23&24

377 26 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
  _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
      

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_23&24

Da sauri Hajiya Maryam ta ida shigowa cikin gidan su Rumaisa, nan ta fara magana tana cewa."Subuhanalillah, lafiya mutanan gidan nan? nike jin hayaniya tun daga kofar gida."? Murmushi Mama tayi sannan tace mata."Hajiya lafiya lau, sannu da zuwa, anzo lafiya."?Itama Murmushin tayi sannan tace."Lafiya lau, nace lafiya duk naga mutanan gidan nan kowa ranshi bace."?
Cewa Maman A'i  tayi tana murmushi."Lafiya lau Hajiya, an dan samu sabani ne tsakanin lami da Maman Rumaisa."kallon Lami Hajiya Maryam tayi sannan tace."ikon Allah mai ye ya hada su."?
Maman A'i tace mata."Eh to Lami ta watsa ma Rumaisa fitsari, bayan ta san Rumaisa bata dade da fitowa daga wanka ba, gashi kuma bata lafiya."wata irin uwar harara Hajiya Maryam tayi ma Lami sannan tace tana kallonta."Subuhanalillah, ashe Lami yar yanzun baki da mutunci, yarinya bata lafiya amman kika watsa mata fitsari."?
Murguɗa baki Lami tayi, tana girgiza tana huce tace ma Umma."Eh din Hajiya, an watsa mata fitsari, ai shine nace ayi abunda za'ayi, zaki wani zo kina gaya ma mutane magana son ranki."
Murmushi Umma tayi, dan batayi mamakin maganar da Lami tayi mata ba, dan tasan su farin sani ba mutunci suka cika ba, ammman sai Maman A'i tace ma Lami."Yanzun Lami Hajiya Maryam kike gaya ma wannan maganar."?
Tsaki Lami tayi sannan tace."Angaya mata, inji bugu ko kuma na gan ni a offishin yan sanda, sai kace wata gold da, naje na gaya maganin abun."murmushi Hajiya Maryam tayi sannan tace ma Lami."Shikenan bakomai Lami, banyi mamaki ba dan kinyi man haka, abunda yafi haka ma kin iya yin shi."cewa Lami tayi."Oho dai, nagode Allah ina da zuciya, duk kudin mutun sai na gaya mashi ta cikina, koda da kudi yake yin mafashin kai, bai damaini ba sai na kalli idon mutun nagaya mashi abunda nayi niya eheeeey."Maman Rumaisa ce tace ma Umma."Hajiya dan Allah kiyi hakuri, ku shigo daki mana, munbarku a tsakar gida tsaye."kallonta Umma tayi, taji ta kara kwanta mata rai, dan babu shaka duk halinta Rumaisa ta dauko, cewa Umma tayi."Bakomai Maman Rumaisa, kuta hakuri da halin su dai,  ke Fadila zo mu shiga ciki, kinyi tsaye a nan."cewa Fadila tayi."To Umma, amman bari na gaya ma yaya Fadil ba abunda ke faruwa, nasan yanzun hankalinki tashe yake."cewa Umma tayi."To yi maza kije ki gaya mashi, sai ki shigo da cooler din kinji."? Cewa tayi na fita."To shikenan, insha Allah Umma."tana zuwa tace."yaya Fadil."kallonta yayi yace jiki duk a sanyaye."naam ina fatan lafiya dai, ba abunda ya faru da Ruma."!? Kallon shi Fadila tayi tana murmushi, dan ta lura yayan nata yayi nisa cikin son ƙawar tata, cewa tayi."eh lafiya lau."sake ce mata yayi."kin tambata."cewa tayi."eh yaya Fadil."ajiyar zuciya ya sauke sanann yace."to shikenan."Fadila tace."Yanzun bani cooler nan na shiga da ita cikin gida."cewa yayi."To anshi, ki gaida man da Rumaisa sosai kinji yar kanwata."!? Dariya tayi sosai, yanda taga Yaya Fadil yake lablaɓata duk dan saboda da Rumaisa cewa tayi."to shikenan."murtukewa yayi sannan yace mata."uban me kike ma dariya."!? Haɗiye dariyarta tayi sannan tace."yi hakuri Yayana, amman bakomai."da yake baisan maganar tayi nisa sai yace mata."ok."
