19&20

363 24 1
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

    _STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_19&20

Tunda Rumaisa ta tashi bacci ta shirya ta wuce gidan aiki, sai da ta gama komai sanann ta wuce room din Fadila kwance ta tadda Fadila tana danna waya cewa tayi yana zama."Kawata gaya man matsalarki, naga kamar kina cikin matsala."? Murmushi Fadila tayi sannna ta tashi zaune tana cewa."Eh Rumaisa, amman ba wata matsala bace mai girma ba, amman abun yana damuna."kallon Rumaisa tayi yana mamakin wannan abun da yake damun ƙawarta cewa tayi tana mai dafa Fadila."Ayya maiye ke damunki har haka? Inasan naji komai ne wannan abun Fadila."girgiza kai Rumaisa tayi sannan tace, cikin damuwa."Rumaisa, wani saurayi nayi kwannan, yana sona, amman nidai sai naga kamar bamu dace ba."kallonta Rumaisa tayi tana mamakin kalmar basu dace ba, ce mata tayi."Kamar ya baku dace ba? Bai da hali mai kyau ne? Ko kuma kawai bai yi maki ba Fadila."? Murmushi mai ciwo Fadila tayi sannan tace."Ko daya Rumaisa, Abdullah yana da kirki, duk da wannan zamanin baka yaban halin mutun koda ko uwarku daya, amman ina yi ma Abdullah kyaun zato."numfashi Rumaisa ta sauke sannan tace."Maiye to matsalar, da har kika ce *BAKU DACE* *BA* ? Abun da mamaki Fadila, tunda kince yana da hali mai kyau."kallonta Fadila tayi, sannna tace."Hmmm ba zan boye maki ba, inason Abdullah, abokin yaya Fadil ne, shima yana sona, saboda ya dade yana dakon sona, dan ni daga baya yake baiyana man sirin da ke cikin zuciyarshi,Abdullah yace yana sona, har nayi accepting din shi, mun fara soyayya, sai shekaran jiya wata yarinya ta turo man wani text marar dadin karanta wa, wai Abdullah yake yi mata kalar wannan maganganu banza, wanda basu da dadin ji,u
yace yana sonta,sun jima suna soyayya sai kawai taji labari gun abokanshi wai ni yake so yanzun ba ita ba, bayan ya gama yaudararta, ya gama bata mata rayuwa, shine yanzun zai juya mata baya ya dawo wajena, shine abun ke bani mamaki, wallahi abun yana damuna, bansan ya zanyi ba, shine nike neman shawarki Rumaisa na kyale Abdullah ko kuwa na cigaba da son shi."? Numfasawa Rumaisa tayi sannan tace."Uhmm, gaskiya dole kiyi mamaki, sannan kuma dole kiji kishi, amman a tawa shawarar shine karki rabu da Abdullah, a hankali in dai halinshi ne watarana dole a sirin shi ya tonu nidai a nawa tunanin kenan, dan kuwa komai yake dole watarana ki gane Fadila."Shiru Fadila tayi tana tunanin maganar Rumaisa sannan tace."Shikenan, Rumaisa yanda kika ce haka zanyi, tabbas Rumaisa ke din yar'uwata ce kuma aminiya, ina ma hmmm... MurmushibRumaisa tayi sannan tace."Ina ma mai kena? naji kin fara magana kinyi shiru."? Dariya Fadila tayi sosai sannan tace."Bakomai watarana Insha Allah zani gaya maki."cewa Rumaisa tayi.ok shikenan ni na wuce gida kinga mangarib har tayi." "ok byeee."
Haka Rumaisa tayi Sallama da Hajiya maryam ta gama gabanta zuwa gida, gidan nasu na *HAYA* mai mutane kala-kala..
Wani kallo Lami tayi ma Rumaisa tana dariya  sannan tace."Bita zai-zai kenan, har mundawo kenan Hindatu daga aiki."? Dariya Hindatu tayi sannan tace."Ai'haiye na naye, Lami kenan, mun dawo zamu shiga daki mu zauna kamar wasu mararsa gaskiya haha haha."dariya Lami tayi sanann tace."Yo daman gaskiyar ke gareki Hindatu?  anfita tun safe antafi wajen maza, sai yanzun aka dawo mana da nadasa a cikin gida ai dole ki shige daki."dariya sosai Lami tayi sannan tace."Ke dai bari Halimai, haka za'akare dai, ba'a gun wancen katon, ba'a gun wancen gardin ina ma amfani."cewa Halimai tayi."babu anfani Lami, Allah yasa mu gane dai."
Ita dai Rumaisa inda suke basu isheta kallo ba, ta shigewarta daki suka ci abinci tayi sallah ta kwanta suna labari da Mama suna cikin labari Baba ya dawo nan suka zauna sukayi fira sannan suka kwanta bacci..
Washe gari, yau Rumaisa ta tashi da wani zazzabi marar dadi, Wanda ya hana ta zuwa gun aiki..
Mama ce tace."Sannu Rumaisa, gaskiya kina jin jiki, kodai mu tafi asibiti."? Girgiza kai Rumaisa tayi sannan tace."Aah Mama ba sai munje ba na fara jin sauki."cewa Mama tayi."Aa Rumaisa kidai tashi muje a duba lafiyarki, har yanzun ace mutun baya son ya asha magani."cewa Rumaisa tayi."naji sauki Mama, insha Allah ma zuwa anjima zani isilamiya."cewa Mama tayi."To shikenan Allah ya baki lafiya, bari na tashi na dama maki fura ki sha, sai ki sha magani."cewa tayi. "to shikenan Mama."Mama tace."Kwanta bari na tashi."girgiza kai tayi sannan tace."sanyi nike ji sosai Mama."Mama tace."to bari na lulubaiki, Allah ya baki lafiya kinji yar albarka."

