35&36

297 24 5
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
   _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

            

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_35&36


Hawayen fuskar shi Fadil ya goge sannan ya kalli Rumaisa yace.""Ayya, yi shiru Ruma, yi hakuri pls, tabbas Ruma labarin rayuwarki tana da abun tausayi, Allah ya jikan Khamis, Allah yasa mutuwa ta zamu hutun shi."
Ɗago kanta tayi daga tsugune, kallon shi tayi,gira ya ɗage mata yana mata nuni da ta goge hawayen fuskarta, goge hawayen tayi sannan tace."Amin Yaya Fadil nagode sosai."murmushi yayi yana kallonta, dan natsuwarta tana kara mashi sonta, cewa yayi."Ruma yanzun haka kuke rayuwa cikin wannan yanayin?kuke zaune a cikin gidan haya."? Wasa take da yatsan hannunta, tana murmushi dan ita ai ta saba da gidan haya, ita da aka haifa a gidan haya ta taso a cikin shi ai ba abun mamaki bane, cewa tayi."Eh har ma ni nasa ba zaman GIDAN HAYA."shiru yayi na wani lokaci, dan parlourn shiru yayi kamar ba mutane a ciki, ji tati yace. "Allah sarki."kamar ba shi yayi maganar ba, dan wani waje yake kallo na daban, kallon shi Kawai take tana mamakin halin shi ace yayi magana kamar ba shi bane yayi taba, tana cikin tunanin taji yace."Ruma inasan nayi wata magana dake fa."kallonshi ta sake yi sannan tace."to yaya Fadil ina jinka, Allah yasa muji alkhari."murmushi yayi Wanda ya ƙara mashi kyau da haiba da kwarjini, waigowa yayi yana kallonta sannan yace."Eh alkhari ne Ruma, amman banson ya zaki dauki magana ta ba, da man ba wata magana bace, uhmmm Ruma."ji yayi ya kasa maganar ma, amman yasama ranshi duk rintsi yau sai ya gaya mata abunda ke cikin ranshi, shima ya dan huta, cewa tayi."Naam yaya Fadil ina sauraranka."murmushi yayi ya sake daga inda yake yaje ya haɗo masu black tea mai zafi,wanda bai cika sugar ba, dawowa yayi ya zauna sannan ya bata yace."anshi nasan zaki bukaci wannan Ruma."dariya tayi sannan tace."ina godiya sosai Yayana."ansa tayi ta dan kurɓa sannan tta ajiye a gabanta tana kallon shi, tana jiran abunda zai ce mata, murmushi yayi da ya kalleta dan ya lura ta ƙagu ya gaya mata abunda yace zai gaya mata ko zata tafi gida, shi kuma bai san  tace zata tafi, daurewa yayi yace."Ruma ina sonki."zunbur tayi tana kirma sosai sannan tace."Yaya Fadil."abun dariya yaso ya badashi yanda ta rude cikin minti ɗaya, tea ya dauka ya bata rike tea din kawai tayi amman ta kasa sha, fahimta yayi da ba sha zatayi ba yace."eh Ruma ina sonki, ina kaunarki Ruma, rasaki shine barazanar dauke war numfashina."tashi tayi tana girgiza kai sannnan tace."Yaya Fadil, amm.... "tabbas Ruma."katseta yayi, sannnan ya cigaba da cewa."Ruma ba mafarki kike ba, da gaske ni ne Fadil durkushe a gaba ina nema samun mazauni  a cikin birnin zuciyarki, ki taimaki ne ki anshe ni hannu biyu please RUMAISA."
Kallon shi tayi duƙe a gabanta, nan fa Rumaisa ta tashi ta fita da gudu tana kuka, ita dai shin farin ciki zata yi ko mai, haka ta shiga dakin Fadila da gudu tana kuka, kallonta Fadila, sannan ta tsinke wayar dasu da Abdullah, tace ma Rumaisa."Lafiya? Rumaisar Mama, naga kin shigo da gudu kuma kina ta kuka."?ƙara rushewa da kuka Rumaisa tayi sannan tace."Fadila na shiga ukuna, na lalace shikenan na gama aiki a gidan nan." dirowa tayi daga bisa gadon, taje wajen Rumaisa jijigata tayi tana cewa."na bani ni Fadila, Rumaisa wa ya mutu? Gaya man dan Allah Rumaisa."kallonta tayi ta kwanta bisa cinyar Fadila, tana hawaye sannnan tace."Fadila ba wanda ya mutu, amman Yaya Fadil ne."ƙara ruɗewa Fadila tayi, taji ance Yaya Fadil, cewa tayi."Yaya fadil kuma?wani abu ya samaishi ne? Na boni ni Fadila."girgiza kai Rumaisa tayi sannan tace."Aah Fadila ba abunda ya samai shi, kwantar da hankalin ki."numfasawa Fadila tayi sannan tace."to gaya man lafiy? duk kin sani cikin damuwa, da ruɗini Rumaisa."kuka ta sake tashewa dashi sannnan tace."Fadila, wai Fadil yace yana sona." ta ida fadi tana kuka sosai, dariya Fadila ta fashe da ita sannnan tace."haha daman dan wannan abun kika shigo duk kika tada man hankali."