4

6K 421 55
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_

_DEDICATED TO_
'''BEST FRIEND FOREVER & EVER'''
*ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA*
~(UMMU AMAAN)~

4⃣

Cikin tashin hankali Neehal yayi saurin shiga gaban Nauman ya tare Najwah,
bakinshi na rawa yace " lafiya Najwah....!?

"Please Neehal ka matsa kaban waje,
" me zakiyi....!?

"Abinda ya kamata, tayi maganar tana k'ok'arin zagaye Neehal,
da sauri ya rik'o ta had'i da cewa " what's wrong with you Najwah...!?

"Wallahi duk wanda yake k'ok'arin shiga tsakanin mu koya kawa b'araka,
ko yayi k'ok'arin saka maka wani abu a ranka da zuciyarka bazan tab'a kyale shi ba,
ko da kuwa ni da kai na ce, bazan tab'a kyale kai na ba,
" calm down Najwah ba abinda kike tunani ko tsammani bane,
" meye idan ba haka ba...!?

" Da kunne na naji yana yi maka maganar wata mace,
naji shi yana k'ok'arin cusa maka ra'ayin mata biyu,
yana k'ok'arin cusa mummunar cousin sister shi,
wacce tayi kwantai babu miji balle mashinshini,
" kai koda aure Neehal zayyi wallahi yafi k'arfin ajin wannan 'yar k'auyen,
ina taje, ina aka santa, da har zatayi tunanin shiga zuciya Neehal ...!?

"Wacece ita dame take tak'ama...!?

" Neehal d'ina yafi k'arfin ajin ta, ya wuce ya had'a jikinshi da wannan abun kyamar,
abin kyankyami da ita, dan kawai tayi secondary school tana school of nursing,
shine har zatayi tunanin Neehal zai so ta, shegiya abin kyankyami da ita,
cikin rawar murya Nauman yace " please Naj....!,
a hasale Najwah tace " kai dalla can rufewa mutane baki,
uban wa saka banzan bakinka cikin magana ta....!?

Cike da tsantsar mamaki Neehal da Nauman suka kalli Najwah,
jin tana neman zagin Nauman,
" shege munafuki annamimi, dama na dad'e ina tunanin hakan,
na jima ina zarginka wallahi, nasan kwata-kwata baka so na da Neehal,
nasan da kana da yadda zakayi da tuni kayi ka shiga tsakani na dashi,
to ta Allah ba taka ba, daga kai har wacce ta turo ka kake yi mata campaign d'in,
ka kwaso uban tsayo zalalo-zalalo kamar me,
ka kwaso uwar k'afar zunk'ai-zunk'ai da uban k'aton kai kamar na majagaban tururuwa,
kazo har cikin gidana, parlor na, ka zauna saman sofa ta tana cin dunduniya ta,
kana munafurta ta,
shege munafuki, fajiri wallahi in banda ina jin kunyarka da sai na zagi uwarka da ubanka,
" enough....! enough....! Najwah baki da hankali ne ko kin yi hauka.....!?

"Eh..! Neehal nayi hauka, bani kuma da hankali indai a kanka ne,
indai akan abinda zai rabani da kai ne zan iyayin abinda yafi haka Neehal,
wallahi ba wannan bak'in munafukin mai fuska irin ta kafiran farko ba,
wallahi ko Hakeem, Naseem, Haleem, Naleela ne suke neman shiga tsakanin mu,
zan taka musu birki irin mai k'arar nan k'uuuuu, zan iya shatawa kowa layi akanka,
dan haka bani guri,
" Najwah ki fita daga parlor'n nan tun kafin ranki ya b'aci,
" bazan fita ba Neehal, wallahi har sai na d'auki mataki akan annamimin dake neman shiga tsakani na da farin cikin rayuwa ta,
tayi maganar tana d'aga wuk'ar hannunta, had'i da k'ara damk'e ta gam,
tana yiwa Nauman wani irin kallo mai cike zallar k'iyayya،
gaba d'aya jikinta ya gama jik'ewa sharkaf da gumi, idonta yayi jajir,
gashin kanta yayi buzu-buzu, kanta a k'asa ta d'ago pure red eyes d'inta ta kalli Neehal,
tace " bani waje....!, tana fad'a tana cije hak'oranta, she look so terrorist,
duk da kasancewar Nauman cikekken namiji mai cikekkiyar k'ira irin ta cikakkun maza,
hakan bai hana shi tsorata da ganin yadda Najwah ta koma kamar mai aljanu ko 'yar cult ba,
sai dai mamakinta da al'ajabinta sunfi tsoran da yake ji yawa nesa ba kusa ba.

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now