53&54

245 20 0
                                    

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_53&54

A haka rayuwa, ta cigaba da tafiya, soyayya mai karfi ta kunnu tsakanin FADIL DA RUMAISA, da kuma FADILA DA ABDULLAH..
Soyayya wanann masoya suke babu kama hannun yaro, zumincin tsakanin Umma da Mama, suma abun sai gaba yake, wannan dalilin yasa Umma ta ba su Rumaisa wani part a cikin gidan.
Kallon Mama Rumaisa tayi sannan tace."Mama wai yaushe zamu koma gidansu Yaya Fadil da zamane? Kinga Umma batajin dadi ace ta bamu wani bangare mu zauna a gidansu amman har yanzun bamu koma ba."
Kallon Rumaisa Mama tayi sannan tace."ba haka bane Rumaisa, nidai sai naga kamar bai dace ba, ace mun tare a gidan surukanki muna zama." Kamo hannun Mama Rumaisa tayi sannan tace." Mama su Umma ba irin wannan mutanan bane, su zasuyi ma mutun abu kuma ba gori har abada, amman yanda kika gani Mama." Suna cikin maganar Baban Rumaisa yadawo, yaji komai suka tautauna akai, zaunawa yayi,sanna yace." Hadiza kuyi sallama da mutanan gidan nan, yau da dare zamu koma gidansu Hajiya Maryam da zama, tunda ba tambayarsu muka yi ba." Murmushin murna Rumaisa tayi da Baba ya amince, itama Mama taji dadi cewa tayi." Shikenan insha Allah zaniyi duk yanda kace." Tashi yayi ya dauko abunda ya maido shi gida dauka sannan yace masu." Ni zan koma." A tare suka ce." Allah ya taimaka ya kawo kasuwa." "Amin." Yace sannan ya fita, fitowa Mama tayi tsakar gida, taddasu Halimai tayi zaune sun hada kai waje daya sai magana suke a hankali ga dukan alamun gulma suke, kallon banza sukayi mata a tare sanann suka kauda kai, bata damu da kallon da sukayi mata ba murmushi tayi sanann tace." Sannunku da hutawa ina kwanan mu."!?  Tsaki Halimai tayi sannan tace." Ke hutu ya gani, kuma da bamu kwana ba da kin ganmu."? Dariya Mama tayi sannan tace." Hakane kuma Halimai, daman zuwa nayi muyi sallama yau zamu tashi daga gidan nan zamu koma gidan Hajiya Maryam da zama." Take fuskokinsu ta chanza, bakin cikine kwance kan fuskokinsu, tsaki Hindatu tayi sannan tace." Andai ji kunya wallahi, kinsan Allah Lami da nayi roko da bara kwara na mutun cikin gidan haya, amman da yake wasu ba su da zuciya anje anyi fadanci an samu anba miji aikin gadi,har ana shirin kome." itadai Lami cewa tayi." aiko dai Hindatu, ni banga amfanin zuwa wani yi mana sallama ba, mu daman anzo anyi mana bakebake cikin gida, ai mu dadi mukaji za'a tafi a barmana gida." itako Halimai bakin ciki yasa ta kasa magana, sai ma kallon Mama da tayi tace." munji dan Allah wuce ki bamu waje Allah ya raka taki gona." itadai Mama murmushi tayi sanann ta koma suka cigaba da hada kayansu, daman Rumaisa ta gaya ma Fadil dawowar tasu yau, aiko suma sukaje suka gyara masu part din da zasu zauna, Baba na dawowa suka kwanshe kayansu nasawa kawai kujerun dakin da gado harma wasu kayan sawar da kwanonin cin abinci, Mama su Halimai taba tace su raba,haka suka tafi suka barsu da kayan bakin ciki, kuma bayan tafiyarsu, harda fada akayi tsakanin Hindatu da Halimai akan kayan da Maman Rumaisa ta bar masu, dan ita Lami cewa tayi ta barmasu su raba, dan taga sun fita bukata tunda ita mijinta ba abunda baya sayar mata.

Su Mama sun dawo gidan su Fadil, da zama suna zaman su hankili kwance, amman duk da haka Baban Rumaisa ya na zuwa neman kudin shi, dan yace shi dai a barshi ya nema na kanshi, ba dan Hajiya Maryam taso ba ta barshi. 
Yau ta kama ranar da Alhaji Khamis zai dawo cikin iyalenshi, dan haka kowa ya tashi da shirin tarbarshi....

__________________________________

     *WUDIL-KANO*

"Malama." Wanda aka kira da Malama naga ta dago tsuhuwar fuskarta, dan da alamu ta tsufa sosai, dan dai bafulatace kuma tana da jiki mai kyau shys ba'a cika gane tsohanta ba sosai, cewa tayi."Naam Malan, ya na ganka haka? Kamar wani marar lafiya."! ? Numfasawa tsohon yayi, dan da alama da kaganshi kasan mijinta ne, cewa yayi."Lafiya lau, sai dai kwana biyu hankalina ya tafi wajen Fadil, ban san yanzun ko yana wani hali ba." Shiru Malama Fadila tayi, dan mijin nata ya soso mata inda yake mata kaikayi, amman bata zabi daurewa tayi sannan tace."Hakane Malan, shiyasa nike nuna maka, rashin dacewar hukuncin da ka dauka, ai in Khamis ya gudu ya barmu, bai ka mata ace muma mun tafi  mun bar dan karamin yaro, saboda san zuciya Irin tamu, mun tafi mubar yaro wanda bai wuce shekara goma ba a duniya, yanzun ko Yana wani hali? Allah kadai ya sani." Cewa Muhammad yayi."Tabbas Malama, mun tabka baban kuskure, wanda in bamu gyara shi ba, mu ka bar duniya, gaskiya sai mun hadu da hushi ubangiji,  ya bamu amana mun watsar mun tafi mun barta." Girgiza kai tayi sannan  tace."Yanzun mai abun yi Malan."!? Tashi yayi yana cewa."Abun yi shine yanzun ki tashi, ki hada kayan ki, dan yau insha Allah a Kano zamu kwana." Itama tashi tayi tana cewa."to shikenan Malan."

A GIDAN HAYAWhere stories live. Discover now