Koda su Umma suka shiga room, Mama ce ta fara bata hakuri."Hajiya dan Allah kiyi hakuri da abunda ya faru."girgiza kai tayi sannan tace."Aah haba bakomai wallahi, ai nasan halin su Lami baki dayan su, su duka sai da suka yi mani aiki a gidana, ammman su duka sata suka yi man shiyasa na koresu."sosai Mama tayi mamaki sanann tace."Sata ikon Allah, to Allah yasa mudace duniya da lahira."cewa Umma tayi. "Amin ya Allah,Daman, Maman Rumaisa munga Rumaisa kwana biyu bata zo aiki ba, shiyasa muka zo muga ko lafiya."? Sosai Mama taji dadin yanda Umma ta damu da Rumaisa cewa tayi."Wallahi Hajiya zazzabi  ne da ciwon kai ke damunta, amman yanzun Alhmdulh jikin da sauki yau aka yi mata allura ma, insha Allah gobe zata shigo gidan aiki."cewa Umma tayi."Ayya Allah bata lafiya, daman naji kwana biyu shiyasa nace bari dai nazo naji kodai laifi mu kayi  bamu sani ba."dariya Mama tayi sannnan tace."Aah Hajiya ba laifin da kuka yi mana, muna godia Allah ya kara budi."cewa Mama tayi."amin ya Allah."cewa Umma tayi tana kallon Mama."To yanzun ina ita Rumaisa take ne."?....."Tana kewaye tana dauraye fitsarin da Lami ta watsa mata, amman nasan yanzun zata shigo."cewa Umma tayi."OK hakuri zaku tayi Maman Rumaisa, da man haka zaman GIDAN HAYA yake sai da hakuri, watarana kaci sa'ar da abokan zama na gari, watarana  kuma ka samu aka sin haka."cewa Mama tayi."Hakane Hajiya, Allah ya kara mana hakurin zama da mutane."..."Amin ya Allah Maman Rumaisa."shigowa Fadila tayi ta ajiye cooler, ta zauna, kallonta Mama tayi sannan tace."Fadila, yau dai Allah yayi naga Fadila, kullun sai an gayaman Fadila, yau dai gani ga Fadilar Rumaisa."murmushi Fadila tayi sannan tace."Mama ina wuni.".."lafiya lau Fadila."cewa Fadila tayi."ya mai jikin."?..."Mai jiki da sauki Alhmdulh, ya gida."...."lafiya lau mama, fatan mun samai ku lafiya."?... "Lafiya lau Alhmdulh."shigowa Rumaisa tayi, ta duƙa kusa da Umma tace."Aunty Sannunku da zuwa, kunzo Lafiya."?kallonta Umma tayi sannan tace."Lafiya Rumaisa, ya jikin naki."?cewa tayi."Da sauki Alhmdulh."...."to Masha Allah, Allah ya Kara lafiya Rumaisa."..."Amin ya Allah."
