47&48

280 20 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_47&48

Sai da Rumaisa ta samu Fadil yaci abinci, ya koshi, sannan hankalinta ya kwanta, Murmushi Fadil yayi sannan yace."Ruma." kasa ɗago kanta tayi balle ta kalleshi, wasa take yatsun hannunta, dan kunyar abunda tayi mashi take, bude dan karamin bakinta tayi, tace."Naam." Fadil ya fahimci Rumaisa kunyarshi take ji, kuma shi baya jindadin wannan kunyar tashi da take ji, langwaɓar da kanshi gefe yayi cikin wani irin sallon soyayya yayi maganar kasa kasa kamar mai jin bacci yace."ki dago ki kyaleni mana Ruma, ina son ki kyale ni ido cikin ido, na gaya maki kallar SON da nike maki Ruma." sosai maganar ta shiga cikin jikinshi Rumaisa dan ko tsikar jikinta sai ta fara tashi, cikin zuciyarta tace."wash yau zan mutun da salon wannan mutum." abunda bata sani Fadil ji ne dashi yaji abunda tace, Murmushi yayi sannan yace."maikika ce Ruma."!? Sauri ta dago kanta tana kallonshi, sunburo mashi baki tayi sannan tace."ni bance komai ba fa." dariya yayi sanann yace."naji Madam bakice komai ba, nace ki kyale ni sosai na gaya maki irin son da zuciyar Fadil yake maki." cikin shagwaɓa tace."Yya Fadil..."Shsss Ruma." ya daura yatsa akan lips din shi, yana mai sauko wa bisa bed din ya duka giwa biyu a gabanta, yana mata wani irin kallon soyayya dan ji yake kamar ya haɗiyeta dan son da yake mata, cewa yayi."Ruma kin san bani son musu, dan haka dago ki kyaleni gani gaban zan nemi wata alfarma." da sauri Rumaisa tta sauko itama ta tsuguna tana cewa."Yya Fadil, dan Allah ka tashi tsaye, ban san na ganka a tsugune a gaba, inba haka na nima ba zan tashi ba.'' Murmushi Fadil yayi, sannan yace."Ruma wallahi ba zan tashi har sai na yi abunda nayi niya, kuma kema yanzun nike son ki tashi ki zauna." bata da zabi, tasan tunda yace baya tashi to ba tashin zaiyi ba, tashi tayi ta zauna, cewa yayi." yauwa kina jina."!? Kallonshi tayi kamar yanda ya bukata sannan tace."Eh ina ji." ƙara matsowa yayi yana cewa."yauwa RUMAISA."kasa cewa komai Rumaisa tayi, dan yanda taji yace Rumaisa, kuma tana tsoran abunda zaice mata raurau tayi da idanu sannan tace."Naam." Murmushi yayi, dan ya fahimci Rumarsa ta tsorata, dan zaiyi magana da ita, cewa yayi."Rumaisa! Rumaisa!! Rumaisa, kinji na kira sunanki sau ukku ko."?...."Eh."..."Rumaisa ina sonki, ina kaunarki, ina tausayin ki, dan Allah ki daure ki ban masauki a cikin zuciyarki, Wallahi zan kula dake ba zan yarda na saki kuka, zan rayu dake, zan mutun dake, ina son ki zamo uwa ga ya'yana." numfasawa yayi sannan ya cigaba da cewa."Ki man alkwarin duk runtsi duk wuya ba zaki zuya man baya ba, ki man alkwarin bazaki hukuntani da laifin da ban nayi shi ba, ki man alkwarin zaki rike ni Amana zaki bani kula ba zaki yarda kiga bacin raina ba." hawaye ta fara sharewsharewa, tasan batayi ma kanta adalci ba, da ta huka masoyin gaskiya har haka, tasan bayan iyayenta bamai son kamar Fadil, cewa tayi." Yaya nayi maka duk wannan alkwarin da kace man, yaya Fadil zuciyar Rumaisa ta dade da dakon sonka, kaga ko ba za ta yarda ta zuya maka baya ba, inasonka yaya Fadil, kaine gishirin rayuwata, inbaka nima bani, dan haka bani fatan naga ranar da ranka zai baci, ko da ya baci, ni Rumaisa sai na sashi farinciki, na gusar da wanda bakin ciki, ba zan iya sa masoyiyina kuka ba, kasani kaine rayuwata dan soyayyarka a jinin Rumaisa take." Wani farin hankichif, ya fiddo ya miƙa ma Rumaisa yayi mata alamun da ta goge hawayen fuskar ta, sannan yace."Nagode Ruma, Allah yayi maki albarka Matata." Murmushi tayi mai haɗa da kuka tace."Amin ya Allah Yayana." Hararar wasa yayi mata yaji tace Yayanta, tashi yayi yana cewa."Ruma to tunda ana sona sai abar ce man *YAYA* *FADIL* , ke kice Fadila tace, nidai gaskiya ke ki chanza man." ya karasa maganar cikin shagwaba,sai kace karamin yaro dan goye, Murmushi kawai Rumaisa tayi, cigaba da cewa yayi." Dan haka daga yau na dawo *PRINCES* , ni kuma zan ringa ce maki *PRINCESS* , haka yayi maki? In bai yi maki ba sai mu chanza wani sunan ko masoyiya." tana dago ta kallashi ya ɗage mata ido, yana mata wani kallon mai wuyar fassara, da sauri ta dukar da kanta kasa tana dariya sannan tace." Haka yayi man my princes, sunan yayi man dadi, dan haka daga yau insha Allah ka zama Princes." cewa yayi."wwoow my princess thank you very much, ilov uh,yauwa wai mai ya samu wayarki Princess."!? Cewa tayi a hankali."Bakomai lafiyarta lau." Murmushi yayi sannan yace."dan kawai nasha wuya shiyasa kika kulle wayar kenan."? Cewa tayi."Uhmmm, amman ba haka bane." cewa yayi."tom naji princess gaya man ya abun yake."? Yar dariya tayi marar sauti, sannan tace."Kawai princes bakomai jin dadi." cewa yayi."to Allah ya kara maki jin dadin princess."
