13&14

336 15 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
         

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wannan page din nakine My Dijja Musa, kiyi yanda kike so dashi❣️*

Page_13-14

"Rumaisa."..."Naam Fadila, kin tashi lfy."? Cewa Fadila tayi."Lafiya lau, har kin gama yin aikin kenan."? Dariya Rumaisa tayi sannan tace."Eh nagama sauran part din Yaya Fadil, kinsan Aunty tace daga yau ni zan ringa yin mai gyaren part din, Shiyasa nike sauri naje nayi ko na gama."mamaki Fadila tayi wai yau Yaya Fadil da kanshi yace yar'aiki taje tayi mashi gyaran daki amman shuru tayi tana tunanin wani abu sannan tace."To shikenan bari ni kuma na gyara dakina, na rage maki aikin, in kin dawo kin yi man Kalaba, ina son nayi wankan tsarki."cewa Rumaisa tayi."to shikenan bari na tafi, nagode Fadilar yaya Fadil yau dai anhutar dani gyaran daki kenan." dariya Fadila tayi sannan tace."haba Rumaisar Mama, ai naga aikin yayi maki yawa ne, bari nayi nawa kuma wallahi Yaya fadil bai isa ya anshe mana ke ba ehe."Fadila ta karasa maganar tana dariya, itama Rumaisa dariya tayi ta tafi tabar Fadila dan ta lura Fadila tsokana take ji yau, tana zuwa part din Fadil tayi sallama."Sallama Alaikum."waigowa yayi yana cewa."Amin wa'alaikumus Sallam, Ruma har kin zo kenan."?itadai Rumaisa tana a dan tsorace cewa tayi."Eh Yaya, yanzun zan fara yin aikin, yau ina da Isilamiya Shiyasa."murmushi yayi shidai halinta yana burgeshi gata da hankali da tarbiya cewa yayu."kafin ki fara aikin je ki hada man tea ko machine sarkin aiki."? Murmushi tayi tana mamakin yanda yau ya chanza mata kamar bashi bane jiya yake mata magana adaƙile, amman cewa tayi."Laaa yaya Fadil, wai machine."? Bai kalli inda take ba, magana kawai yayi."eh mana Ruma daga shigowar ki ko hutawa babu kince zaki fara aiki, wai ke maiyasa baki son hutu."? Kallonshi tayi taga kamar bashi yayi magana ba, tana mamakin halin Fadil, dan tunda take a duniya bata taba ganin mutun mai murɗaɗan hali irin nashi ba cewa tayi."Ina san hutu mana sosai, amman ai kasan shi hutu kamawa yake Shiyasa, na tafi na hada maka tea din."
Nan Rumaisa ta wuce kitchen ta fara hada ma Fadil tea, tana mamakin yanda Fadil yake, cewa take."ashe daman yana da mutunci da sakin fuska kamar su Fadila?  gaskiya mutanan gidan suna da kirki sosai, ni da ina yi ma Yaya Fadil kallon marar mutunci, ashe ba haka abun yake ba, Allah na tuba, Shiyasa ba kyau yin zato, gashi naga deal ai yanzun." haka dai har ta gama hada mashi tea da yaji kayan hadi, dan *TURKEY* *TEA* ta hada mashi, sannan ta kai mashi...
"Ga tea din nan Yaya Fadil."kallonta yayi sannan yace."To Ruma sannu da aiki, nagode sosai kinji Ruma."cewa tayi."haba Yaya Fadil, sai kace wani abu, da zaka ce ka gode, asha lafiya."murmushi kawai yayi yace."to Allah yasa." nan Rumaisa ta shiga cikin bedroom ta fara gyara shi dan yau harda new bedsheet ta sauya ma bedroom din, ta shiga bathroom shima ta gyara shi ta chanza new carpet don daman bathroom din ba wani baci yayi ba don Fadil ba daga baya ba wajen tsafa, sai da tagama gyara ko ina sannan ta dawo sitting room lokacin ya gama shan tea din yana ta game din shi....
