39&40

296 21 2
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

            

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_39&40

Shiko Fadil, ya kira wayar Rumaisa ya jita switch off, ya sa bata da chaji shiyasa bai damu ba sosai sai dai kawai yayi ta text messages..

" _Zumata, yakike, duk yau ban ganki ba Allah ya tsare man ke duk inda kike, anjima zamu yi waya inki bude wayar, gaskiya Ruma ina sonki ki tamaki dan almajiri Ruma ki ceci rayuwata,, ILOVE YOU TOOO RUMA, I miss ur beautiful face, and I miss ur hot killer smile and voice 💖_

Nan ya tura mata text messages din sannan yayi arwala ya tafi mosque, yana dawowa ya wuce part din Umma suyi fira ko sun rage mashi abunda yake ji cikin zuciyarshi, kallonshi Umma tayi sannan tace."Fadil."dago kanshi yayi sannan yace."Naam Umma."ce mashi tayi. "lafiya naga duk ka rame."? Murmushi yayi sannna ya girgiza mata kai yace."Bakomai Umma, maikika gani."?harararshi Umma tayi sannan tace."Ai kaji matsalar dan Nigeria kana yi mashi question shima na yi maka question, maimakon ka bani ansa, amman kace mai na gani, to ban sani ba."dariya yayi sannan yace."Yi hakuri Umma, wallahi ba abunda ke damuna kawai dai nazo muyi fira kafin isha'i tayi na wuce mosque."shiru tayi na wani dan lokaci, sannan tace."to shikenan ai sai ka zauna, ya aikin, yau ba naji kace zaku yi wata shari'a ba."?gyara zama yayi sannna yace."Eh Umma yau aka fara gudanar da cases din, amman da yake cases din fyade ne, dole sai an samu shedu, shiyasa aka kara sati, sai a dawo a ciki gaba da case din lokacin mun samo shedu."salati Umma tayi sannan tace."Kai, Allah yasa mu dace."..."Amin Umma."cewa Umma tayi."wallahi Fadil yanzun duniyar nan ana yawan samun issues din repping, abun nan yana bani mamaki, koni asibitina a rana sai mu samu patient kusan goma kuma duk fyade ne to wai ni Maryam daga ina matsalar take gun iyaye ko su yaran ko kuma sun samarin."? Dukar da kanshi yayi sannan yace."To Umma su duka suna da Laifi."cewa tayi."gaskiya haka ne Fadil, kaga wasu iyayen basu damu da ina yarinyarsu zata tafi ba, bata damu da kula da lamarin yarinya ba, kin sake diya a tsikiyar unguwa bata gidan wannan bata gun wannan, ai dole wataranan a samu matsala,ko kuma ki daura ma yarinyarki talla tun safe bata dawowa sai ta sayar da tallar duka, in ko bata sayar ba kin kama yi mata fada kenan, kin manta da Allah yake bada kasuwa, amman kin aika yarinya matashiyar budurwa talla tsakar gari,su kuma mazan sama rai jarabar banza da wofi wanda bata bulleka da komai ba sai dai aikin da na sani, dan wallahi ba samari kawai ke ma mata fyade ba harda maginanta masu iyali, kana da matarka amman ka buge kallon matan mutane daga nan sai shiden ya shiga cikin zuciyarka ya kwadanta maka gonar da ba taka ba, amman ka shiga kayi barna."cewa yayi."hakane gaskiya Umma."cigaba da cewa Hajiya Maryam tayi."Suma yan-matan harda laifinsu, saboda yanzun sunan kawai buduwarmu bahausace, kums tana sa kaya a jikinta, sai kaga yansa kayan damanmu wanda ko tafiya sai tayi da gaske take yin ta, ga uban gyale tasa na  iskanci ,  dan gyala wai ita a dole a ce mata ta waye, abunda bata sani ba shine wannann ba waye wa ba ce JAHILCI NE, tunda ta wannan dalilin bata san maza nawa ta taso ma da shi'awarsu su, wani yaji zai mutu kaga ai dole ya hayaima yarinyar mutane ko."?
cewa yayi."Hakane gaskiya Umma, Allah ya rabamu daga sharin zina."cewa Umma tayi."Amin Fadil da sauran al'umman muslamai baki daya."....."Umma ni zan wuce sallah lokaci yayi."......"to Fadil nima bari na tashi naje nayi tawa sai da safe."......"to Umma Allah ya kaimu lafiya.".... "Amin."
Bayan Fadil ya dawo daga masallaci ya dauko tea ya sha, sannan ya dauki waya ya danna ma Rumaisa waya, Amman abun mamaki Kalma daga ake ce mai IS CARY SWITCH OFF, ya kira ya kusa kai sau 10,amman ansa daya ake bashi ba yanda ya iya yace bari ya barshi zuwa anjima sai ya sake kiranta...
Ita kuma Rumaisa bayan ta dawo daga Isilamiya, suka yi abincin dare ita da Mama, bayan sun gama yin komai sanann suka tashi suka shiga daki suka zauna suna fira da Mama...
