RANAR HAUSA

16.5K 524 54
                                    

*RANAR HAUSA TA DUNIYA*
(26/8/2019, 25/12/1440)

*HAUWA A USMAN JIDDARH*

~MARUBUCIYAR:-~
'''WANI AL'AMARI'''
'''K'ADDARA TAH'''
'''GADAR ZARE'''
'''RASHIN SANI...!'''
'''RABO AJALI'''
'''WATA SHARI'AR...!'''
'''SAKI RESHE...!'''

ASSALAMU ALAIKUM

Ina mik'a sak'on gaisuwa ta ga dukkan Hausawan duniya a duk inda suke.

*SALON MAGANA*

1. "Sannu sannu, "ina ciwo ne?
"Da kana ciwo da baka hau gado ba?
"In hau gado ni sarki ne?
" Da kai sarki ne, da ba'a kada maka tambari ba?
" A kad'a min tambari, ni Amale ne?
"Da kai Amale, da ba'a aza maka kaya ba?
" A aza mini kaya, ni jaki ne?
"Da kai jaki ne, da ba'ayi maka duka ba?
" A dake ni, ni b'arawo ne?
"Da kai b'arawo ne, da ba'a yanka ka ba?
"A yanka ni, ni nama ne?
"Da kai nama ne, da ba'a cika ba?
"A cini ni, ni kasuwa ne?
" Da kai kasuwa ne, da baka tashi ba?
"In tashi, ni shirwa ne?
" Da kai shirwa ne, da baka zari d'an-tsako ba?
"In zari d'an-tsako, ni muzuru ne?
" Da kai muzuru ne, da baka shiga daji ba?
"In shiga daji, ni kwad'o ne?
"Da kai kwad'o ne da baka shiga ruwa ba?
" In shiga ruwa, ni kifi ne?
"Da kai kufi ne, da bakayi santsin baya ba?
" Inyi santsin baya, ni karkashi ne?
"Da kai karkashi ne, da ba'a tausa ka ba?
" A tausa ni, ni baka ne?
"Da kai baka ne, da baka yi harbi ba?
" Inyi harbi, ni kunama ne?
"Da kai kunama ne, da baka bi bango ba?
" In bi bango, ni kyenkyaso ne?
"Da kai kyenkyaso ne, da kai kyenkyaso ne da baka shiga gora ba?
" In shiga gora, ni nono ne?
"Da kai nono ne, da ba'a shaka ba?
" A shani, ni bante ne?
"Da kai bante ne, da ba'a d'aura ka ba?
" A d'aura ni, ni aure ne?
"Da kai aure ne, da ba'a tara maka shaidu ba?
" A tara min shaidu, ni mai shaidar zur ne?
"Da kai mai shaidar zur ne, da baka fita gari ba?
" In fita gari, ni d'an hari ne?
"Da kai d'an hari ne da baka taimaki Musulmi ba?
" In taimake Musulmi, ni Annabin Allah ne?
Sallallahu Alaihi wa sallam.

2. "Zangar zangar!
"Alharinin goro.
"Wuce gaba in biki.
" Ni 'yar sarkin hanya ce?
"Hanya tsawo gare ta,
" Duk tsawonta tayi ya zare ne?
"Zare fari gare shi.
" Duk tsayinshi ya kai rago ne?
"Rago shan ruwa gare shi.
" Kome shan ruwan shi yayi ya Alkama?
"Alkama ja gare ta.
" Komai janta tayi ya barkono?
"Barkono kisa gare shi.
" Komai kisansa yayi ya kunkuniya?
"Kunkuniya kisa ta kama.
" Komai kisanta tayi ya sarki Allah?

*IDAN KA CIKA CIKEKKEN BAHAUSHE MAIMAITA*

1. "Ke matar k'ona-k'ota, bani aron k'otar k'ona-k'ota in k'ona.
" Ni matar k'ona-k'ota ban k'ona k'otar k'ona-k'ota ba, bare kai bak'on k'ona-k'ota, in baka k'otar k'ona-k'ota ka k'ona?

2. Kadan ka san bata san daka san ba, kasan ta san da kasan.

3. Sarki yace ya aiko a kawo masa fatar farin kadan Kano bakwai.
"Ni ban samu fatar farin kadan Kano bakwai ba, yo ina zan kai masa fatar farin kadan Kano bakwai.