Umma ce ta shigo tana cewa.to kai patient sai ku tashi mu tafi gida ko."? Saukowa yayi daga bisa gadon yana cewa."To Umma, da man ni tuni naji sauki, ko princess."? Nan dai Rumaisa ta dukar da kanta kasa tana wasa da hannunta, dan ita yanzun bala'in kunyar Umma take ji, lura da hakan Umma tayi tace."Kaji dashi dan nema, ku taso mu wuce, kaga magrib tayi, mu aje Rumaisa gida, kar hankalin Mamanta ya tashi kaga har yanzun bata dawo gida ba." cewa yayi."alright Umma."
Nan suka shiga motar Umma, aka bar ta Abdullah wani mai gadi zai maida masu ita gida, Umma ce tace." Fadil kana jina."!?.."Eh Umma." cigaba da ce mashi Umma tayi."sai ka rage yawan tunani, indai kana son lafiyarka da kuma kwanciyar hankalin mu." cewa yayi."insha Allah Umma, ni yanzun ai bani da matsala balle har nayi wani tunani, tunda princess ta yarda da soyayyata." dakuwa tayi mashi tana cewa."sannu shugaban masu kunya, a gabana kake princess ko."? Dariya yayi yana cewa."To Umma laifi ne in mutun ya nuna ma matarshi So, matsala hausawa kenan wallahi komai kunya, sai kunyar ta cucesu, nidai gaskiya bani da kunya a kan princess." kallonshi Umma tayi, tana mamakin Fadil, soyayyar Rumaisa tasa ya chanza hali sosai, Fadil din da ko magana bata damaishi ba, amman yanzun magana yake, cewa tayi." To naji, mai princess, a yi hakuri karda naji duka." rufe baki yayi yana cewa."rufaman asiri Umma." waigowa baya Umma tayi sannan tace."to Rumaisa mun iso gida, sai gobe ko."? Duk kunya ta isheta abunda Fadil yace a cikin mota, cewa tayi."Eh Umma nagode sosai." cewa Umma tayi."Dan Allah Rumaisa ki gaida man da Mamanki, kice ina gaida ta gobe Insha Allah zani shigo muyi magana, yanzun dan dare yayi shiyasa." cewa tayi."To zan gaya mata, sai da safe, Allah ya kara lafiya." Fadil yace."ban ji ba gaskiya princess, abunda zaki ce man kenan."? Gwalo tayi mashi sannan ta ruga da gudu tana yi ma Fadil gwalonta." a hankali yace."Hmm yarinya zan kama ki, zaki shigo hannu ne." Murmushi yayi kawai.
Bayan su Fadil sun koma gida, wanka yayi yaci abinci, sannan ya samu suka yi waya da Abdullah, bayan sun gama waya, yaje mosque, suna fitowa , ya biya yayi ma su Umma sai da safe nan ya wuce part din shi, ya buga ma Rumaisa waya...
"Hello princess, ya gajiya."? A hankali tace."Alhmdulh princes, ya jikin ka princes."? Rumgume pillow yayi sannan yace kamar maiyin raɗa. "to da sauki sai da ina ta tunanin sauranniyar zuciya ta, baki ji yanda nayi missing dinki ba." daga can bangaren ta, itama kara kashe murya tayi sanan tace."Nima nayi missing dinka princes, nidai ka rage yawan wannann tunanin pls princes, bani son nayi asara." Murmushi yayi sannan yace."to shikenan, zan rage, ni fa na kosa naji ansa mana baiko, inda so samu ne anyi bikinmu cikin wata nan."
Dage kirji tayi sannaan tace."haba princes wani rawar jika har haka."? Cewa yayi."Naji din idan akan sonki to akirani *MAJUNUN* , princess na fi son ayi mana aure na nun maki kallar son da nike maki physical, sannan zaki yarda da Son da nike maki." cewa tayi."Tom princes Allah ya kaimu lokacin.".."Amin, ki gaya ma Mama zani zo na gaida Baba, dan inason manya shigo cikin maganar mu, dan gaskiya cikin shekarar nan nike son na ganki a dakina a matsayin mata." cewa tayi."to zan gaya mata." cewa yayi."yauwa, fatan zaki shigo gobe ko."?.."Eh zan shigo, prices bacci, yanzun har 12 tayi. Cewa yayi."ok bari na barki, amman ba dan na gaji ba, byee iluv you."...."byee luv uh too."
bayan su princess sun gama waya, Fadil sai da ya tura mata text messages kamar haka

_I cannot imagine a day without you my love. I feel insane with you. Nothing ever is the same. You touch my heart with your very presence and when we kiss it takes me to my soul. I am so madly in love with you princess.._

Bayan Rumaisa ta karanta message din Fadil itama ta maida man da nata

_As I lay_
_As I lay on the bed this night,_
_I was thinking about you so strong,_
_I want to come and hug you tight,_
_I know to me you belong,_
_My love for you my_ _feelings are that strong,_
_I so love you my love,_
_Have a lovely night,_
_And yes do sleep tight_ _my princes.._

Haka suka kama tura ma junansu sakonnin soyayya sannan suka yi bacci cikin farin ciki da annashuwa.

Washe gari...

*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now