24&25

340 28 1
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
  _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

            


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_25&26

Dariya Fadila tayi sannan tace."Eh munji haka muke, mu mutane, ai daman ita soyayya a cikin ido ake ganin ta, kuma wallahi keda yaya Fadil ana kallon idanunku za'aga son jununku, amman nan gaba zaki fahimta."tsaki Rumaisa tayi sannan tace Fadila."ke dai kika sani, amman kisa nidai ba wani wata fahimtar haka wai ana ganin soyayya a idanu, kuma ni nasan Yaya Fadil ba sona yake ba tausayina ne kawai yake, nima haka ba sonshi nike ba, ina mashi kallon Yayana,dan haka Fadilar yaya Fadil wallahi  kibar yi man haka."
Taɓe baki Fadila tayi sannan tace."To shikenan Rumaisar Mama zamu gani nan gaba."shiru kawai Rumaisa tayi mata, dan taga komai zata ce ma Fadila ba yarda zatayi ba, kawaai tana ɓata lokacin ta ne wajen yi mata bayani, ji sukayi Umma na cewa."Fadila fito mu wuce dare ya fara yi."cewa tayi."to Umma, kawata sai kin shigo goben,amman ki sani ina kan bakana, Yaya Fadil yana sonki, kuma nan gaba zaki ce ni Fadila ni na gaya maki, na barki lafiya."cewa Rumaisa tayi."to kawata, Amman kisani Yaya Fadil baya sona, kumaa kema nan gaba zaki sani."dariya Fadila tayi sannan tace."haka zaki ce daman, amman mu dukanmu mu bari idan muna da rabon ganin gaba duk zamu gani."suna maganarsu har suka iso parlour Rumaisa tace."Aunty mungode sosai, Allah ya bar zuminci."cewa Umma tayi."Amin Rumaisa, yauwa zo ki ansa wani sako Rumaisa."cewa tayi."to Aunty."Mama ce ta tashi yana cewa."Hajiya mungode sosai, gashi mai gidan baya nan bai Kai da dawowa ba, da kun gaisa."cewa Umma tayi."bakomai Maman Rumaisa in ya dawo kin gaisheshi."haka Mama ta rakosu har kofar gida, sannan ta juya, ita kuma Rumaisa har bakin mota taje, nan Umma tace."Rumaisa anshi wannann, kin gaida Babanki in ya dawo kinji."? Ansa tayi tana cewa." to insha Allah Aunty, nagode sosai."cewa Umma tayi."bakomai Allah ya kara baki lafiya."..."Amin ya Allah, ƙawata sai goben ko."? Murmushi Fadila tayi sannan tace."eh ƙawata Allah ya kaimu."...."Amin ya Allah, Yaya Fadil nagode sosai."Rumaisa tace tana shigewa gida, suma suka kama hanyar gida, koda ta shiga gida, dakinsu ta shiga sannan tace."Mama kinga abunda Aunty ta kawo man, ga kuma abinci nan duk sun kawo, Allah ya saka masu da alkhari."cewa Mama tayi."Amin Rumaisa, gaskiya Hajiya Maryam tana da mutunci sosai, Rumaisa ji yanda ta saki jiki ta zauna muke ta labari bata jin komai ba."cewa Rumaisa tayi."ai haka take Mama."Mama cewa tayi."gaskiya taji dadin halin ta."haka sukai ta labarin su har Baban Rumaisa ya dawo, aka gayamashi.
Washe gari, tunda safe Rumaisa ta tashi ta shirya, tayi wanka da aikin da take yi ma Mama, sannan wa wuce gidan aiki...
Bayan taje ta gaida da Hajiya Maryam, sannan ta fara yin aikin gida sai da tagama yin komai a part din Hajiya sannan ta shiga dakin Fadila...
"Kawata tashi hakanan mana."Fadila ta tashi tana cewa."oyoyo ga kawata, wallahi nayi missing dinki sosai."itama Rumaisa cewa tayi."nima haka kawata, kiji dadi sai bacci kike."cewa Fadila tayi."wani bacci yanzun na samu na kwanta kika
