9&10

437 35 5
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

            

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*wannan page din naku ne Bilkisu D da Shuraihat da Mummy Musty kuyi yanda kuke so dashi*

Page_9-10

Bayan Rumaisa ta gama yin komai a gida, sannan tace."Mama ni zan wuce."kallonta Mamarta tayi yana murmushi tace."To Rumaisa kiyaye kinji."? "Insha Allah Mama."Rumaisa tace nan  ta wuce warta gidan su Fadila, tana zuwa tayi aikin ta,
tayi komai da komai , sanann suka shiga kitchen itada Fadila da Umma sukayi masu Lunch, bayan sun gama aikin suka gyara ko'ina tsa suna cikin yin fira Fadil ya kira Umma waya ta turo mashi Rumaisa tayi mashi gyaran a part din shi, ce mashi Umma."kaga Fadil bani son shashanci kai har wani gyara za'ayi maka? Kai ba halinka bane kiran yan'aiki, amman ya naji haka yau."? Cewa yayi."Umma nasa kisan waye ni?to kawai ki turota please Umma, wallahi aiki zata yi man."numfasawa Umma tayi sannnan tace."shikenan gata nan zuwa."
Umma tace."Rumaisa tashi kije part din Fadil, yace kije zaki taya shi aiki."sosai gaban Rumaisa ya fara dukan uku uku, dan bata abunda zai haɗa ta da Fadil, dan ta lura ba mutunci ga gareshi, tana iya zuwa ya disgata yace ma mai ya kawota, nan take fuskarta tanuna bataso zuwa ba, abunda ba ta taɓa yima Hajiya Maryam ba, kuma ita Hajiya Maryam ta lura da haka, Rumaisa cewa tayi."To Aunty."girgiza kai Hajiya Maryam tayi tana murmushi, dan bata ga laifin Rumaisa ba dan taa nuna bata son zuwa apartment din Fadil, dan ko Fadila itama bata son zuwa wajen Yayan nata saboda murɗaɗan halinshi, cewa Hajiya Maryam tayi tana murmushi."Amman Rumaisa kina ga mawa ki taho kinji yar albarka."? murmushin karfin hali Rumaisa tayi sannan tace."insha Allah Aunty."tafiya tayi  ta wuce part din Fadil jiki duk a sanyaye.
"Assalama Alaikum." Fadil ne yace. "Amin wa'alaikumus sallam."tsaye Rumaisa tayi taƙi shigowa, cewa yayi."shigo mana kika yi man tsaye sai kace wani abu zanyi maki."?nan Rumaisa ta shigo, ta zauna kasa kan carpet din dakin, tunda ta shigo yake kallonta da gefen ido,ba tare da Rumaisa ta lura ba, sosai ya gama ƙare mata kallo sannan yace."Yauwa Rumaisa ko."? Sosai  Rumaisa taji haushin yanda Fadil yayi mata question, amman cewa tayi."Eh Rumaisa."cewa yayi yajan latsa laptop gami da dan kallonta kaɗan yace."Yauwa *RUMA* , da man gyara zaki yi man na duka apartment din nan, zan je na dawo na san kafin nadawo kin gama, inkin gama sai ki kai ma Umma keys din kinji."ɗaga mashi kai tayi sannan tace."eh naji."tashi yayi yana cewa."ok na tafi."
Nan Rumaisa, ta fara gyara parlourn kasa, parlour ne babba wanda yasha royal cunshen har guda uku, ga wani lafiyayen dining table nan wanda yasha ado da ruwan royals din, ga wata makekiyar plasma ta mamaye bango daya ga uban homethearters nan suma manya manya, sannnan ga uban Chinese carfect nan an baza a cikin parlon masha Allah...
Ash and black two set sunyi bala'in yi ma parlon sama kyau, shima ga wata yar medium din plasma taci kunsan rabin bangon, tana waigawa hannunta na dama ta hango wasu hotona guda hudu, daya nashine shi ya yana dariya yayi bala'in kyau, bata san lokacin da ta dauki hoton ba tana kallon nan ta kare man kallo..