"Wai Mama lafiya, naji kwana biyu gidan nan anbar yin fada."? Kallonta Mama tayi sannan tace."Hmmm Rumaisa kenan ai dole kice haka tunda ba zaman gidan kike ba, dan ko yau da safe sai da aka dambace tsakanin wannan bakuwar karimai ita da Halimai, ta kama Halimai tana daukar mata kudi cikin jikka."zaro idanu Rumaisa tayi sannan tace."Ikon Allah, wai ita Halimai sai yaushe zata daina wannan bakin halin  nata, ina anfani bata gudun mijinta ya sani."? Cewa Mama tayi."Kin dai gani Rumaisa, kuma jiya aka yi tsakanin mijin Halimai da mijin Lami."cewa Rumaisa tayi."mai su kuma ya hada su Mama."? Cewa Mama tayi."Mijin Lami ya kama Mijin Halimai yana leƙa Lami a kewaye." zaro ido Rumaisa tayi sannan tace."na bani Mama a kewaye? Daman ni tuni nike gaya maki  mijin Halimai shine ke leka mutane a kewayen gidan nan, amman Halimai tace bashi bane wai barawo ya shigo ranar da dare shiyasa na ganshi, ni kuma da ido na naga yana leka Hindatu a bayi."cewa Mama tayi."To dai aiko ya sha bugun banza, dan wallahi ba karamin duka ya sha ba, sai da ita Haliman ta shiga tsakaninsu tana kuka, tana a rufa mata asiri karda akashe mata miji."....."Kai, banji dadi ba, Allah ya sawaka, ya shirya su baki daya."....."Amin ya Allah.''....."Yauwa Rumaisa, na gaya ma Babanki, yaron gidan da kike aiki yace yana sonki."shiru Rumaisa tayi tana kallon Mama, sannan tace."to Mama mai Baban yace."?murmushi Mama tayi sannna tace."Cewa yayi in naga ba matsala ai shikenan Allah ya tabbatar da alkhari."Murmushi Rumaisa tayi sannan tace."Allah sarki Baba, Amin ya Allah,amman Mama har yanzun ba gaya mashi na aminta da shi ba."kallonta Mama tayi sannan tace."yo saboda mai Rumaisa."?..."Eh Mama, ai Umma ta bani shawara." nan dai Rumaisa ta gaya ma Mama yanda suka yi da Umma, kuma tayi Amanna da shawarar Umma.
"Mama ni zan kwanta sai da safe."...."To Allah ya kaimu lafiya."..."Amin Mama."
Fadil ba kiran da bai yi ma wayar Rumaisa ba amman dai har lokacin wayarta a kashe yatada hankalin shi, ya tashi sosai, da yayi niyar ya kira Fadila ya tambayeta, amman sai yayi tunanin ba ta sani ba, inda ta sani ta tayi mashi maganar shiyasa sai ya koma ya kwanta, kuma baya son ita Fadilar ta raina shi..
Haka ya kwanta yai ta juyi bisa gado, dan tunanin Rumaisa ya hanashi bacci ko kadan dan gashi yanzun karfe 11 na dare, sai da ya dauko wayarshi ya kunna pics din da yayi mata tana bacci ya kama kallo sai kace tsohun maye, sannan Allah yaso shi baccin ya kwasheshi ragunme da hoto yana kallo..
Shine bai tashi daga bacci ba sai da lokacin sallahr asuba yayi, sannan ya tashi yayi raka'atul fijir, ya wuce masallaci..
Bayan ya dawo daga masallaci bai koma bacci ba sai da ya gama yin azakar sannan ya dan kwanta, karfe 9 ya tashi yayi wanka, yayi shirin office, yana sauri ya shiga part din Umma, dan yasan Rumaisa tazo aiki tunda tun 8 take zuwa aiki...
"Umma ina kwana"?....."Lafiya lau Fadil." "antashi lafiya"? "Lafiya lau, Umma yau ke daya kike hada breakfast din."? Murmushi tayi sannan tace."Wallahi ko Fadil, har yanzun Rumaisa bata shigo aiki ba, ina jin maybe zuwa anjima zata shigo, daukarman wannan cooler mu wuce kiyi breakfast."take yaji baiji dadi ba, daurewa yayi yace."To Umma, Allah yasa dai lafiya? Dan ni ko jiya ban ganta ba."bata kalleshi ba, cewa tayi. "lafiya lau, take, muci abinci."Fadila ce ta fito sannan tace."Umma ina kwana? "Lafiya lau Fadila."zaunawa tayi tana cewa."Yaya Fadil ina kwana."cewa yayi."qlau, kin tashi lafiya."?... "Lafiya lau." nan suka ci gaba da yin breakfast, amman banda Fadil, dan Fadil cokali kawai ke kara cikin plate din shi, dan ba abunda yake sai tunani, "ayya Ruma tana lafiya? Trust out jiya wayarta kulle take, kuma yanzun gashi har yanzun bata shigo aiki ba "Fadil,kai Fadil, magana nike tun dazun kayi banza ka kyaleni."Umma tace tana bugoshi, saurin juyowa yayi yana cewa."Naam Umma, yi hakuri banjiki ba."Harararshi tayi sannan tace."wai mai ke damunka, kowa na cin abinci banda kai."? Cewa yayi."Bakomai Umma, yanzun zan cigaba da ci."nan dai Fadil ya samu yayi cokali shidda, sanann ya tashi ya ce ma Umma sauri yake ya makara..
Amman Fadil gidan su Rumaisa ya nufa..



*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now