? Cigaba da cewa tayi tana dariya."Ai da man tuni na gaya maki yaya Fadil Sonki yake, amman sai ke kice man ba wani kawai jininku ya hadu, to ai yanzun kinga haduwar jinin ko Rumaisar Mama?  hahhahhahha."tashi tayi tana goge hawayenta sannan tace."Amman Fadila... "shhhhh, yi man shiru na baki shawara a matsama na yar'uwarki, Rumaisa karda ki kuskura ki gyale yaya Fadil, ki anshi Soyayyarshi, in kuma kika tsaya kunya da wasa, to kina nan zaki ji ya samu wata ya aura,dan haka shawara ta rage naki."kallon Fadila tayi tana girgiza kai sannan tace."Fadila, yaya Fadil ba sa'ar aure na bane, yaya Fadil yafi ni komai, shi dan hutune dan masu hannu da shuni, karki manta ni yar'aikin gidan ku ce, kinga bai dace ace na buge yin soyayya da dan masu gida ba, ku......"Rumaisa, ashe matsayin da muka ba ki a gidan nan ke ba haka kika dauke shi ba? Rumaisa mun daukiki yar'uwa bamu nuna maki banbanci, amman duk da haka kina yi ma kanki kallon yar'aiki a gidan nan."? Zatayi magana Fadila ta katseta ta cigaba da cewa."A she yaya Fadil bai da arzikin da zaici darajar Umma ki aminta da Soyayyarshi ba, tabbas Rumaisa baki yi mana adalci ba, kuma banji dadin jin haka daga bakin ki ba gaskiya."saurin rufe mata baki Rumaisa tayi sannan tace."Fadila dan Allah kiyi hakuri, wallahi banyi tunanin rainki zai baci har haka ba, nima na baku matsayi mai girma a rayuwa, har abada ba zan manta da hallacin ku daga gare ni ba, kawai dai sai naga kamar banga dacewar mu ba da yaya Fadil."kallonta Fadila tayi sannan tace."Mungode da matsayin da muka samu, Rumaisa kinga na tsuguna giwowi na duka biyu in ma kina so zan dafa kafafunki ki taimaka ki Aminci ce Yayana."ɗago ta tayi tana cewa."Subuhanalillah, Fadila dan Allah ki mike tsayi, wallahi kin fi garfin komai a wajena, ai bun kunya ne naki dan uwanki, naso wani, Amman ina san ki bani dama nayi shawara da su Mama."murmushi Fadila tayi sannan tace."To shikenan Rumaisar Mama, Allah yasa muje alkhari, Amman dan Allah ki tausayama Yayana."tashi tayi tana cewa."to ni Fadila na wuce gida sai gobe." tashi Fadila tayi, ta tafi wajen Umma tana cewa."Umma albishirinki."? Kallonta tayi sannan tace."Goro."cewa tayi."fari ko ja."? Cewa Umma tayi."Fari tas da shi ma."dariya tayi sannan tace."to Umma yau dai yaya Fadil yace ma Rumaisa yana sonta."murmushi Umma tayi sannan tace."Alhmdulh Allah nagode maka, gaskiya na baki kyautar MOTA cikin new motors din da aka kawo jiya, amman ita Rumaisa mai tace mashi."?cewa."nagode Umma, ita bata ce komai ba, wai sai tayi shawara da Mama."cewa Umma tayi."Da kyau bani son ta bashi ansa dan yanzun har sai na ida tabbatarwa da kallar son da yake mata, dan ni na haifi Fadil na san waye shi, shi mutun ne mai wuyar fahimta."dariya Fadila tayi, sannan tace."To shikenan Umma, haka za'ayi, zan sa ta gara shi yanda ya dace, shima ya san yanda ake san wuya wajen neman aure."cewa Umma tayi."yauwa albarka haka nike son ji da man."
Tunda Rumaisa ta koma gida, ta kasa yanda zatayi, daurewa tayi sannnan tace."Mama da man ina son na gaya maki wata magana."kallonta Mama tayi sannan tace."wace magana ce haka Rumaisa? Fadi inajinki." kallok Mama Rumaisa tayi sannan tace."da man Fadil ne."kallonta Mama tayi sannan tace."Fadil ne mai wani abu ya sa mai shi."?cewa tayi."Aa da man ce wa yayi yana sona."tashi Mama tayi sannnam tace."Yana sonki fa Rumaisa."? Kallon Mama tayi sannnan tace."Eh Mama."zaunawa Mama tayi sannan tace."Rumaisa kiyi hakuri da Fadil, dan Fadil ba sa'an aurenki bane, ko ke baki lura ba."?cewa tayi."Mama ni ma haka nace ma Fadila, amman sai ta nuna bacin ranta, wai ashe ban dauki matsayin da suka bani ba, har da tsugun nawa tayi kasa tana neman alfarman na so Yayanta."shiru Mama tayi, dan itama ta hango hallacin mutanan gidan, take jikinta yayi sanyi sannnan tace."To shikenan Allah yayi maki albarka, Allah yasa shine alkharinki."cewa tayi."Amin Mama, ni zan kwanta sai da safe....












*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now