17

5.1K 337 92
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*

*ZAN CIGABA DA YIN POSTING RABO AJALI IN SHA ALLAH, AMMA MATUK'AR AKA CIGABA DA SIYAR MIN DA NOVELS CIKI ABU HUD'U TABBAS ZANYI D'AYA, KO NA MAYAR DA NOVELS D'INA NA KUD'I, KO NA YI APPLICATION NA MAYAR DA NOVELS D'INA CIKI, DUK MAISO YAJE PLAY STORE YAYI DOWNLOADING KO NA MAYAR KAN YOUTUBE DUK MAISO YAJE CAN YA SAURARA, KO NA DAINA RUBUTUN KWATA-KWATA GABA D'AYA DAN BAI YIWA KURA DA SHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, NI INA NAN INA SHAN WAHALA WANI NA CAN NA AMFANI DA WAHALA TA, BASIRA TA BA*

_Ina masoya masu goyan bayanmu a da yaushe, masu san shek'e masge kwarkwatar idanunsu wajen karatun littattafan Hausa? to ku matsu kusa, dan nesa tazo kusa, ga shahararriya, hazik'a, fasihiyar marubuciyar nan da kuka sani, kuka dad'e kuna jiran sabon littafinta_ *AISHA ALIYU GARKUWA,*
_ta sake dawo muku da wani sabon salon littafinta mai k'unshe da abubuwan mamaki, al'ajabi, kala-kala, wanda zai nishad'antar daku, ya d'ebe muku kewa ya sanya masu hawan jini, sauka, masu ciwon zuciya darawa,_ *HUKUNCIN ALLAH....!* _shine sunan littafin wanda zai zo muku nan bada jimawa ba, *HUKUNCIN ALLAH....! duk masu buk'atar wannan shahararran labarin ya tura naira 200 kacal, ta wannan account number  0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA ko ta WhatsApp number da za a turo katin mtn 09097853276*_

1⃣7⃣

" I said who is she....!? Najwah ta fad'a cikin masifa da tsananin k'arfi tana kuwwa da d'aga murya,
wacce duk ilahirin gidan sai da ya amsa, k'utttt...! yawu ya wucewa Neehal babu shiri,
yayi shiru had'i da zuba mata ido yama rasa me zai ce mata,
" dama wannan dalilin ne ya hanaka dawowa gida tsayin shekara d'aya....!?

" Dalilinta ne ya hanaka dawowa ka ganni tsayin watanni goma sha biyu....!?

" Akan wata ne dama ka barmu cikin k'unci da kewar juna tsayin shawaki d'ari uku da sittin da biyar (365)....!?

"Opss...! na manta ka barni ma zance, tunda na tabbatar kai kana can tare da ita cikin farin ciki da walwala,
tunda har ka iya barin kowa akanta, ka k'aurace mana akanta tsayin lokaci,
ni ina nan ina ta faman hauka, bana ci bana sha, na hanawa kai na farin ciki da jin dad'i,
ashe kai kana can tare da wata ta maye maka gurbi na,  dama jiki na ya dad'e yana bani akwai wani abu,
tunani na ya jima da tabbatar min kana tare da wata,
ni dama nasan matuk'ar babu wani dalili babu yadda za'ayi ka k'aurace mana,
kabar kowa duk akanta why....!?

" Meyasa kayi min haka Neehal....!?

"Meyasa ka ci amana ta.....!?

"Why Neehal....!?

Ta k'arashe maganar cikin matsanancin kuka, tana dukan k'irjinshi,
cikin k'arfin hali da dakewa Neehal ya rik'e hannunta had'i da cewa " enough...! ya isa haka dan Allah,
am tired Najwah, na gaji da irin abubuwan nan, na rasa yaushe zaki yarda dani,
na rasa yaushe zaki aminta dani, ki bani amicewarki da yardarki,
d'ari bisa d'ari, na rasa dalilin da yasa kike min kallan mara kamun kai.....!,
ban san me kike so nayi miki dan ki yarda dani ba, ban san me zan miki dan ki zama kina da yak'ini akaina ba,
ta yadda zai zamana baki da kokonta ko shakku kwata-kwata akai na,
meyasa kika k'i yarda dani.....!?

"Meyasa har yanzu baki aminta da ni kin yarda da ni ba.....!?

" Meyasa kika k'i bani yardarki da amincewarki Najwah....!?

"Meyasa har yanzu kike da shakku had'i da kokonto akaina....!?

" Meyasa kika bar zuciyarki take sak'a miki munayen abubuwa akan mijinki na sunna....!?

"Meyasa hakan ke faruwa bayan ina da tabbacin tunda muke dake, tun daga ranar da Allah ya fara had'a mu, har izuwa yau baki tab'a kamani da laifin sharin gaskiya ko na ha'intarki ba.....!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now