51&52

259 22 2
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING BY_
        
_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      

*BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wannan page din nakane Yayana Muhammad Kareem kayi yanda kake so dashi, kaba wanda kake so ka hana wanda kake so Yayana na kaina🤗*

Page_51&52

Bayan Rumaisa ta tashi tayi duk abunda zatayi ma Mama sannan ta wuce gidan aiki, bayan ta gama aiki sukayi girki ita da Fadila sannan ta wuce part din Fadil, sallama tayi ta shiga zaune ta iskeshi yana danna laptop, kallon shi tayi na wani lokaci tana murmushi dan ji take sonshi na kara fisgarta cewa tayi."Good morng Prince." dago kanshi yayi yana kallonta fuskarshi cike da annuri, dan baisan ta shigo ba, hankalinshi yana kan aikin da yake, cewa yayi."oyoyo Princess, sai yanzun kika shigo kiga masoyinki? Bayan tun tuni nike zuba ido naga shigowarki."
Ida karasowa tayi ta zauna tana kallonsh nuna tayi mashi da ido ma'ana kar ya damu yasan komai takeyi cikin ranta tana tunaninshi, murmushi yayi ya cigaba da aikinshi, itama gyara mashi ko ina tayi ta hado masu tea sannan ta zo ta zauna ta zuba mashi ta bashi tea din sannan ta kwashe laptop din ta kai daki ta dawo ta tana kallon shi sannan tace."Prince ina sauraren ka yau dai ka bani labarin waye Price." Murmushi yayi sannan yace."tom karkaɗe kunnanki yanzun zakiji ko waye Fadil."
Gyara zama tayi tana kallonshi  shima kallonta yayi sannan ya fara cewa."Ni suna na *FADIL* *KHAMIS MAI DAKO* , mahaifina haifafen dan jihar Kano ne, iyayenshi talkawane sosai, dan ba ko da yaushe suke cin abinci ba."
Numfasawa yayi ta kurbe tea din shi sannan ya cigaba da cewa."Sunan mahaifiyarshi *FADILA,* Sunan Mahaifinshi *MUHAMMAD* , Babana su biyu iyayensu suka haifa, shine babba, sai kaninshi Fadil, duk da Khamis ya girmi Fadil da shekara shidda, amman shakuwa da soyayya tashi ga tsakaninsu, sosai dan Khamis babu abunda ba zaiyi ba akan Fadil."
"Talauci yayi ma Muhammad katutu, wanda baida abincin da zai ciyar da iyalenshi, wannan dalilin yasa Khamis ya shiga kasuwa ya fara sana'ar *DAKO* , lokacin Khamis yana da shekar 16,shi kuma Fadil yana da shekara 10."
Rayuwa kenan, dama haka take Princess dan talauci baya dadi ko ya yake ko, dan ko idan Khamis yayi dako, sai ya raba kudin da yayi ciniki gida biyu, ka so daya yake boyewa, sai kaso daya ya sawo masu abincin da zasu ci shida iyayenshi."

"Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Khamis shi ke ciyar da iyayenshi, watarana ya samu da yawa, watarana kuma aka shin haka."

"Kinsan ance hannu daya baya daukar damai, aiko haka maganar take Princess, dan ko Khamis ya gaji da ciyar da iyayen shida yake duba da karancin shekarun shi, kuma ba wata sana'a mai karfi yake ba dakon nan dai shine yake yi har ya ciyar dasu, to kasuwar Dako ta tsaya sai suyi kwana biyu basu ci abinci ba, kuma Baban shi na kwanciya yayi ba shima yana nema amman baya samu, sai dai Khamis yayi bara ya samo abincin da zai ba kaninshi Fadil yaci, sai Fadil yaci ya koshi sauran da Fadil ya rage Khamis yake ci."
"Kawai watarana aka wayi gari, babu Khamis babu labarinshi, haka malan Muhammad ya sha neman dan nashi, amman bai sa mai shi ba, haka ya dawo yana kukan bakinciki."

"Tunda Khamis ya gudu gun iyayenshi, ya shiga sabuwar rayuwa, ya maida hankalinshi wajen neman kudin shi, a rana Khamis sai yayi kunsan 1000 duk rana indan ya shiga kasuwa yin Dako."
"Watarana a kwana a tashi, Khamis ya hadu da ubangida Alhaji Nurandden, shine mahaifin Ummana."
"Alhaji Nurandden, sunyi sabo da Khamis sosai, tunda ya lura Khamis mutun ne mai zuciyar neman na kai, bai dogara da abun wasu ba."
"Alhaji Nurandden, yaso  hana Khamis yin dako, amman Khamis yace ya barshi ya nemi kudin kanshi, ba dan yaso ba ya kyale Khamis yana dako kasuwa, Amman duk da haka sai da yasa Khamis a makaranta."
"Khamis, yana makaranta, yana zuwa kasuwa, lokacin yana da shekara 18,ya gama makarantar secondary school, ya cigaba da dakonshi, Alhaji Nurandden yaso ya shiga jami'a, amman Khamis yace shi daga secondary ya gama."
"Cikin ikon Allah, Allah yasa ma kasuwar Khamis albarka, dan Khamis yayi suna a wajen dako a kasuwa, dan yanzun Khamis ya saya motoncin da suke yin dako cikin ko wace kasuwar Kano, ko wace mota ansa mata suna *KHAMIS DAKO* ."


