15

5.1K 326 77
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*

*ZAN CIGABA DA YIN POSTING RABO AJALI IN SHA ALLAH, AMMA MATUK'AR AKA CIGABA DA SIYAR MIN DA NOVELS CIKI ABU HUD'U TABBAS ZANYI D'AYA, KO NA MAYAR DA NOVELS D'INA NA KUD'I, KO NA YI APPLICATION NA MAYAR DA NOVELS D'INA CIKI, DUK MAISO YAJE PLAY STORE YAYI DOWNLOADING KO NA MAYAR KAN YOUTUBE DUK MAISO YAJE CAN YA SAURARA, KO NA DAINA RUBUTUN KWATA-KWATA GABA D'AYA DAN BAI YIWA KURA DA SHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, NI INA NAN INA SHAN WAHALA WANI NA CAN NA AMFANI DA WAHALA TA, BASIRA TA BA*

_DEDICATED TO_
'''BEST FRIEND FOR EVER'''
*ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA*
             ~(UMMU AMAAN)~

1⃣5⃣

Da k'arfi Neehal ya sanya k'afa ya hankad'ata, ta fad'a baya ta mugu da k'asa,
batare daya damu da fad'uwar da tayi ba, yace " uban me kike shafa min a fuska ...!?

Bata kalle shi ba, bare ta tanka mishi, ta tashi zaune tana kakke jikinta, had'i da murza inda ta buge,
" ba magana nake yi miki ba...! nace uban me kike tofa min....!?

Yayi maganar cikin zafin rai yana tunkaro ta, cikin tsoro da fargabar ganin yadda yake tunkaro ta tace " babu komai,
" bazaki fad'a min abinda aka baki kike shafa min a fuskata ba....!?

Yayi maganar cikin masifa yana tsatstsare ta da ido, " "Allah ba komai....!,
" idan babu komai uban me kike tofa min....!?

"Wani lak'anin aka baki kike shafa min danki mallake ni....!?

"To bari kiji imma wani suddabarun da surkullan kuke yi akai na wallahi na fi k'arfin ku,
and you will never have me as husband, fool villager kawai,
ya fad'a yana huci kamar zaki,
" Allah babu abinda nake tofa maka ko nake shafa maka,
" to uban me kike min....!?

Cikin yarinta tace " kallanka kawai nake yi...!,
" kallan me kike yi min to...!?

Ya fad'a yana d'aukar step zuwa gareta, " nima ban sani ba, kawai dai naji ina san kal....! kasa k'arasa maganar tayi ganin yadda ya tsare ta da ido,
" uhummm ina jinki, " kawai naji ina san kallanka  ne....!, ta fad'a cikin fad'uwar gaba,
kasak'e Neehal yayi yana kallanta batare dayace komai ba,
" 10yrs in love...!?

Ya fad'a idanshi kanta , tare da komawa ya zauna saman foam, had'i da sauke ajiyar zuciya,
" you're 10yrs an you're in love with unknown person, yayi maganar yana murmushin gefen baki had'i da shafa k'asunbarshi cike da mugunta,
can k'asan mak'ogwaronshi yace " SO.....!, yarinya kinyi mugun ganganci,
jin ya fad'i kalmar so yasa Neelah yin murmushi had'i da cewa " dama Abpa yace wata rana zaka so ni, sai da akayi 'yan sakanni kana Neehal ya fahimci maganarta,
aiko yadda kasan an tsira mishi allura ya zabura had'i da cewa " what....!?

"Ni zan so kin ko wa....!?

" Eh! tace tana kallanshi! " wonder shall never end, shi baban naki ne ya fad'a miki wata rana zan so ki....!?

"Eh! ta kuma bashi amsa, " God forbid...! Allah ya tsare ni da sanki,
" wallahi Allah nayi muku alk'awari ke dashi, har abada har na mutu bazan tab'a sanki ba,
I said it now and I will say it for ever & ever bazan tab'a sanki ba,
ke koda gaba k'addara ta k'addara nace miki ina sanki, ko na zo miki da maganar soyayya k'arya nake,
idan har kika ga nace miki ina sanki akwai babban dalili, na zo ne kawai na cimma buri na akanki, amma bawai soyayya ce ta gaskiya ba,
dan haka ki aje wannan a ranki may be gaba yayi miki amfani,
bana sanki ba kuma zan so ki ba, dan k'arshen tab'ewar da zanyi a duniya da kuma walak'anta had'i  da kankanci shine na so ki,
babu wata bak'ar k'addara ko masifar da zata k'ara samu na a duniya kamar AURANKI,
babu wani iftala'in da zai kai min na AURANKI, bani da babbar jarabawa a duniya ta kamar ta AURANKI,
daga kan AURANKI bana jin zan k'ara ganin bala'i sama da wannan.

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now