9

6.4K 451 112
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_

*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*

9⃣

Cikin tsantsar tashin hankali, firgici da kid'ima Neehal ya d'ago kanshi,
ya kalli mutumin dake magana cike da isa wanda ko darajar mai gadin gidan su bai kai ba,
d'an shiru Neehal yayi yana tunani dan a zatonshi baiji abinda mutumin yace ba,
dan haka Neehal ya sake kallan mutanan dake zagaye dasu,
tamkar wad'anda suka aikata wani mugun abun kana Neehal,
ya mayar da kallanshi ga mai garin yace " banji abinda kace ba,
mutumin yayi murmishi a karo na biyu kana yace " cewa nayi mu'a garin mu ba'a zama babu aure,
domin kujewa b'arna yasa yaran mu maza suna da shekara sha shida,
16yrs)  muke yi musu aure yayinda yaran mu mata ke da sheraka,
goma zuwa sha biyu (10 to 12yrs),  yawancin mu duk sai da akayi mana aure kana muke balaga daga baya, bayan munyi auren,
mazan mu da matan mu daka gani anan gaba d'ayan mu haka aka yi mana,
tun iyayen mu da kakanin mu wannan dokar take cikin garin nan,
dan haka koda bak'o ne yazo baya zamar mana a gari babu aure,
dan haka na baka zab'i cikin uku ka d'auki,
na farko kodai ka kira matarka tazo nan ku zauna tare,
ko kuma kayi aure a garin nan cikin mu idan da wanda zai iya bawa bak'o 'yarshi,
sayya baka danya fanshe ka ko kuma mu kashe ka, saboda idan mu bamu kashe ka ba,
kai zaka kashe mu ko kuma ka turo mana 'yan sanda su kama mu dan ku 'yar birni imani da tsoran Allah ba isarku yayi b........!,
tunkan shugaban k'auyen ya k'arasa maganarshi, Neehal yayi murmushi had'i da cewa,
" karka damu bakomai indai dan zuwan mata ta ne babu matsala,
zanzu zanyi waya gida zuwa gobe sai a kawo min ita, 
shugaban k'auyen yace " to..!  to...!  madalla kira ta,
batare da Neehal ya kuma yin magana ba, ya ciro wayarshi cikin aljihu,
yayi dialing number Najwah,
deep down yana tunanin yadda Najwah zata iya rayuwa cikin wannan k'asurgumen dajin,
dan bama za'a kira shi da k'auye ba sai dai daji,
" but I know she can do anything akan ayi mata kishiya,
zata iya zama koda cikin dokar daji ne inda babu mutane da ayi mata kishiya,
yayi maganar cikin ranshi while yana dialing number ta bisa mamakinshi sai yaji wayar not reachable,
k'ara dialing number yayi still not reachable, a k'alla Neehal yayi dialing number Najwah yakai sau 30 but not reachable,
d'ago kanshi yayi yaga gaba d'ayan mutanan k'auyen sun zuba mishi ido suna kallanshi,
d'an muguntun murmushin yak'e yayi wanda iyakacinshi labb'anshi,
hannunshi na kerrrrrma yayi dialing number Daddy,  shima Neehal ya kirashi yakai sau 20 amma baya shiga,
daga Daddy ya kira Mamy sau 20 itama number bata shiga,  ya kira Nauman ko yakai sau 50 bata shiga,
duk danginshi har wad'anda basa magana basa wani zumunci ranar sai da Neehal yayi ta neman numbers d'inshi bata shiga,
kamar daga sama Neehal yaji muryar shugaban k'auyen yana cewa,
"yaro dena wahalar da kanka a banza kana bawa kanka wahala abanza,
saboda bamu da HANYAR SALULA , dan kwata-kwata bamu da hanyar sadawarta,
wata irin fitinanniyar fad'uwa gaban Neehal yayi, cikin tsantsar rud'ewa da zallar tashin hankali ya kalli shugaban k'auyen yace "what....!?

"Ba..... ba... ba... bangane abinda kake nufi ba,
kana nufin kona kira bazata shiga ba....!?

Shugaban k'auyen yayi murmushi had'i da d'aga mishi kai alamar eh,
da sauri Neehal ya mik'e tsaye hannunshi na rawa ya soma daddana wayarshi,
ganin gaba d'ayan wayoyinshi babu services d'in  ya d'auke,
durk'ushewa Neehal yayi a wajen had'i da tallafe kanshi,   shugaban k'auyen yace " yaro kuje kuci abinci ku huta zuwa gobe ma nemeku,
kana ya mayar da kallanshi ga wasu matasan masari,
yace " kuyi hak'uri ku basu sababbin bukkokinku da kuka yi,
inyaso sai ku sake wasu cikin girmamawa matasan suka ce " to ranka ya dad'e,
kana ya kuma kallan Neehal yace " kuje su raka su yanzu za'a kawo muku abinci,
Neehal bai mik'e ba ya cigaba da zaman dirshen, cikin bak'in ciki da takaici yadda kasa an aiko mishi da sak'on mutuwa,
shugaban k'auyen  ya kuma cewa " yaro ka tashi kuje ko....!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now