45&46

285 23 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

            
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_45&46

*Iye iye nanaye 🤗, inji mawaƙa, haka maganar take, idan Allah ya nufa zaka cigaba, zaka zama wani tam ba wanda ya isa ya hana, duk ko bakin cikin mutun da hassadarshi🤣, dan haka nidai Jameey yar'mutan kankia sai dai a ganni a kyale nan gani nan bari, idan ko aka shigoman gonata zan shafa ma👀kwali nayi ma mutun abunda baya tunani, dan haka sai a kiyaye🤓*

_Masoyana kuna raina, kamar yanda nima nike ranku, inayinku over and over, soyayyar da kuke nunaman tana sani farinciki sosai💋_

Kallon Fadila Rumaisa tayi yana girgiza kai sannan tace."Fadila taya zanyi shiru, bayan kinsan ina cikin matsala, masoyina baya lafiya,  amman fa Fadila Yaya Fadil Aman jini fa yake, ni ya zanyi da raina, nasan ban kyauta ma kaina ba."

Tashi Fadila tayi tana lailashin Rumaisa sannan tace."to yanda zaki yi da rainki, shine kiyi addu'a, kuma insha Allah ba wani abu ki ringa yimai hasashen alkhari, mana Rumaisar Yaya Fadil."zaunawa Rumaisa tayi tana cewa."To Fadila nagode sosai."murmushin karfin hali Fadila tayi sannan tace ma Rumaisa."yanzun tashi mu tafi mu daho mashi abincin kafin a fito dashi."girgiza kai Rumaisa tayi tana cewa."Aah Fadila kedai ki tafi ki daho mashi, nidai ina nan har sai naga an fito dashi."shiru Fadila tayi tana dan tunani na wani lokaci sannan tace."To Rumaisa, tunda baki zuwa, bari na kira Dear  yazo ya dauke ni, sai na hado mashi."cewa tayi."ki hado mashi harda tea please."harararta tayi sannan tace."shi da yace ban iya hada tea ba sai dai ke, amman zanyi dai dan baya lafiya,  bari na kira shi, mu tafi."

Dauko wayarta tayi, tana kiran Abdullah."Hello Dear, kana jina."daga can bangaren Abdullah yace."yes Sweety am hearing you, what wrong."? Murmushi tayi sannan tace."Da man yaya Fadil yana hospital."tashi Abdullah yayi daga zaune sannan yace."what? Kina nufin Fadil baya lafiya."? Cewa Fadila tayi."Eh Dear  yanzun haka ina hospital, kazo ka dauke ni naje gida na hado mashi abinci."tashi Abdullah yayi yana cewa."ok wait for me am coming now." Cewa tayi."ok safe trip."waigowa Fadila, taga Rumaisa tana kuka,matsowa tayi kusa da ita tana cewa."Yanzun tsakani da Allah Rumaisar Mama, har yanzun baki daina kukan ba? Shi yaya Fadil ba mutuwa yayi ba."

"Hmm  Fadila kenan baki san yanda nike ji ba shiyasa kike cewa haka."kallon Fadila tayi sannan tace. "Uhmmm nidai na tafi kinga dear har ya iso." Cewa tayi."to Fadila ki gaida da man da Abdullah.".."to zai ji."

Haɗe hannuwanta tayi waje ɗaya, ta langwaɓar da kanta gefe tace."Dear sorry na barka tsaye." murmushi yayi, dan yanda tayi sosai tayi mashi kyau, cewa yayi."bakomai Sweety,shigo mu tafi ko."? Shigiwa tayi tana cewa."ok, ya gida."?..."lafiya lau."..."ya Adda ta take."?..."tana lafiya lau,wai Sweety da yaushe aka kawo Fadil hospital? Daga gidan mu yake,ya anshi motana zai je wajen Rumaisa." numfasawa Fadila tayi sannan tace."to wallahi ,muma anyi mana waya ance muzo yana asibiti,abun da mamaki da muka tadda Rumaisa tana kuka."murmushin taƙaici Abdullah yayi sannan yace."To may be ,itace tayi causing din matsalar ko."? Shiru Fadila tayi na wani lokaci sannan tace."nima haka naki tunani,to ka bani some minute, yanzun zan fito." fitowa tayi zata shiga gida, dan har sun iso, cewa yayi yana murmushi."to a fito lafiya."

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now