41&42

293 18 2
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

            

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_41&42

Bayan yayi parking wajen gidan su Rumaisa ya aika wani yaro yace yaje yace ana sallama da Rumaisa.
Tafiya yaron yayi yana sallama."Sallama Alaikum, ance ana sallama da Rumaisa."zaro ido Hindatu tayi, tana cewa."kaje kace wake sallama da ita."da saurin Rumaisa ta fito tace."kai wuce kace bata nan." nan yaron ya juya ya fita, tsaki Hindatu tayi sannan tace."aikin banza aikin wofi, yarinyar banza ana zuwa neman aurenki, amman kina tsayawa ruwan ido, kinfi son kije martin banza suna hawa suna sauka ana baki kudi, mtssss."duk da Rumaisa tayi abunda Hindatu tace, amman sai tayi kamar bata jita ba, ta koma dakinsu ta kwanta, ita dai sanan tayi ma su Hindatu nisa nesa ba kusa ba, dan haka bata da lokacin mai yin koda lokacinsu ne, yaron ne yaje yace ma Fadil."Ance bata nan."cikin damuwa yace ma yaron."ba tanan kace fa? Ko dai ba Rumaisa kace ba? Tunda gidan yawane."yaron cewa yayi."wallahi Rumaisa nace, amman sunce man bata nan."numfasawa Fadil yayi sannan yace ma yaron."To shikenan, nagode kaji boy, baka gaya man sunan ka ba."? Dariya yaron yayi, yaji Fadil ya ce mashi boy, cewa yayi."Sunana Malak."zaro ido Fadil yayi yana cewa."Woow suna mai dadi, ai nan ne unguwarku ko."?ɗaga mashi kai yayi sannan yace."Eh nan ne."shiru Fadil yayi na wani dan lokaci sannan yace."amman baka san Rumaisa ba."? Ce mashi yayi."Eh bansanta ba."shafa mashi kai Fadil yayi sannan yace."to bakomai, anshi wanann ka saya sweet."girgiza kai Malak yayi sannan yace. "Aa ka barshi nagode."murtuke fuska Fadil yayi sannan yace."kai zo nan ka ansa, ai ba tambaya ta kayi ba."sosai Malak ya tsorata da yanda yaga Fadil ya chanza mashi fuska lokaci guda cewa yayi."to nagode sosai."
Nan Fadil ya tafi office duk jiki a mace,dan  yaso ya ga Rumarshi ko yaji saukin abunda yake ji amman ba yanda zaiyi, in yaje office ya kira a waya...
Bayan fitar yaron Rumaisa kasa hakuri tayi har sai da ta fito tace ma Hindatu."daga yau ba ruwanki da duk wani yaron da aka aiko nazo, tunda bake baci uwata ba, da zaki ji waye, ba ruwanki in na fita, kuma ba ruwanki in ban fita ba, kuma idan ma ƙatin banza suke hawa suna sauka suna bani kudi, ba abunda ya dameki tunda ba kabarinmu daya ba, kuma ke ba uwata bace kamar yanda na fada maki can baya, ina fatan kin gane."rike baki Hindatu tayi tana salati sannan tace." Ke har ni zaki fadi ma haka."? Matsowa Rumaisa tayi kusa da ita sannan tace."An fadi maki, ba dai takaimarki sa ido ba? To yanzun ko na fara gaya maki haka indan har baki fita harka ta ba kinji dai na gaya maki."
Nan Rumaisa ta juya ta koma daki  tabar Hindatu da kunwar baki, ta shirya ta wuce warta gidan aiki, tana shiga ta fara gaida Umma....."Umma ina kwana."?murmushi Hajiya Maryam tayi sannan tace."lafiya lau Rumaisa, ya Mamarki."?...."Lafiya lau take, tana gaidaki.".."ina ansawa."
Nan ta cigaba da yin aikin gabanta, bayan ta gama gyra part din Umma ta wuce na Fadil.
Nan shima ta gyara mashi ko ina tas, ta chanza mashi bedsheet, sannan ta dafa mashi tea, da duk abunda take mashi, sannna ta wuce part din Umma suka shiga kitchen ita da Fadila.
"Kawata gaskiya yaya Fadil yana ansar gashi,  kinga yanda ya koma cikin kwana biyu kaɗa, amman duk ya rame yayi baki, yayi ba kyaun gani, ko abincin bai cika ci sosai ba."shiru Rumaisa tayi tana tunani sannan tace."Allah sarki masoyina, nima kullun ina cikin tunanin shi, kin san yau da safe sai da ya biyo ta gidanmu nice dai nace bani fita, ace mashi bani nan."murtuƙe Fuska Fadila tayi sannan tace."Haba kawata, gaskiya ki raga ma Yayanan nawa mana, wallahi tausayi yake bani, gashi har yanzun yaki gaya ma Umma matsalarshi sai dai yace bakomai ko ta tambaye shi."murmushi Rumaisa tayi sannan tace."amman ƙawata wai maiyasa Fadil yake da zurfin ciki."? Harararta Fadila tayi sannan tace."Nima bansaniba kawata,amman Yaya Fadil bai cika fadin matsalarshi ba, inko kinga ya fadi matsalarshi abun ne yafi karfin shi."
Cewa Rumaisa tayi."Ikon Allah, kowa da yanda Allah yake hallitarshi, shi kinga Yaya Fadil ga yanda Allah ya yi shi, tom shikenan Allah shige mana gaba."
Kallonta Fadila tayi sannan tace."Amin, wai kawata jiya nai ta kiran wayar amman switch off."? Murmushi tayi sannan tace."Eh ni na kashe ta, amman nan gaba zan kunna ta."ɗaga kafaɗa Fadila tayi sanna tace."ok any way, yanzun dai tunda mun gama  ta shi ki tafi gida, yanzun kinga yaya Fadil ya shigo."tashi tayi tana cewa."To shikenan, sai da safe."...."ok Mrs Fadil." hahhahah Fadila tayi dariya, murguɗa mata baki Rumaisa tayi sannan tace. "byeee Mrs Abdullah."dafe zuciyarta Fadila tayi sannan tace."uhmmm har kin san naji sanyi cikin zuciyata."dariya Rumaisa tayi sanna tace."Allah ya shirya ki Fadilar Yaya Fadil."..."Amin Rumaisar yaya Fadil."...."yau kuma eh mana."
Abdullah ne ya shigo office din Fadil, taddashi yayi yana tunani, kallon abokin nashi tayi sannan yace."Fadil wai bai dai Rumaisar bace har yanzun."? Kallonshi Fadil yayi sanna yace."Hmmmm Abdullah, Ruma so take ta kasheni kasheni da raina."zaunawa Abdullh yayi sannan yace."Subuhanalillah, lafiya kuma."? Yarfe zufar ta tayarmai yayi a goshin shi sannan yace."Ina fa lafiya yau kwana biyu kenan ban san Ruma a ido na ba, kuma wayarta ta kashe ta balle na rage zafi ko ta nan ne."numfasawa Abdullah yayi sannan yace."To kaje gidan su mana."kallonshi Fadil yayi, yayi tsaki marar sauti sannan yace."eh ai naje da safe, amman zan koma indan muka tashi, zan fara biya wa ta gidan su, in gani ko zan dace."cewa Abdullah yayi."To Allah yasa."...."Amin Abdullah."
"Assalama Alaikum."...."Amin wa'alaikumus sallama, Aaha Rumaisa har kin dawo? Naga kwana biyu kina dawowa da wuri."?zaunawa tayi tana cewa."Eh Mama yanzun ba wani aiki ke akwai ba mai wahala, shiyasa nike dawowa da wuri."...."To shikenan, Allah ya taimaka.".... "Amin Mama, Umma tana gaidaki."murmushi Mama tayi sannan tace."Allah sarki Hajiya Maryam badai zuminci ba ina ansawa,itadai mace ce mai son zumincin."..."aiko dai  Mama, Allah ya bata ladar zuminci."..."Amin ya haiyu ya kaiyimu."

