18&19

351 24 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_17&18

Washe gari, bayan Rumaisa ta gama yi ma Mama gyaran daki da dan wanke-wanken su, sannan  tayi breakfast, ta shirya tace ma Mama ita ta wuce wurin Aiki, "Mama sai nadawo."cewa Mama tayi."a dawo lafiya." "Allah yasa."Rumaisa tace tana mai shirin fita, koda  tazo taho mu haɗa sukayi da Halimai, wani malalacin kallo Rumaisa take ma Halimai sai da hantar cikin Halimai ta kaɗa, dan har yanzun kumatunta zafi suke mata marin da tasha jiya a wajen Rumaisa, amman da yake Halimai ƙarfin hali ne da ita, sai da tayi ma Rumaisa kallon banza da tsaki sannan tace."antafi yawon ta zubar kenan?Allah dai ya tsare cutar ƙwanjamou."
Ita dai Rumaisa batace ma Halimai komai ba tabi ta gefenta tayi ta tafiyarta, amman maganar da Halimai tayi mata tayi mata zafi sosai, sai dai ba yanda zatayi ne, dole tayi hakuri ko dan farincikin Mama, koda ta shiga gidan su Fadila ta fara gaida Hajiya maryam.
"Aunty ina kwana."?kallonta Hajiya maryam tayi tana murmushi tace."Lafiya lau Rumaisa, ya Mamanki."?cewa tayi. "tana nan lafiya lau, Alhmdulh."nan ta tashi ta fara yin abun da ya kawo ta tana gama yin aikin gida, suka wuce kitchen ita da Fadila...
Fadila tace."Rumaisa, yau saboda muyi fira shiyasa na tashi da wuri."cikin jindadi Rumaisa tace. "dan Allah kawata? naga ai Kamar da magana a bakikin ki." Dariya Fadila tayi sosai sanann tace."au haka ma zaki ce kenan."? Itama Rumaisa dariya take sannan tace."Ehmna ai haka abun yake don tun jiya naga da magana a bikin ki."
Fadila tace tana murmushi."Aiko kin gano gaskiya, aiko maganganu a baki na, amman sai kin gyaro wajen Yaya Fadil sannan mu zauna muyi maganar, lokacin ba wani aiki da ke gabanki."murmushi Rumaisa tayi sannan tace."To shikenan Fadila, munyi saurin mu gama wannan girki tunda ba mai wuya bane zamuyi ba."kallonta Fadila tayi tana mamaki wai ba mai wuya bane zasuyi ce mata tayi."Aiko dai ba mai wuya bane, amman a wajenki yake ba ya da wuya amman niko tsakani da Allah *DAMBUN MASARA* da *ZOGALE* yana bani wuya,  ko dan daman ke na fara ganin kinyi shi, shiyasa har yanzun na kasa na koya."kallon mamaki Rumaisa tayi mata sannan tace."Haba Fadila, in banda abunki maiye abun wuya ga *DAMBU* ? Ai Kamar yanda kika iya yin *DAMBUN SHINKAFA* watarana hadda *GWAƊA* kuke sa mashi, to shima haka ake yin dambun masara shima."girgiza kai Fadila tayi tace."Niko Rumaisa, wallahi sai naga Kamar na masara yafi na shinkafa wahala, Rumaisa."Rumaisa cigaba da yanka albarsarta tayi sai da ta gama sannan tace."Ai haka zaki gani, tunda kinfi iya na shinkafar, amman nidai naga Kamar duk wahalar su daya, nima kafin na iya na shinkafa sai nace na masara yafi na shinkafa saukin yi, amman daga baya sai naga duk wahalarsu daya, ke ni baki daya ban daukesu wani aiki ba, tunda gashi har mungama yanzun, cikin dan lokaci kadan, albasa kawai zan kara sawa."cewa Rumaisa tayi."Eh gaskiya, haka ne nima yanzun na kara fahimta, kuma Kinsan Rumaisa sai kasa abu rai kake koyanshi, sannan kuma in ka sama ranka baka iya abu kaza to baka iya yinshi tunda kasashi a ranka,  shiyasa ni komai nike sama raina zani iya shi."dariya Rumaisa tayi."Eh hakane, amman kisan wasu matan basu dauki abun a haka ba, Allah yasa mudace, yanzun ni zan wuce na gyara ma Yaya Fadil part din shi sai ki juye dambun cikin cooler tunda mun gama."Murmushi Fadila tayi, dan ita har yanzun ta kasa yarda wai Yaya Fadil shi Rumaisa ke gyara ma apartment mutumin da ba kirki ya ishe shi ba ai tana kokari ma cewa Rumaisa tayi."To shikenan, sai kin dawo dan Allah kiyi sauri ki dawo ina son yin magana dake mai mahinmanci Rumaisa."cewa Rumaisa tayi."To shikenan, na wuce." nan fa Rumaisa ta wuce part din Fadil ta fara aiki da ya ke ta tadda baya nan.