"Khamis, yayi suna cikin garin Kano, yana da shekara 25,ya gina gijajen haya, sanann ya saya *KEKE-NAPEN* , ya raba ma mutane ya suna ba shi balance."
"Soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Khamis da Maryam, lokacin maryam, tayi degree din ta affanin Likita, ba su dade suna soyayya ba, Alhaji Nurandden yayi masu aure."
"Bayan aurensu da shekara biyu aka haifeni, naci sunan kanin Khamis wato Fadil, bayan suna na, Khamis yaje wajen mahaifanshi, amman sai kash ya tadda basu nan, da ya tambaya aka ce mashi tsawon shekaru rabon da a san inda mahaifanshi suke ba, sun tafi sun bar kaninshi Fadil."


"Khamis ya tambayi ina shi Fadil din yake, suka ce yana wajen kanwar Babanshi, ya nemi gidan Ba'bar tashi amman bai samu ba, dan itama ta chaza unguwa, da man gidan haya take zaune."
"Khamis, yayi kuka, ya na da ya sanin tafiya da yayi ya bar iyayenshi, ba inda bai bada cigiyarsu ba, dan harda gidajen radio duk a je, ya sa kudi masu tsoka ga wanda yaga yan-uwanshi, amman shiru kake ji ba'a gansu ba."
Khamis yayi hakuri, ya barma Allah lamarinshi, ina da shekara 7 aka haifi Fadila, mun taso cikin jin dadin rayuwa, dan a Dubai mu kayi karatun mu baki daya, tun daga kan primary school har zuwa university, dan ni sai da nayi *M. S. C* a dubai, lokacin Fadila tayi degree din ta, ta karanci *B.S. C* *NURSING* , ni kuma nayi karatun *BARRISTER* , sannan muka dawo Nigeria."
"Bayan mun dawo Nigeria, Abba ya bude ma Umma hospital ita da Fadila, amman ita fadila tace ba dan tayi aiki tayi karatu ba, sai Umma Kawai take zuwa sunan hospital din *DOCTOR* *MARYAM PRIVATE* *HOSPITAL* , ni kuma ina yi ma gwannati Aiki."
"Yanzun haka Abba, ya tafi neman yan -uwanshi a wudil nan Kano, dan ya ji labarin suna wudil da zama, amman jiya nayi waya da shi yace ya kusa dawowa cikin satin nan ma, dan Allah bai sa ya gansu ba." kallon Rumaisa Fadil yayi sannan yace."Princess kinji Labarin Barrister Fadil Khamis Dako."numfasawa tayi sannan tace."eh Prince, naji labarinka, Kuma Allah yasa Abba yaga yan'uwanshi, Kuma Allah yasa suna cikin koshin lafiya." cewa yayi."Amin ya Allah Princess, da nafi kowa farinciki idan Abba yaga danginshi, amman Princess  tunanin ke yar kanin Abba  ne, amman ni bansan kanin nashi ba da na biki na gan shi ba Wanda ya sanshi mu duka gidan nan, sai dai labarinshi, dan haka in dan Abba ya dawo yaje gida ya ga Babanki, tunda da man zaije ya nema man aurenki, dan tunda kika ban labarinki nikeji yayi shige da wanda Abba ya bani akan yan'uwanshi." shiru Rumaisa tayi tana tunanin maganar Fadil, tabbs labarinsu yayi shige dan itama Babanta ce mata yayi iyayenshi da yayanshi sun gudu sun barshi shi daya sai Ba'ba Rumaisa data rikeshi, numfasawa tayi sannan tace." Allah yasa muji alkhari Prince." Murmushi yayi yana mikewa dan yaga marece yayi cewa yayi."Amin Princess, taso na maida ki gida, kinga dare ya fara yi." "to, mu tafi."
Bayan Rumaisa, ta gama abunda take ta kwanta, nan fa as usual suka yi wayar da su ka saba sanann suka tura ma juna text massage..

*Nisa tsakanin zukata biyu baya nufi shinge face yana tuna mana da kyakyawar alakar dake tsakanin mu. Ina kewar Ki princess 💖*

Bayan ta karanta ta maida mai da haka🤪

*Farin ciki mara misaltuwa kan ziyarci zuciyata a dukkan lokacin da na ji sautin muryarka, murmushinka babban abu ne da yake yayen damuwa, bana kasancewa dai dai da, shakar nimfashi ba tare da tinaninka ba a cikin zuciyata, kaine d’aya tilo da na damkawa ragamar zuciyata. Ni taka ce har abada, Ina son ka.💞*
Washe gari, bayan Rumaisa, ta gama yin aiki, Baba ya kira ta..
"Rumaisa.".."Naam Baba." Murmushi yayi sannan yace."naji komai daga bakin Maman ki, a kan maganar yaron nan Fadil, ta gaya man yanda suka yi da Mamanshi yaron, naji dadin haka sosai, amman dan Allah Rumaisa ki kula da mutuncin ki kinji."? cewa tayi."Eh Baba nagode sosai."

'''Wayyo Allah, Wallahi na gaji sosai😢, typing ba sauki, gashi kunce dole sai anyi maku read more 🙍‍♀️, ni kuma wallahi ban son ya wan typing sosai☺️, amman ai bakomai book ya zo karshe dan bai fi sauran yan pages ba, ya kare baki da'ya😍..
'''
'''Ina yinku my fans I love you wujiga-wujiga, dan comment din ku shi ke sa man kwarin giwar yi maku yanda kuke so 😁
'''

*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now