shigo kuma."kallonta Rumaisa tayi sannan tace."Ikon Allah, hala waya kika tsaya yi da Abdullah ko."? Ƙara kwanciya Fadila tayi ta rungume pillow sannan tace."Eh mana wai bacci yake so ya koma ya kasa shine ya kira ni na sashi baccin."dariya Rumaisa tayi sannan tace."eyyye ha haha kawata masoya,anyi nisa ba'ajin kira."cewa Fadila tayi."eh bakomai, ai mu mun bai yana tamu soyayyar ba kamar ta wasu ba da suke cutatar kansu."shiru Rumaisa tayi sanna kuma tace."Ke dai kika sani Fadila,  ni na wuce gun yaya Fadil na fara yin aiki karda na makara wajen tsayawa jin shirman ki."dariya Fadila tayi sannan tace."Ba wani nan kedai kice kin tafi kiga sinadarin rayuwarki."tafiya Rumaisa tayi tana cewa."ke dai kika sani Fadilar yaya Fadil."dariya Fadila tayi sannan tace."muka dai sani baki dayan mu Rumaisar Mama."ita Rumaisa tana mamakin yanda Fadila take haɗata da yayanta, bayan ita tasan ba abunda ke tsakaninsu sai dai mutunci, da tausayinta da Yaya Fadil yake, haka tai ta tunanin ta har ta shigo part din shi, tana cewa."Hello, yaya Fadil, sannu da hutawa."waigowa yayi yana cewa."oyoyo ga Ruma welcome back, gaskiya munyi missing din ki sosai."murmushi tayi tana cewa." nima haka yaya Fadil,gaskiya yaya Fadil kuna da mutuncin sosai, baku da wulakanta tallkawa."kallonta yayi sannan yace."haba Ruma maiyasa kike kallar wannan magana? Ai ke kin zama yar gida kuma yar uwa."murmushi tayi tana cewa."To nagode sosai."nan Rumaisa ta fara yin aiki bayan ta gama ta zauna sunata labari ita da Fadil, suna kallon wani film a MBC BOLLYWOOD, ko wannan su film din yayi mashi kyau saboda soyayyar da ake yi cikin film din, sai da suka gama kallon film din baki daya sannan tace."yaya  Fadil ni zan tafi."cewa yayi."ok Ruma sai gobe ko."!? Cewa tayi."insha Allah byee."
A kwana a tashi, shakuwa mai tsanani ta shiga tsakanin Rumaisa da Fadil , wanda takai da bamai sun yaga dan uwanshi cikin bacin rai, ko wani hali na daban...
Fadil ya saya ma Rumaisa waya, in ba gidan su, to suna tare da waya, sai sunyi wayar awa biyu, ammn duk a cewar Rumaisa haduwar jini ce ita da Fadil."
Rumaisa tana zaune ita da Fadila suna labari sai kawai Fadila ta hau cewa."Rumaisa! Rumaisa!! Rumaisa!!! Wallahi soyayya kike da yaya Fadil, in kuma ba soyayya bace mai ce?  kagaya man."kallonta Rumaisa tayi sannan tace."wallahi kin tada man hankali irin wanann kiran dakika yi man, kuma gani gaki, nasan wani abu kika gani ma."cewa Fadila tayi."nidai ba wannan na tambayeki ba, soyayya kuke da Yaya Fadil, idan kuma na soyayya bace mainene."? Tsaki tayi sannan tace."Ni fa ba wata soyayyar da muke na ce maki haduwar jini ce da kuma tausayi haba."cewa Fadila tayi."to shikenan na yarda haduwar jinice."
Ita ko Hajiya Maryam tuni ta gama gane takun Fadil, tana mamakin yanda Fadil  ya fada kogin son RUMAISA ita abun yayi mata dadi sosae.
Dan ko idan har abunda take tunani ya tabbata sai tafi kowa farin ciki, dan dama tuni take ma Fadil shi'awar auren Rumaisa..."Mama ni zan tafi, insha Allah daga nan zamu wuce kitso nida Fadila."Rumaisa ke cema Mama tana sa hijab zata wuto gidan aiki, cewa Mama tayi."to shikenan Rumaisa adawo lfy.".."Allah yasa."
"uhmmm ta bizaro,,an tafi yawau ta zibar da aka saba, yo ni Halimai Allah ya sawaka ina anfani ƙwaƙwa."? Halimai da fitowarta kenan, daga dakinta take wannan maganar ko kalaci batayi ba, amman ta tsaya tsokanar faɗa.
Hindatu ta amshi maganar tana cewa."Kin dai ji ye man Halimai, ai karshen duniyar kenan, yanzun da sanin iyaye yara ke yin karuwanci."
Cewa Halimai tayi."Hakane Hindatu, kinga dai yanzun an tafi sai kuma hali ya nuna za'a dawo."tsaki Lami tayi sannan tace."oni Lami ina ganin karshen zamani..... 







*Yar'mutan kankia ce ❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now