Fadila tace ma Rumaisa."kawata ya jikin."? Kallonta tayi tace."Da sauki kawata, nayi missing dinki sosai."murmushi Fadila tayi sannan tace."nima haka kawata,yaya Fadil yana waje muje mu gaisa tunda jikin naga da sauki sosai."cewa Rumaisa tayi."To shikenan, amman ki bari na shirya sai mu tafi, ki shigo daga ciki mana."cewa Fadila tayi."Aa ki barni nan gun su Umma, zaki yi saurin shirya wa in baki gani na."cewa tayi."ok na wuce na shirya."bayan Rumaisa ta shiga mai ta shafa da farar hoda da man baki ta zunbula hijab, sannnan ta fito tace ma Fadila."To tashi mu tafi na fito, Mama mun tafi gun Yaya Fadil kofar gida."cewa Mama tayi."to shikenan Rumaisa ki gaida shi kice muna godia."..."to Mama."tunda suka fito Fadil ta saki baki yana kallon Rumarshi dan tayi mashi kyau sosai, duk ta dan rame, amman hakan ma kara yi mata kyau yayi,  bai san da isowarsu ba sai dai yaji Fadila na cewa."Yaya Fadil ga Rumaisa nan na kowa maka ku gaisa."murmushi yayi wanda ya kara fiddo mashi da kyanshi yace ma Fadila."aiko kin kyauta kanwata, nasan ba dan ke ba,  da bata fitowa mu gaisa."dariya Fadila tayi sannan tace."Ni zan shiga ciki yaya Fadil."da sauri Rumaisa tace."Aah kawata ki tsaya gaisawa kawai za muyi sai mu shiga ciki tare."dariya ciki ciki Fadila tayi, dan tasan halin Fadil baisan ana dariya sosai, cewa tayi."Aah kawata niko kinga tafiya ta sai kin shigo."kallonta Rumaisa tayi tana girgiza kai,  sannan tace."amman kawata.... "Amman mai sai kin shigo."Fadila ta tari numfashinta tana shigewarta cikin gida. Kallonta Fadil yayi sannan yace."Shine dan ta tafi kika wani shiga damuwa."? Murmushi tayi tace."Yaya Fadil ai banga dalilin tafiyar ta ba."sake kallonta yayi sannan yace."Ke ce baki ga dalilin ta fiyarta ba, amman ita tasan ya dace ta shiga ciki kin shigo daga baya, ke idan mun gama gaisawa."taɓe fuska tayi sannan tace."amman yaya Fadil.. "Amman mai Ruma, kinsan bani son aita magana daya ko."? Cewa tayi."To shikenan, ina wuni."..."lafiya lau, ya jikin naki."?..."Da sauki Alhmdulh."... "Allah ya Kara baki lafiya."..."amin ya Allah."cewa yayi yana kallonta." Ruma nayi missing din ki sosai,  sannnan nayi missing din kallan wannan beautiful face din taki, kuma, tunda kika tafi ban sake shan tea ba."cewa tayi."Ayya yaya Fadil, ba sai kasa Fadila ta hada maka tea din ba."? Girgiza kai yayi sanann yace."Aah ni in ba naki ba bani shan kowane tea yanzun, dan haka yanzun dai yaushe zaki dawo."? Cewa tayi."Gobe insha Allah."cikin jindadi yace."to Allah ya kaimu lafiya Ruma, dan baki daya gidan  yayi missing dinki sosai."cewa tayi."nima nayi missing dinku sosai,to yaya Fadil ni zan shiga ciki."ba dan yaso ba ta tafi ba yace."to Ruma, sai goben ko."?..."Eh Allah ya kaimu lafiya Amin."nan ta wuto gida, Fadil ji yake kamar ya riketa karta tafi, amman bashi da zaɓi, tana shiga taga Fadila, kallon banza tayi mata, dariya Fadila tayi sannan tace.""Kawata sai yanzun kike dawowa, da kina wani yi man efizi hahahahaha."kallonta Rumaisa tayi sannan tace."Haba kawata maiyasa zaki tafi ki barni ni daya."? Cewa Fadila tayi tana dariya."Saboda na ba masoya wuri su gaisa sosai ko Rumaisar Yaya Fadil."? Cewa Rumaisa tayi."Wai masoya? Ku mutane kuna bani mamaki, mutun bai da ikon ya yi mutunci da mutun sai ku kama Cewa wai soyayya mtsssss.....


*Yar'mutan kankia ce ❣️*

Share
Comments
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now