"Yaya Fadil, zan gyra nan amman inka gama."cewa yayi."to Ruma bari na tashi, amman inkin gama ki yi man magana kafin ki wuce."? Cewa tayi."to shikenan, insha Allah." nan fa shima sitting room ta gyrashi tsaf da dashi ta chanza ma duk royals din nan waje tayi mopping sanann ta kunna boner nan take dakin ya gume da kamshi mai sanyaya zuciya, ta wuce kitchen ta gyra sannan ta fito, tace."Yaya Fadil na gama."cewa yayi."ok Ruma, gani nan zuwa, dan jirani kadan kinji."samun waje tayi ta zauna tace."to yaya Fadil."sai da ya ida gama abunda yake sannan ya fito yace."yauwa sannu da aiki Ruma."cewa tayi."yauwa yaya Fadil."zama shima yayi sannan yace."anshi wannan kin saya jan baki da za'ayi kwaliya."kallon kudin hannun shi tayi sannan tace."to ngd, amman don Allah yaya Fadil kabar kudin ka nagode."sosai Fadil yayi mamakin yanda taƙi ansar kudin, nan take ta ƙara shiga zuciyar shi cewa yayi."Ruma keki tambayeni na baki kudi."? Girgiza mashi kai tayi sannan tace. "Aah bani bace." daure fuska yayi tamou sannan yace."to bari kiji, in har kina san karda muyi fada daga yau in har na baki wani abu karki ce baki ansa, kin dai jini ko."? Cikin tsoro tace."Eh naji kayi hakuri."dan sakin fuskarshi yayi yace."naji karki sake Ruma, dan ni bani bada abu ace ba'a ansa, haka nike bani bada abu amai doman, tashi ki ka tafi, kaji mince zaki tafi isilamiya karda ki makara."tashi tayi tana cewa."To shikenan, nagode yaya Fadil."har ta kusa fita taji yace."Ruma."waigowa tayi tace."Naam."rasa abunda da zaice mata yayi ji yayi yana cewa."daga yau ki ringa dafa man tea di nan da yawa wanda zai kaini har safe kinji."? Cewa tay."Eh Insha Allah, sai anjima." shi ko Fadil bai son ta tafi doman bai son abunda zai yanke fira da ita dan yana bala in jin dadin muryarta ita dai Ruma da ban take cikin mutanan, komai ta iya haka Allah yayi ta dai.
Tunda ta fito daga part din Fadil take gode ma Allah da suka rabu lafiya dashi, zuwa tayi wajen Fadila tace."Fadila taso na yi maki ko na tafi."kallonta Fadila tayi sannan tace."wai Rumainsar Mama saurin mai kike har haka."? Ce mata tayi."Wallahi Fadilar Yaya Fadil, sauri nike yau Isilamiya zan tafi bani son na makara shiyasa."tashi Fadila tayi tace."ok to yi man sai ki tafi, ammn naso yau muyi fira sosai, amman bakomai, in kinzo munyi gobe."cewa Rumaisa tayi."to shikenan." nan Rumaisa tayi ma Fadila kalaba, sannan ta wuce gida, ta dauki abincin ta koda taje gida samun taje gida kwantawa tayi kusa da Mama tana cewa."wai Allah na, Mama yau duk nagaji sosai."kallonta Mama tayi sannan tace."to Rumaisa, sannun kinji, Allah yayi maki albarka."cewa tayi."amin ya Allah Mama, ga wannan kudin Fadil ne ya bani su."kallon kudin Mama take sannan tace."Rumaisa wannan kudin basu yi yawa ba."? Numfasawa Rumaisa tayi sannna tace."Mama sai da nace bani amsa amman yace sai na amsa na ni da yanda zani yi."jinjina ma Fadik Mama tayi sannan tace."mun gode, Allah ya kara masu bude."cewa Rumaisa tayi."Amin ya Allah, yanzun bari dai na tashi na wuce isilamiya karda na makara kin san halin malam Ahmed sai yace zai wulakantaka ba abu bane mai wuya agareshi."cewa Mama tayi."To tashi maza ki tafi, inkin dawo kinci abincin, dan nasan baki komai ba har yanzun."cewa tayi tana mikewa tsaye."to Mama na tafi."cewa Mama tayi."adawo lafiya."
