37

7.4K 359 51
                                    

://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

3️⃣7️⃣

Shiru d'akin yayi babu wanda ya  furta koda kalma d'aya, sai sautin kukan Najwah dake tashi,
cikin sanyin jiki Najwah ta zame k'asa ta zube gaban Neelah tana cigaba da kukan batare data iya cewa komai ba,
cikin ranta tana tunanin yau wacce tafi tsana fiye da kowa da komai a duniya tayi mata abinda 'yan uwanta, uwa d'aya uba d'aya suka kasa yi mata,
wacce ko k'aunar ta bud'e idonta ta ganta bata yi amma gashi ta rufa mata asirin da duk duniya babu ne rufa mata,
tayi mata abinda uwa ko ubanta bazasu iya yi mata ba, tayi mata kyautar da Allah ne kad'ai yake yinta, wato kyautar d'a, cikin muryar kuka tace " I'm sorry, I'm so so sorry Neelah,
nagode sosai ina rok'on Allah ya saka miki da mafificin alkhairi,  ta fad'a muryarta na sark'ewa,
fuskar Neelah d'auke da murmushi ta sanya hannu ta d'ago Najwah ta zaunar da ita a kusa da ita,
tace " tsakanin mu babu godiya tunda abu d'aya ne yayi mu, dukkan mu dodo d'aya mukewa tsafi,
yaran Neehal yaranki ne,  dan haka har abada sun zama naki, nayi miki alk'awarin su kansu yaran bazasu san bake ce kika haifesu ba,
shiyasa nake san ki shayar dasu, ta fad'a tana gogewa Najwah hawaye,  cikin nutsuwa Neelah ta mayar da kallanta ga Neehal dake tsaye hard'e da hannuwa a k'irji,
ta marairace fuska tace " I'm sorry na yanke hukunci batare dana tuntub'eka kona shawarceka naji ta bakinka ba,
a hankali ya taka ya isa gabansu ya sanya hannu ya shafa fuskar Neelah yana murmushi,
yace " ai abu me kyau kikayi, nagode sosai Neelah, kinyi abinda ba kowacce mace ce zata iya yinshi ba,
ya fad'a cike da tausayawa, " tom! Maman twins munyi yara, kuma naga kamar suna kama dake ma,
ya fad'a yana zama kusa da Najwah, Najwah ta sanya dariya had'i da d'an kai mishi duka tace " tunda suna kama dakai ai dole suyi kama dani, ya goce yana dariya,
" kuyi hak'uri iyayenmu na yanke hukunci batare dana nemi izini daga gare ku ba, Neelah ta fad'a tana kallan iyayensu,
cikin sanyin jiki suka sauke ajiyar zuciya, suka shiga kallan juna deep down suna jiinjinawa Neelah,
" mun gode miki sosai Neelah Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, Ubangiji ya biyaki, Allah ya saka miki da gidan aljanna ya shirya muku zuri'a,
Abban Najwah ya fad'a hawaye na gangarowa daga idonshi, gaba d'ayansu suka amsa da Amin ya Allah, Umman Najwah tace " bamu da bakin da zamuyi miki godiya,
baku da kalmar da zamuyi miki amfani da ita wajen nuna miki tsantsar farin cikin mu, iyakaci dai muyi muku addu'ar Allah ya had'a kanku,
ya raya muku zuri'arku ya had'e kan yaranku, ya baku zaman lafiya da fahimtar juna, tayi maganar muryarta na sark'ewa,
Mamy, Umairah  dasu Suhaima da kowaccensu ke d'auke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe suka matsa kusa da Neelah cikin farin ciki,
suna yi mata godiya, Mamy ta shafa kanta, tana murmushi tace " Allah yayi miki albarka, Ubangiji ya albarkaci rayuwarku data yaranku gaba d'aya, suka amsa da amin ya Allah.