Nan fa Rumaisa ta fara dafa ma Fadil tea, bayan ta gama hada tea sannan ta wuce ta fara gyaran dakin, ta na niyar fita dan ta gama suka ci karo da Fadil, wani irin yanayi ya tsinci kanshi dan ko sai da yace."wash."dabarbarcewa Rumaisa tayi nan ta fara matsa kwalla, dan gani take yau mai rabata da Fadil sai Allah, balle yanda taga yayi tsaye ya kasa ko motsi a tare suka fara magana, sai Rumaisa tayi shiru, shiko cewa yayi."sorry, bansan kina ciki  ba."cikin Mamaki ta ɗago ido tana kallonshi, aiko crab suka haɗa ido cikin ido, da sauri Rumaisa ta ɗukar da kanta kansa, dan bata iya jure kallonshi, shi ko kallonta kawai yake, dan natsuwarta tana kara mashi sonta a zuciya, cewa Rumaisa tayi."Aa ba komai yaya Fadil nice ya dace na baka hakuri, dan Allah kayi Hakuri."kallonta yake yana mamakin hali irin na Rumaisa shi yayi mata laifi amman ita ke bata hakuri ce mata yayi."naji nayi hakurin, yanzun ina zaki."? Cewa tayi."Da man yanzun na gama yin gyaran, ban zo da wuri ba, da yake yau mu muka yi sauwa nida Fadila, shiyasa, kuma tafiya zanyi."murmushi yayi sannan yayi mata alamun da ta koma ciki, koma tayi ta zauna shiga bedroom yayi ya ajiya suit dinshi sannan ya fito kallonta yayi sannan yace."Mai kuka dafa mana? Dan tunda na shigo da motana nike jin gidan baki daya sai kamshi yake buga wa."murmushi tayi tana wasa da yatsan hannunta tace."Ba wani abu mai dadi bane yaya Fadil, dambun masara ne da *ZOGALE* ."kallonta yayi sannan yace." *DAMBUN MASARA* kuma? Daman ana yin dambun masara, bayan dambun shinkafa da kus-kus."? Murmushi ne kwance a fuskar ta sannan tace."Eh mana, ai da dambun masara kawai aka sani, sai daga baya dambun shinkafa ya shigo, yanzun kuma naga harda dambun *KUS-KUS* duk ana yi."mamaki yake sosai, dan tunda yake bai taɓa ganin dambu masara ba, bai ma san anayi ba, ce mata yayi."Ikon Allah, amman nayi mamakin sosai fa."murmushi tayi tace."Ai ba abun mamaki bane, wannan zamanin ana yin kala kala, wani abincin ma yaya Fadil baka iya cin shi, amman mutanan da daga tuwo sai fura suka sani da dashishi, shiyasa suka fimu lafiya, domin yanzun ba kowa ke cin abincin gargajiya ba."kallonta yayi yanajin wani irin sonta na fisgar shi cewa yayi."Hakane, fatan kin da faman tea din ko."?cewa tayi." Eh na dafa, komai ma duk nayi, yanzun zan wuce gun Fadila muyi fira sannan na wuce gida."tashi yayi yana cewa."Ok shikenan kin gaida man da Mama inkin koma gida, nima yanzun wani file na manta ban fita da shi office ba kuma yau za muyi cases din shiyasa na dawo."itama tashi tayi tana cewa."Allah ya taimaka, Allah baku sa'a"cewa yayi. "Amin ya Allah."
Bayan Rumaisa ta gama gaisawa da Fadil ta wuce wajen Fadila domin sunyi magana da itace zasuyi.

*BUƊEƊIYAR WASIƘA*

*Buɗeɗiyar wasika zuwa ga masoyana masoyan litafin *A GIDAN HAYA* fatan kuna cikin koshin lafiya? Ya gida da kowa da kowa, Allah ya sa mu cika da imani Amin kuma muyi kyaukyawan karshe Amin ya Allah 🙏🏻*

*Dalilin  da yasa na rubuto maku wannan wasika shine, kuna ra tambayar  11&12,wasu na kirana waya wasun ko kuma suna yi man textmassege wasu kuma suna yi man magana ta whatsapp akan baku ga 11&12 ba, tom kuyi hakuri mistake nayi wajen rubuta number amman idan kuka fahimci labarin yana tafiya dai dai ba'a tsalake wani waje ba, abunda nike so na gaya maku shine babu page 11&12 sai dai 13&14 nayi mistake ne sai ayi mana hakuri duba da abubuwa da suka yi man yawa shiyasa aka samu wannan akasin, Ina godiya kamar yanda kuke cewa kuna tare dani Nima haka ina tare da duk wani masoyina a duk inda yake🥰*

Karku manta *Yar'mutan kankia taku ce ❣️* ina godiya byeeeeee🤝🏻


*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now