Bayan Rumaisa taje isilamiya sun gama yin karatu, hanyarta ta dawowa ta gamu da Fadil a hanya shima,ji tayi yace."Ruma."tsayawa tayi tace."Naam Yaya Fadil, kai ne nan  da kanka."? Kallonta yayi ya kauda kai sanann yace.eh nine, daman nan wurin isilamiyarku take kenan."?ansa mashi tayi da."Eh nan ne, gama ta can."waigawa yayi yaga isilamiyar sanna yace."wai da itace kenan? Allah sarki, yanzun kuma gida zaki sannan ki huta ko."? Murmushi tayi sannan tace."Eh wallahi gida zani na samu na dan huta, kafin mu daura abincin dare nida Mama."cewa yayi."to shigo na kaiki gida mana."cewa tayi."Yaya Fadil na hutar dakai ai gidan ba wani nisa keda akwai ba."wani kallo yayi mata sannaan yace."wallahi Ruma daga na sake saki abu kika yi man gardama sai na ɓata maki rai, ki bari sai na saki abunda Allah ya haranta mana da muyi shi sannan kice bakiyi, oya come in Madam."hakuri ta bashi sannan ta shiga motar  sannan tace"to shikenan nagode."ce mata yayi."Sannu Ruma, kina kokari sosai."kallonshi tayi sannan tace."Yauwa Yaya Fadil, amman ba wani aiki bane mai wahala ba."cewa yayi ba tare da ya kalleta ba."daman kema nan ne unguwarku kenan."? Ce mashi tayi."eh mna unguwarmu daya da ku ai."murmusawa yayi sanna yace."to nuna man gidanku sai na ajiye ki nima na wuce."ce mashi tayi."kana shan wannan kwanar shikenan kazo gidan mu."sai da ya sha kwanar da tace mashi sannan yace."to shikenan, ai mun iso kenan."? Cewa tayi. "aiko dai, to nagode sosai."tadda motar yayi yana cewa."bakomai ki gaida man da Mama."cewa tayi."to zataji."tafiya ta fara yi taji ana cewa."Na boni, ni Halimai, mutanan gidan ku fito kuji ikon Allah, dan Allah duk ki fito, zargin da muke yau dai ya taibabata gaskiya."Hindatu ce ta fito tana cewa."lafiya Halima? zaki tadamu muna cikin hutu."? Cewa Halimai tayi."Ina fa lafiya Hindatu, ai wani baƙin gani nayi."Lami ce ta tashi har tana faduwa tana cewa."baƙin gani kuma Halimai."? Cewa Halimai tayi."Eh Lami baƙin gani, ki godema Allah da bake kika yi wannan bakin ganin ba."tambayarya sukayi a tare suna cewa."wannan wani kalar bakin ganine har haka."? Cewa Halimai tayi."Yanzun naga wani mutum ya sauke Rumaisa cikin wata bakar mota, kafin ta fito sai da tayi kusan minti 20, sannan ta fito tana gyra hijab dinta."wata irin dariya Hindatu tayi sannan tace." daman ke sai yau kika fara gani Halimai."? Kallonta Halimai tayi sannan tace."Eh Hindatu, kardai kice man kema kin gani."? Cewa Hindatu tayi."yo wani dare ne jemage bai gani ba? sau nawa ina kamata, ke ni nan har gani nayi wani gardin Allah yana yi mata kiss, yo da man ai ku ake yi ma alaye da sunan gidan aiki da isilamiya ba dai ni ba."kallonsu Lami tayi sannan tace."Ni fa duk kun sani a duhu, kuna nufin Rumaisa da gaske tana bin *MAZA*." ? cewa Halimai tayi."haba Lami, sai kace wanda bata waye ba, ai da kinga ido Rumaisa kinga idon Yan duniyarnan, wanda suka zama Yan hannu a cikin harka."cewa Lami tayia tana mamaki."Tabbas biri yayi kama da mutun, banyi mamaki ba, yanda suke cin abinci mai kyau, su sa kaya masu kyau, ai dole wanann harkar sai da bin mazan banza, dan ba kudin keke napen kawai ne zasu rike mutum ukku ba."
Cikin fushi da konar zuciya Rumaisa ce tace masu."Ya ishe ku haka...

*😂😂😂😂 ya kuke ganin next page zai kaya tsakanin Rumaisa da su Lami🤔,  sai naga ruwan comment dinku sannan zan baku next page😉*

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

Share
Comments
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now