30

8.6K 499 153
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE, DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI, TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

3️⃣0️⃣

Cikin tashin hankali, kid'ima da matsananciyar razana taja baya tana nuna shi da hannunta,
ta kasa furta koda kalma d'aya sai bakinta dake rawa hak'oranta na kaf kaf,
duk ilahirin jikinta na tsuma kamar mazari,, nuna Neehal ta shiga yi da hannunta ta kasa magana,
kanta ta shiga girgizawa tana cewa " no! no! bashi bane, cikin mamaki Doctor ya kalle ta yace " Doctor NM kin san shine?

"Miji na ne! ta fad'a batare data sani ba,
a kid'ime ta nufi jakarta tayi zaman dirshan a k'asa,
ta zazzage jakar, hannunta na rawa ta d'auki wayarta, tayi dialing number Mamy,
Mamy nayin picking Neelah tace " Mamy ina Neehal?

"D'azu da safe naji Daddy yana sanar dashi zasuyi bak'in turawa daga Landon ya tafi Lagos ya tare su,
naji Neehal d'in yana waya Airport a aje mishi ticket d'in Lagos, amma dai ban sani ba koya tafi,
bata tsaya bawa Mamy amsa ba ta kashe wayar, had'i da fashewa da gigitaccen kuka,
Doctor da nurses nata bata hak'uri amma bata kulasu ba, sai da tayi me isarta sannan ta mik'e,
k'ara shiryawa tayi tsaf cikin shigar operation sannan tace " Bismillah mu fara aikin mu,
jiki a sanyaye Doctor ya kalle ta yace " zaki iya kuwa Neelah naga kamar bakya cikin nutsawarki?

"Bakomai! tace a tak'aice, sai da sukayi awa uku cur sannan suka kammala yi mishi aikin,
ta kalli Doctor tace " ka k'ara yi mishi gwaje-gwajen, a kaishi resting room,
batare data jira abinda Doctor zai fad'a ba ta fice, gidan da aka bata a unguwar Lekki ta nufa,
babu abinda babu a gidan dai-dai da cokali akwai a gidan, 3 bedroom plate ne, da babban parlor & kitchen da dinning area,
gaba d'aya bedrooms d'in da furnitures, haka ma parlor yasha Turkish sofa, d'aya daga cikin bedroom d'in ta shiga,
ta fad'a saman bed ta saki kuka mai cin rai, wanda idan za'a kashe ta bata san dalilin yin kukan ba,
a hankali ta mik'e ta shiga bathroom tayi wanka ta d'auko alwala, sallah ta fara gabatarwa, sannan ta shirya kayanta cikin wardrobe,
ruwan tea kawai tasha ta d'auki key d'in motarta ta fice, sai da Neehal yayi kwana biyar a asibiti sannan ya farfad'o,
tunanin shi komai normal sai dai ba um bare um'um baya iya magana, baya iya tafiya,
ko zama bai iyawa, Neelah ce komai nashi itake yi mishi komai, tun daga kan wanka, wanki saka pampers, ci da sha, ita ke mishi komai na rayuwa,
sai da Neehal yayi wata uku a hospital sannan aka sallame su, a lokacin ya fara zama akan walk chair,
gidanta ta kaishi ta cigaba da kula dashi, a b'angaren Najwah ko yau wata uku kenan har lokacin tana asibiti tana fama da jinya,
yayinda hankali ya tashi akayi ta neman Neehal amma ko d'oriyarshi basu samu ba, anyi cikiya a gidajen TV da redio da kafafen sada zumunta amma shiru,
dole suka dangana aka sanya malamai suna rok'on Allah ya bayyanashi,
duk lokacin da Mamy tayiwa Neelah magana tazo gida weekend sai tace ba dama saboda aiki yayi yawa sosai,
duk wani abu da kuka sani na buk'atar d'an Adam tun daga kan tsarki, wanka, alwala gyaran fuska da sauransu Neelah keyiwa Neehal.

Neelah zaune tana bawa Neehal abinci a baki, ya kafe ta da ido, tsaki taja had'i da dungure mishi kai tace " dalla Malam daina kallo na,
masifaffan banza kawai Allah ne yayi maganinka ya zaunar dakai waje d'aya, tayi maganar tana mik'ewa,
bata jima ba ta dawo d'auke da glass cup ta bud'e bakinshi ta zuba mishi magani kana ta bashi ruwan,
lips d'inshi ta kama ta murd'e da k'arfi tace " shegen bakin rashin kunya da bak'ar magana,
k'ara matse lips d'in tayi tace " bakin k'arya da munafurci, da wannan shegen bakin babu irin cin mutuncin da zagin da ban sha ba,
ta k'arashe maganar tana k'ara murd'e mishi baki, Neehal ya runtse ido da k'arfi, ta tsaya a kanshi tace " ja'iri ko zaka rama ne?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now