*********************
Fadil ne yace ma Umma."Umma."..  "Naam Fadil wannnan kiran fa."? Cewa Fadil yayi."Wai ena Rumaisa ita nike jira tun dazun, amman har yanzun bata gama yi maku aikin ba."? Kallon shi Hajiya maryam tayi tana mamaki yanda Fadil yake nuna damuwarsa a fili a kan Rumaisa cewa tayi."Au ai duk yau bata shigo ba, inajin wani abu mai mahinmanci ne ya tsada ta shiyasa bata shigo ba."shiru yayi yana mamakin abunda zai hana Ruma zuwa yau, amman adduarshi Allah yasa lafiya, cewa tayi."To shikenan Allah yasa dai lafiya,mai kuka yi mana breakfast."?cewa tayi." Soyayen Irish mana Fadila tayi mana, gashi can dinning in zaka ci."
Cewa yayi."Nidai bani son Irish, ina awarata?  ita zanci kawai, amman gaskiya na koshi da wannan Irish din."kallonshi Umma tayi sanann tace."Shin kai dai kasani Fadil, tashi Ka ban waje ni, ka kira Fadila ta soya maka warar, kai ka dauki ta duka ka maida ta gunka, ka ringa soya abunka da kanka."cewa yayi."Ummma yanzun ita Fadilar bata soya man."? Cewa tayi."Eh gaskiya, dan yau Fadila ta gaji sosai ita daya tayi aikin gidan fa."tashi yayi yana cewa."to shikenan ni zan wuce na soya kayana, tunda ni na damu."cewa Hajiya maryam tayi."kai dai akeji Fadil."

*********************
Mama tace ta shigo tana cewa."Tashi kisha fura, ga magani nan sai ki sha."cikin jin raɗaɗin ciwo Rumaisa tace."Mama ni.... "ke mai Rumaisa, wahala zaki bani ko? Ke dai in baki lafiya shikenan baki kara cin abinci balle magani, haba ai yanzun kin girma, tashi ki ansa kafin raina ya baci."tashi tayi tace."to Mama."murmushi Mama tayi tace. "yauwa ko kefa.."haka taci abinci sannan ta sha magani ta koma ta kwanta, koda dare yayi Babanta ya dawo cewa yayi."Sannu Rumaisa."cewa tayi."yauwa Baba, ka dawo lafiya."? Cewa yayi."Lafiya lau ya jikin."?cewa tayi."Da sauki Baba."dafa koshinta yayi sannan yace."Allah ya baki lafiya."kallon Mama yayi sannan yace."Maman Rumaisa gobe Insha Allah ki kai ta chemist din Bala ko allura yayi mata muga yanda hali zaiyi."cewa Mama tayi."to shikenan Allah ya kaimu goben Lafiya." "Amin ya Allah."