Cikin nutsuwa Daddy yayi gyaran murya ya soma da cewa " Alhamdulillah Alhamdulillah ala kullu halin,
ina godiya ga Allah daya had'e mana kan zuri'armu suka fahinci junansu, Allah ya k'ara had'e kansu,
shi kishi ya zama dole, dan Allah ya halicci shi a jikin kowacce irin halitta, har wad'anda ba bil Adama ba,
har dabbobi suna da kishi, haka hadisi yazo mana Annabi SAW yace " duk wanda baya kishin iyalinshi bazai shiga aljanna ba,
sai dai kishin wasu yana zama hauka, dabbanci da rashin hankali wanda ko dabba bata yin haka,
akwai matakan kishi da mutum zai kiyayesu dan gudun fad'awa kishin halaka wanda zai iyakai mutum aikata aikin nadama,
na farko a babin adalci mu sani cewa " _gairatul mar'a amrun jiblat alaihi faliza latu akaz'alaihi_ kishi wani abu ne da Allah ya halicci dukkan halitta akai,  dan haka baza'a iya raba mutum da kishi ba,
shiyasa Malaman musulunci irinsu Ibn Rajab da Imamun Taba'i Allah ya rahama alaihi,
suka ce ba'ayiwa mata azaba akanshi _illa  anta 'ta'adda_  sai dai idan kishin nata ya wuce gona da iri,
wato tayi zalunci akanshi, ta zagi wata, kota ci mutuncin wata, ko k'arya, ko cutar da wani, ko duka kota raba wani da ranshi,
to anan ta wuce gona ana iya yi mata ukuba akansa, baya da haka yazo a cikin Hadisi Irwa'ul Garib jiz'i na 7 shafi na 80,
Annabi SAW ya gaya mana kishi kala biyu ne akwai kishin da Allah yake so akwai kishin da Allah baya so,
yace "  _Innaminal khaira  mayi hibbullahi anza wa jannah wa minha  mayif khudhullahu anza wa jannah_
daga cikin kishi akwai wanda Allah yake so akwai wanda Allah baya so, kishin da Allah yake so shine akwai damar aikata mummunan zato na aikata haramun a cikinsa,
misali mace ita kad'ai ce awajen mijinta, yayi tafiya daya dawo sai taga condoms a cikin kayanshi,,
bayan bai tab'a yi mata amfani da condom ba, kuma ajikin rigarshi taga alamar jan baki da hoda na mace,
to wannan tana iyayin kishi da zargi akansa saboda zina aramunce,
kishin da ba'a so shine kishin haramta halak, ki haramtawa mijinki abinda kike da tabbacin Allah bai haramta masa ba,
ki damu kanki akan binciken wayarshi, da wayarshi tayi k'ara ki kai hannu zaki d'auki, idan yayi wanka zai fita ki dame shi da tambayar inda zaije,
idan yayi dare bai dawowa ba ki sakawa kanki zargi yana wajen wata, haka idan ya tashi k'ara aure ki damu kanki da al'umma,
ki hana kowa zaman lafiya,
bayan kin san Allah ya halatta mishi k'arin aure, dan da farko ma cewa akayi ku auri mataye bibbiyu, uku-uku,
hurhud'u sai dai idan bazakuyi  adalci a tsakaninsu ba saiku auri d'aid'aya,
baya ga haka akwai Hadisin da yazo cikin Fathul Bari Jiz'i na 9 babi na 325 Annabi tsira da aminci su k'ara tabbata a gare shi,
yayi mana bayanin illar mummunan kishi da cewa " _Innal gaira latu uk'usuru asfalal wajibun a'ala_
ma'ana lalle mace mai zurfaffan kishi irin wanda ba'a so bata iya gane inane zurfin rijiya yake,  wato bata ganin gabanta,
daga kishin ya motsa saita yanke hukuncin da zatayi danasani daga baya, duk matar da take da makahon kishi bazata tab'a rabuwa da nadama da danasani a rayuwarta ba.

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now