4. "Assalamu Alaikum matar duba-rudu.
" Maraba da bak'on duba-rudu.
" Bani aron madubin duba-rudu in duba.
"Ni matar duba-rudu ban duba mudubin duba-rudu ba, bare kai bak'on duba-rudu kace in baka mudubin duba-rudu ka duba?

5. "Assalamu Alaikum matar komod'o-komod'o, nazo ki bani komod'on komod'o-komod'o in kwakkomad'a.
" Kai, Ni matar komod'o-komod'o ban komod'a komod'an komod'o-komod'o ba, sai kai bak'on komod'o-komod'o zakace in baka komod'an komod'o-komod'o ka kwakkomad'a?

6. Haka silif na sallib'e siliya a wuyan salamatu, ashe ban sani ba an yiwa Malam Salihu satar santali a santala.

7. Na yi asubanci na iske durumin duru, na ce kai durumin duru mai kayiwa mutanen duru suke saranka da duruduru?

8. Da kwad'o da k'ato suka tafi yawan k'ota. K'ato yayi k'oto, kwad'o yayi k'oto, k'ato ne zai kwacewa kwad'o, ko kuwa kwad'o ne zai kwacewa k'ato k'ota?

9. Nayi gudu dakyar na k'etare kogi na k'etare matar kogi, na kama tsugwagun ragon Baba na layya naja k'irit.

10. Haka tsom na tsoma naman tsofon zomona a gora, daga bani ba wanene zai tsoma naman tsofon zomona a gora?

11. Rub a gaton k'ayar can na kama kadabkara bakwai.

12. Shamuwa ma shan ruwa wuya mik'e.

*KACICI-KACICI*

*(IDAN KA ISA CIKEKKEN BAHAUSHE KA BADA AMSARSU DAI-DAI)*

1 Ja ya fad'i, ja ya d'auka.
2 Icen gidanmu inuwa a gidan wani.
3 Mutane suna jin tsoranka mata suna fad'awa.
4 Zubi na azufa datsi na jar fata.
5 Gangara kogi mu je zariya.
6 Tafiya sannu-sannu kwana nesa.
7 Hanyata noman tudu.
8 Abu siriri tubkar Allah.
9 Kullum ana baka babu godiya.
10 Na wanke kwaryata, naje da ita gabas naje da ita yamma, na dawo bata bushe ba.
11 Tasa guda d'aya ta isa duniya amfani.
12 Rufe-Rufe tak'i rufuwa.
13 Binne-Binne tak'i bunnuwa.
14 k'aramin gaya dama kogi.
15 D'an k'aramin abu gama duniya.
16 Na fashe d'aya naga biyu.
17 Tsohuwar gidanmu ta takwarkwashe tana rok'on Allah.
18 Mace da Miji sun haifi 'ya'ya ba lissafi/adadi.
19 Abu na ruri a dawa ba hanji.
20 Na sayi abinda bashi da riba.
21 Jeji na kaya-kaya kutunka na shiru.
22 Daga nesa na hangi layan amata.
23 Giwa da bante.
24 Riga guda d'aya aljihu d'ari.
25 Uku-uku taga gari.
26 Ka fashe kwai kaga kwal.
27 Kwaryata ta fad'a daga sama bata fashe ba.
28 Rawanin Baba ya gagari nad'uwa.
29 Rigata biyu wacce nake sawa itace sabuwa, wacce take aje itace tsohuwa.
30 Akushin Baba ya faskari sud'ewa.
31 Babban Bamaguje ya kara gaban mata.
32 Abu guda ya mai k'ofa uku ya raba mutum tsaka.
33 Baba na ciki gemu na waje.
34 Shanu d'ari mad'aurinsu d'aya.
35 D'an baka a bayan shuri.
36 Tsumagiyar kan hanya fyad'e yaro ki fyad'e babba.
37 Matan gidanmu masu fararen baki.
38 Tafi da k'ura dungusa.
39 Shirin ba ci ba.
40 D'akin samari ba k'ofa.
41 Daga nesa naji muryar wa na.
42 Taka ni in fita.
43 Allah me nayi maka duk jikina kufato.
44 K'ulun k'ulu fita.

*MAKARANTA DA MARUBUTA AKAFTA, A WASA KWAKWALWA*

GMAIL:- jiddarh012@gmail.com

*HAUWA A USMAN JIDDARH*

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now