End

360 18 2
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_____________________________

      
*Alhmdullilah, laifin dadi kwarewa, nasan zakuce nayi maku shortcut har nazo last page🥱, to naji ance on 12 akeyin resume din makarantu, shiyasa nayi haka, inason na baku ƁAROWO NE, bansan ina cikin yi a koma school na ajiye maku typing ba batare da na gama ba, nidai abunda nike ku dauka a cikin novel din A GIDAN HAYA shine ba kyau HASSADA, bata da amfanin shine darasin da nayi niyar isarwa a gareku sai kuma ka mutunta mutun ko ya yayake dan baka san waje shi ba a duniya da kuma wajen ubangiji, kunga yanda ta kasance da Rumaisa da su Halimai, su Halimai suna mata HASSADA sai ga Allah ya daga Rumaisa ta zama wata, tama tashi a gidan haya baki daya, sai kuma su Fadil kunga basu wulakanta Rumaisa ba a matsayinta na tallaka sun janyota a jiki sun nuna mata duk daya suke Allah cikin ikonsa sai yanuna masu wacece Rumaisa a wajensu, kunga da sun wulakanta ta da sunji kunya sosai, konan zaku gane ba kyau wulakanta dan'adam dan baka san matsayin shi ba, FATANA WANNAN SAKON NAWA YAJE GAREKU, dan ba cewa Yayi dadi ba, Jameey kin iya novel A'a nafiso ku dauki darasin dake ciki😊🙏*

*Insha Allah cikin satin nan , zan fara posting din ƁAROWO NE, ina gama shi ban sake wani posting har sai 2021 insha Allah, itama 2021 din sai anyi mana hutun school sannan zakuji, nidai nasan ko ina nike masoyana suna tare dani, kamar yanda nima ina tare daku 🖤❣️*
     

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

🔚🔚🔚

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Aiyan ya girma dan yanzun yana da shekara 3 a duniya, yaro ne fari mai kama da Baban shi..


Deejat ce zaune tana ma Fadila rigima tana cewa."Ammi, ni yau sai kin kaini gidan su Yaya Aiyan."kallonta Fadila tayi sannan tace. "haba Deejat da mai zanji da wanann cikin zanji ko kuma da rigimarki, ke kullun sai kinje gidan su Aiyan, to ni na gaji da rigimarki, dan na kusa bugunki cikin gidan."kuka Deejat ta farayi ma Fadila, aiko Fadila, tayi ma Deejat jan ido, sannan ta sha fama mata lafiya, dan yanzun Fadila tana fama da cikin dan wata shidda....




Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, sunata zumincin su, dan Rumaisa da Fadila, yanzun sai abunda yayi gaba, basu boye ma junan su duk halin da suke cike...

Fadil ya sa Rumaisa a university a nan buk kano, ta karanci *MASS* *COMMUNICATION* , shiyasa ita bata kara daukar ciki ba saboda tayi planning, har aiki duk ya nema mata, dan tana aiki a court din su yanzun haka, tare suke zuwa aiki su dawo tare...

Har makkah Rumaisa taje, bayan ta dawo suma su Baba suka je makkah, bayan dawowarsu ne Allah yayi ma Alhaji Muhammad rasuwa,  sunyi kuka sunyi hakuri, dan Allahn da ya basu ya fisu san shi, kuma ya anshi abunsa.....


Fadila ta haihu, ta haifi d'a namiji ansa mashi suna Abubakar, suna kiranshi da shi, ita kuma Deejat ta koma da zama gidan su Aiyan....

Yanzun Rumaisa tana da cikin dan wata hudu, cikin yana bata wahala sosai, dan ko cikin Aiyan bai bata wahala ba kamar wannan, dan haka sai da ta dauki hutu gun aiki, sai bayan ta haihu sannan....

Bayan wata shidda, Allah ya sauki Rumaisa lafiya, ta samu diyarta mace, ranar suna taci sunan Maryam, suna ce mata *FUNDA* .

Kwanaki sun sude, shakaru su sude, abubuwa da dama sun faru mai dadi da marar dadi, dan Allah ya anshi rain Inna Fadila, dan Fadil da Khamis sunyi rashin mahaifiya, sai dai muce Allah ya basu hakuri...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 11, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now