Shidai Fadil farine kyaukyawan ajin farko, yana da hanci gashi da farfaden girji, ga idanu, idanun farare ne tas dasu, ga dan pink colour din lips dinshi dai-dai bakin shi, finally Fadil yana kama da *SIDAT* *KOKUREJA* , actor din *KING OF HEART* , dayan hoton kuma Shida Fadila ne su duka sunyi kyau suna dariya sun rungume juna, dayan kuma suda Umma ne sun sata tsakiya suna dariya sunyi bala'in kyau, na hudu kuma wani mutunine shima yana dariya, amman da alamun shi hoton wannan mutunin ba lokaci daya akayi shi ba, nan Rumaisa tace."ko waye ne wannan mutum shima yana kama da indiyawa."
Nan dai Rumaisa ta gama yin gyaran dakin, tana cikin yin gyaran dakin taga rappers din dollars baje saman bed dinshi, haka ta gyara bed din ta maida mai kudin shi inda ta gansu, ta fesa room freshener, ta dai gama komai sannan ta kaima Hajiya Maryam keys tayi masu sallama ta tahowarta gida..
Bayan Rumaisa ta dawo gida, ta iske Mamanta zaune ita ɗaya a ɗaki babu abokin fira, kallonta takr tana murmushi, sanann tace."Mama  Allah yayi nadawo."murmushi Mama tayi tana shafa gefen fuskar Rumaisa tace."to Alhmdulh  tunda an dawo lafiy , Yakika baro su Hajiya Maryam din."?cewa tayi tana mai kwacinya bisa cinyar Mamanta."Lafiya lau tana gaidaki ma Mama."cewa Mama tayi."ina ansawa, gaskiya Rumaisa Hajiya maryam tana da mutunci sosai, tana da tausayi da ina da abunda zansaka mata da na yi mata , amman ba hali sai dai na cigaba da yi mata fatan alkhari."cewa Rumaisa tayi."Haka ne ko Mama Aunty tana da mutunci ita da yaranta,kin san ko ina a gidan ta shiga nike, ga kuma ina ƙa ruwa da ita sosai, yanzun ba sanwar zamanin da bani iya ba, Mama kinsan yau har da bangaren baban danta na shiga ko ina a cikin part din, har da kudi masu yawa nagani.''zaro ido Mama tayi, tana mamakin irin yarda dasu Hajiya Maryam suka ba Rumaisa kuma tana jin dadin haka, cewa Mama tayi."Rumaisa dan Allah ki zamo mai rike Amana da alkhari dun idan kika samu kanki, karda ki kuskura ki zamo mutum mai son zuciya ta, har ta kaiki da kinci Amanar wanda ya yarda dake ya baki Amanar, ina neman wannan alfarmar a wajenki Rumaisa ko bayan rainane ki zamo mai rike Amana."cewa Rumaisa tayi."Insha Allah Mama, nayi maki alkhawarin zan zamo mai rike Amana da mutuncin kaina."cikin jindadi Mama tace."Allah yayi maki albarka kinji yarinya kirki."Rumaisa tana jindadin yanda Mama take sama ta albarka cewa tayi."Amin ya Allah Mamana ta kaina, uwar da tafi ta kowa, yauwa Mama  har yanzun Baba bai dawo ba ko lafiya."? Murmushi Mama tayi sannan tace."Lafiya lau insha Allah, kin san hidimar kasuwa, ba kamar kasuwa irin ta Babanki, kinsan masu *KEKE-NEPEN* har 11 suna kaiwa, ila yau 11 zai kai kafin ya dawo."cewa tayi."to Allah dai tsare man Babana, inason Baba sosai, duk da Baba bashi da wani garfi sosai, hakan baisa ya ragemu da komai ba."cewa Mama tayi."Hakane Rumaisa tunda Allah yasa na auri mahaifinki bantaba kukan babu ba, sai dai nayi kukan zaman *GIDAN* *HAYA* , domin *GIDAN HAYA* baida dadi zama, indan kuma ka samu wani gidan mai dadin zama, sai ka manta da *GIDAN HAYA* kake zauna, indan kuma Baka samu uban gida mai dadi ba sai Kai ta kuka kullun, Allah ya arzirta mu da *GIDAN KANMU* , da sauran mabukata kamar mu."cewa tayi."Amin Mama, insha Allah sai munyi *GIDAN* *KANMU* , hawayen da kike cewa kin zubda saboda *ZAMAN GIDAN HAYA,* insha Allah nan gaba sai dai kiba wasu *LABARIN* kin *ZAUNA GIDAN HAYA* , nayi wannan alkwarin mundun ina numfashi a doran kasa."murmushi Mama tayi sannan tace."Allah yasa Rumaisa."cewa tayi."Amin Mamana, ni zan kwanta sai da safe, kince ina ma Baba sannu da dawowa."cewa Mama tayi."to Rumaisa mu kwana lafiya."