Fadil ne ya biya office din Abdullah yana cewa."To ni Abdullah zan wuce, komai kenan sai munyi waya zaka ji yanda muka yi dan na fara gajiya da azabadta dani da Rumaisa take yi." ɗago kanshi Abdullah yayi sannan yace."To, idan ma ba ta bari ka ganta ba ka gaya man, ni zan saman maka solution yanda zamu bulo ma abun."cikin jindadi yace. "to byeee."
Bayan Fadil, ya isa kofar gidan su Rumaisa, ya kara aiken Malak yaje ya kira mashi Rumaisa...
"Sallama Alaikum."..."Amin wa'alaikumus sallama, shigo mana yaro."shigowa yayi yana cewa."ina wuni."? Cewa Mama tayi tana Murmushi."Lafiya lau, lafiya."?cewa Malik yayi."Wani ne ya aiko ni yana kiran Rumaisa a kofar gida."dasauri Rumaisa ta fito cikin daki tana cewa."Mama sannu da hutawa, kai wuce kace mashi bata nan."kallonta Mama tayi sannan tace."kai zonan."da sauri Rumaisa tace."dan Allah Mama ace mashi bani nan."harararta Mama tayi sannan tace. "kika san ko wanene."? Cikin shagwaɓe tace ma Mama. "Koma waye ace mai shi bani nan."girgiza kai Mama tayi sannan tace."to shikenan Yaro wuce kace tace ace bata nan."
da gudu  Malak yaje wajen Fadil yana cewa."Tace ace bata nan."kallon mamaki Fadil yayi ma Malak sannan yace. "ita tace maka bata nan  da bakinta."? Cewa yayi. "Aah ba ita bace." nan dai Malak ya fada mashi yanda Rumaisa tayi da Mama.  Zufa ce ta ketoma Fadil, furzar da iska yayi sannan yace."to shikenan nagode kaji Malak."
Shiga mota Fadil yayi, yayi har koma gida duk bai ji dadin abunda Ruma ke yi mashi kwananan, bayan yayi wanka yayi sallahr la'asar ya wuce part din Umma yaci abinci, ya dan huta sannan ta wuce masallaci sallahr magrd, bayan ya dawo daga sallah ya kira
Rumaisa amman still wayar kashe ta ke nan ya tura mata text messages

" *Haba Ruma ya kama ta ki tausaya man, karda ki sani cikin wani hali mana. Iluv uh..*

Bayan ya tura mata text messages, ya kira Abdullah waya....
Bayan sun gama gaisawa da Abdullah, yake gaya mashi yanda suka yi da Ruma da ya aiki yaro...
"Abokina shawara daya ce kawai kaje ka gaya ma Umma halin da kake ciki, na san Umma bata rasa abun yi."
Shiru Fadil yayi sannan yace."Ni bani san da ta sani har sai mun satanta kanmu nida Ruma."cewa Abdullah yayi."Ai ba lokaci Abokina, tunda ita Rumaisa taki ta baka hadin kai, ai kawai kasa manya a cikin maganar, dan haka kaje ka gaya ma Umma  matsalarka kawai Fadil."cewa Fadil yayi."To shikenan, yanzun dare yayi, tunda gobe week end zan gaya mata da safe insha Allah."..."Allah ya yarda, nima yau zan gaya ma Fadila halin da ake ciki muga, ko za'a samu solution."shiru yayi na wani dan lokaci Sannnan yace."Ok, Abokina, nagode sosai, sai da safe..

*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now