27

5.7K 444 109
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

2️⃣7️⃣

Ya bud'e baki zayyi magana idonshi ya sauka akan Nail, Neelam da Nailah,
sark'ewa bakinshi yayi ya kasa furta koda kalma d'aya,  fuskar Neelah ya gani sak a fuskar Nailah,
take gabanshi ya shiga dukan uku-uku k'irjinshi ya shiga harbawa,  ganin yaran ya tabbatar mishi akwai wani abu a k'asa,
muryarshi na rawa yace " Mamy wad'annan yaran waye...!?

" Ina tambayarka kana tambayata dan ubanka nace a ina kayi bautar k'asa....!?

Dayake Neehal d'an duniya ne yasa ya saita kanshi ya kawar da idonshi daga kan yaran ya kalli Mamy,
yana k'ak'aro murmushin k'arfin hali,  while deep down a tsorace yake in banda harbawa babu abinda zuciyarshi keyi,
with full confidence yace " kai Mamy badai har kin manta ba...!?

Fuska Mamy ta k'ara tsukewa idonta kanshi ta kafe shi da ido tana san gano ainahin abinda yake k'ok'arin b'oyewa, 
ganin irin kallan da Mamy keyi mishi yasa shi cewa " Adamawa Yola mana Mamy,
ya fad'a dan yasan Mamy da mantuwa sosai yanzu za'ayi abu yanzu zata manta,
cikin rashin aminta da maganarshi tace " Neehal kada ka raina min wayo,
" Allah Mamy ba k'arya nake yi miki ba badai har kin manta ba...!?

Zatayi magana Najwah ta shigo falon direct kusa da Neehal ta zauna,
tana murza idonta alamun yanzu ta tashi daga baccin tace " yunwa nake ji,
ta wutsiyar ido ya saci kallan Mamy yaga tayi tsaye idonta kanshi ta kafe shi da ido cike da tuhuma,
saurin mik'ewa yayi tare da rik'o hannun Najwah yace " muje kiyi sallah saiki dawo kici abincin,
baki ta zumb'uro tace " ni dai gaskiya yunwa nake ji,  mu fara cin abincin tukunna sai nayi wanka nayi sallah,
yana daga tsaye ya saci kallan Mamy  yaga har lokacin idonta kem a kanshi,  k'ut ya had'iye yawu,
cikin alamun rashin gaskiya muryarshi na sark'ewa yacewa " no muje kiyi sallah, zatayi magana yace " amma kin san ban san gardama ko?

Mik'ewa tayi tana b'ata fuska tayi hanyar fita,  kukan da Neelam ya saka ne ya ja hankalin Najwah kansu,
cike da mamaki ta bud'e baki had'e da cewa " wow!  masha Allah Mamy ina kika samo kyawawan yara?

Ta wutsiyar ido ya kuma satar kallan Mamy still idonta na kanshi,
" am... am Ma... m... y kin... ce... wani.... abu... ne?

Ya fad'a muryarshi na cracking,    " wani abun kaji nace ne...!?

Ta fad'a while idonta kanshi,  " Mamy badai Umairah ce ta haihu ba'a sanar damu ba...!?

"Allah yaran kamarsu d'aya da Neehal da Naufal da Daddy,  macen kuma dake take kama, Najwah ta fad'a tana d'aukar Nailah,
kasancewar Najwah tana bala'in san yara sosai,  Neelam ya matsa yana mik'a mata hannu yace " yi ma,
dariya tayi mishi kana ta sauke Nailah ta d'auke shi, aiko Nail na ganin an d'auki Neelam ya matso,  yana mik'a hannu,
take Najwah taji san yaran ya shiga ranta, Allah ya jarrabe ta da matsananciyar k'aunarsu, " Mamy ya sunansu...!?

Murmushi Mamy tayi mata tace " macen sunana aka saka mata ana kiranta da Nailah,
ta nuna Nail tace " wannan kuma sunan Daddy ne ana ce mishi Nail,  sai wannan rigimammen sunan mijinki ne dashi ana shi ce mishi Neelam,
" wow!  habibi!  I love you,  tace tana shafa kan Neelam,  Mamy tace " san kai dayake shi sunanshi Neehal ko?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now