***********************
Fadil ne zaune yake cema Umma."Umma gaskiya, wannan yarinyar Rumaisa ta nada hali mai kyau."kallon shi Umma tayi tana mamaki wai yau Fadil ne yake yabon halin mace a gabanta, yaron da ko maganar mace baison ayi sai yace zama a samashi ciwon kai,amman yau shi da kanshi yake yaba halin Rumaisa cewa tayi."Allah mai iko, kaiko Fadil ya'akayi ka ce haka."? Numfasawa yayi sannan yace. "Umma kudi na ajiye rappers har hudu kuma dollars, amman bata dauki man ko daya ba, kuma na ajiye ne saboda da na gwada halinta."murmushi Umma tayi sannan tace."haka ne Fadil ko nima nasha na ajiye kudi cikin daki, amman bata dauka kuma bata ceman ta gani, haka ma Fadila tasha ajiye abubuwa na mata, wanda yanmata zamanin nan ke bukata, amman bata dauka sai dai tace kawata kinbar abunki kaza, shiyasa nike sonta na dauke ta kamar ni na haifenta."ya gamsu da maganar Umma, dan yau kawai da gyra mashi daki yaji halinta yayi mashi cewa yayi."Wai Umma ina ne gidansu a unguwarnan."? Sai da ta kalllleshi, dan tayi mamakin jin haka daga gareshi cewa tayi."Kasan *DAKI GOMA*."? Girgiza kai yayi yace."Aah amman naji kamar ana fadin shi a anguwarnan."cewa Umma tayi. "eh nan unguwar yake , *GIDAN*  *HAYA* ne."kallon Umma yayi sannan yace." *GIDAN HAYA* Umma."? Cemashi tayi. "Eh *GIDAN HAYA,* nan suke zaune."basarwa Fadil yayi, dan yaga Umma naso albo jigirshi cewa yayi."ok daga yanzun nidai Umma ki ringa turota tana yiman gyaran daki pls."wani kallo tayi mashi sannna tace."baka isa ba Fadil, ko ka manta kai da kanka kace baka bukatar wasu yan'aiki, ba yanda banyi da kai ba kabari a ring gyara maka apartment dinka kace kai a dole baka so sai yanzun zaka ce na dunga turo Rumaisa, to kaji ni da kyau bani wani turota."marairaicewa yayi sannan yace."please Umma karki ce haka, itama na sati ne zatayi man sabda aikin da yayi man yawa banda lokacin da zan tsaya gyara ne shiyasa nace ki turota, bancin haka ai ni ba abunda yar'aiki zata yi man a apartment."kallonshi Umma tayi sannan tace."To shikenan, amman ka kiyaye kaji."?cewa yayi yana murmushi. "Eh insha Allah Ummana."






*Yar'mutan kankia ce ❣️*

Share
Comments
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now