsu😡, wannan dai hali ni yar'mutan kankia nayi tir da shi wallahi🤨, Allah ya mudace dai🙏🏻'''






*Yar'mutan kankia ce ❣️*

Share
Comments
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin