57&58

303 13 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia  ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar  da masoyan ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_57&58

Yau da misalin karfe 2pm aka daura auren FADIL KHAMIS  MUHAMMAD da Amaryarsa RUMAISA FADIL MUHAMMAD a kan sadaki naira dubu Dari, sannan aka daura auren ADBULLAHI ABUBAKAR SULE da Amaryarsa FADILA KHAMIS MUHAMMAD akan sadaki naira dubu Dari, bayan an gama daura auren aka wuce reception aka ci aka sha..
Bayan nan sun Fadil suka yi pictures da abokanansu, sanann ya samu ya turama Rumaisa message..
Gidan cike yake da yan'uwa da abokan arziki, su Rumaisa suna part din Inna ta shirya su, dan har anzo daukar Fadila, tana basu wani jiko da ta anso masu,kallon Rumaisa Inna tayi sannan tace."wai Rumaisa zaki ansa ki sha ko sai muyi ta dake cikin gidan nan."turo baki tayi tana cewa. "Inna wallahi na gaji da shan wannan abubuwan naki, su ba wani dadin kirkiba." Cikin fada Inna tace."ai da yake bani zan ji dadin abun ba keda mijinki zaku ji dadin abun ku, lokacin ni banma san inda kaina yake ba,ku kuwa kina can kuna murzar juna, dan dagake har shi Fadil din ba hak'uri gareku, yanda kuke rawar kan nan ai dole sai da gyara." Rufe fuska Rumaisa tayi, tana cewa."ni dai Inna bani na sha yanzun zaki fara kallar wanann maganar taki ba dadin ji,ki tasa mutun yana jin kunya." ai Rumaisa tana cikin sha taji message ya shigo wayar ta nan ta fara karantawa..

_Yau din na kin zama tawa halak malak, inyi yanda nike so da yarinya ba mai ce man dan mi, congrats Rumaisa Fadil, yau kin zama matar Aure.._

Nan take Rumaisa ta fasa ihu, da man mai neman kuka, an gaya mashi mutuwa☺️,kallonta Inna tayi sannan tace. "ooo ni Fadila yau ina ganin zamani, shine kika kama kuka, daga anshi kisha? To ajiye ki tashi mujo gun iyayenku su yi maku fada, tunda ba ku za'a tsaya jira ba." Ida shanyewa Rumaisa tayi, ta cigaba da kukan ta itadai bata ce ma Inna komai ba. 
Nan aka kaisu part din Abba yayi masu fada, da fatan alkhari, sannan Baba, shima yayi masu fada, yi nayi bari na bari subi mazajensu, banda biyema shawarar kawaye...
Dan ga nan kuma suka wuce part din Umma, Umma tayi masu fatan alkhari, sai Mama itama ta fadi ta bakinta...
Nan aka fito da Fadila za'a tafi da ita, nan suka rungumi junansu suna kukan rabuwa, sai da Fadil ya shiga tsakaninsu yana ma Rumaisa magana a hankali yanda ba mai jinsu sai ita daya, yace."Haba princess, kukan ya isa haka mana, sai kace gidan makiyanku za'a kai ku, ai kyau kuyi murna ma, zaku zama cikakiyar mace."

(team Rumaisa kunji abunda Fadil yace😁)

Haka aka tafi da Fadila tana kuka, Umma na kuka, Rumaisa na kuka, Mama ce kawai tayi karfin halin basu hakuri..
Bayan sun isa unguwar da za'a kai Fadila a kano..
A parking space duk aka tsaya su Hajiya Zainab (yayar Umma ce) ne suka fito da amarya daga cikin motar Saif fuskarta na rufe suka ka mata aka nufi cikin gidan inda sauran mutanen suka take masu baya a dai dai bakin k'ofar da zata sadaka da cikin gidan aka ja aka tsaya inda amarya tayi addu'a sannan aka ida shiga Masha Allah tun daga nan aka fara santin gidan amarya saida aka shiga part d'in da yake mallakinta inda aka zuba mata kaya abun sai wanda ya gani ana shigowa parlour ne da yasha tank'ama tankaman kujeru royal brown and milk color sai faskekiyar plasma da aka yi ma gefenta decoration din well stickers, daga chan gefen haggu kuma wani dining area ne da ya sha ado masha Allah,  inda suka nufi wata k'ofa dake gefen dama ana bud'ewa wani parlourn ne maroon color aka zuba leaders cunshen masu bala'in kyau,  mai d'auke da room uku d'aya daga cikin room d'in aka shiga da ita nan ma komai na ciki royal ne Ash and black Color an tsara mata bedroom d'inta sosai abun sai wanda yagani haka jama'a suka dinga bin gidan suna tofa albarkacin bakinsu itadai amarya kuka kawai takeyi har aka zaunar da ita saman gado, sannan yan kawo Amarya suka fita gani gidan..

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now