*********************
Fadil ne ya shigo part din Hajiya maryam, zaunawa yayi ya fara gaida Mahaifiyar ta shi sannan yace."Umma." kallon shi Umma tayi sannan tace."ina jinka, lafiya."?Sosa ƙeya yayi sannan yace."Eh to Umma, amman kinga duk yau Rumaisa bata zo ba, Allah yasa lafiya."Murmushi tayi sannan tace."Amin ya Allah, nima abunda nike tunani kenan, abunda Rumaisa bata taba yi ba, in bata zo yau ba,  gobe sai muje muga ko lafiya."cewa yayi."To shikenan Allah yasa dai lafiya."cewa tayi."Amin tashi kije ki kwanta dare yayi, nima sai da safe."
Cewa yayi."ok Umma byeee tooo."





_*Ina masoyana suke😘masoyan yar'mutan kankia, wanda suke fadin yar'mutan kankia itace tauraruwa a social media, nice dai yar'mutan kankia wanda ta kawo maku NANA JAWAHEER, karku manta irin soyayyar da aka sha da Sadiq da Nana, sannan kuma ta sake kawo maku shahararrin litafin nan nata wato GIMBIYA HAKIMA inda aka zuba soyayya Hakima da Hakim, sannan kuma ta kowo maku SANADIN LINK, inda Sofy ta cancaɗa soyayya da Aliyunta, ba tayi ƙasa a gwiwa ba tazo ta kawo kamu IZZAH KO MULKI, inda kukaga yanda ake mulkin zalinci, sannan kuma kuka ga yanda ake makirci iri iri, ga ban tausayi dai dau abubuwa a cikin Izzah ko mulki.*_

_*Yanzun kuma take kawo maku A GIDAN HAYA, wanda A GIDAN HAYA aka fara wasan dan ko ba'ayi komai a cikin shi ba😁, uwa uba kuma ga SADAUKIN BURHAAN, wowowoho!!!! SADAUKIN BURHAAN kenan karku manta cigaban Izzah ko mulki ne, inda zakuji ina Sadauki yaje? Wata kallar fansa Sadauki zai dauka? Abubuwa da dama fa😘, To Masoyana anan zaku nuna man soyayyar da kuke cewa kuna yi man, domin ku masoyana, zan baku GARAƁASA! GARAƁASA!! GARAƁASA!!!  Daga yau 10/9/2020 zan sakar maku da Sadaukin Burhaan akan naira 200kacal, karku manta naira 300 nasa shi to duk domin ku masoyana mai doshi 200 daga yau tara ga wata zuwa ashirin da ɗaya ga wannan watan na satuba 31/9/2020 an single kenan, yan vips kuma nai maido maku shi akan naira 400,karku manta daga yau 9 ga zuwa 31 ga watan September din nan insha Allah.*_

_Wata GARAƁASAR kuma masu bukatar karanta Izzah ko Mulki yanda zasu ji dadin karanta Sadaukin burhaan su fahimci ida labarin ya dosa zaku bada naira 100 kacal ba baku document din sa, kunga kenan idan single ki saya Sadaukin burhaan zaku bada naira 300 duk da Izza ko mulki, idan kuma sadauki kawai kike bukata zaki bada dari 200 kawai, idan kuma vips ne zaku bada naira dari 450 duka biyun kenan sadauki da izzah ko mulki idan kuma sadauki kawai kike bukata zaki bada naira 400 kawai  Masoyana karku manta tana nan ne kawia zaku nuna man kaunar da kuk cewa kuna ma NOVELS dina, sannan kuma Hausawa sunce sayan na gari mai da kudi gida😍, ina maraba daku MY GUYS🥰_


*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now