24

6.6K 410 136
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...! 300*_
_*ABU A HUDU...!*_
*_DA KAMAR WUYA...!_*
_*SAKI NA DAFE...!*_

2⃣4⃣

Murmushi Nauman yayi had'i da cewa " ban san sunanta ba,
Neehal yace " please ka tuna mana, Nauman yayi shiru yana tunani,
amma ya kasa tuno sunan Neelah, kanshi ya girgiza a hankali yana cewa " wallahi na kasa tuna sunanta,
a fili Neehal ya sauke ajiyar zuciya batare daya ce komai ba, har Nauman ya gama cin abincin Neehal bai kuma cewa komai ba,
washe gari Neehal da Nauman suka bazama Neeman admission a Oxford university,
Allah ya taimaki Neehal cikin sati biyu an shiga na uku suka gama komai,
while duk abinda suke Daddy na sane dasu, ido ya zuba musu,
bayan Neehal ya gama komai da komai, ya sanar da Najwah sosai tayi farin cikin jin zasu koma karatu,
koda Neehal ya sanar da Daddy cewa  next week yake son su kuma Dubai makaranta Daddy bai nuna mishi komai ba,
yayi mishi addu'ar fatan alkhairi, ya amsa da amin, bayan kwana hud'u jirgin su Neehal ya d'aga zuwa America.

************************************

Sunkhanni

Duk inda kake tunanin k'unci da matsatsin rayuwa Neelah ta shiga,
sosai take cikin damuwa dan ba hali ta fito ko kewayen bukkarsu sai yara su biyo ta suna yi mata ihun tayi cikin shige,
dole ta koma zaman bukka, ya zama na ko k'ofar bukkarsu bata fitowa,
idan kaga ta fito daji zata je idan tana buk'atar band'aki, ko idan zatayi sallah,
Abpa da Dada na cikin bukka, Neelah ta fito ta nufi daji dan tanasan kewayawa,
bayan ta gama biyan buk'atarta ta taso da niyyar komawa bukkarsu,
dandazon yara wanda a k'alla zasu kai 20 suka shiga binta a baya,
suka yi mata ihuuu tayi cikin shige, wasu na d'iban k'asa suna bud'a mata a jikinta,
wasu na jefanta da duwatsu, haka suka taso ta gaba har bukkarsu suna jefanta da duwatse,
Dada da Abpa suna daga cikin bukka suka fara jiyo ihuuun yara suna cewa " ku bud'e ta tayi cikin shege,
ihooo me abin kunya, ganin yadda yaran suka jiwa Neelah ciwo,
ga jini yana ta zuba daga jikinta yasa Abpa saurin k'arasawa gareta,
ya tsugunna dai-dai tsayinta yana goge mata jinin dake zuba,
cikin muryar kuka Neelah tace " dan Allah Abpa ka barni na bar k'auyen nan,
ka barni nayi nesa da mutanen nan marasa inamani da tausayi,
wad'anda basu san tawakkali ko milk'alil zarratun ba,
Abpa zayyi magana ya jiyo muryar Dada na cewa " Malam tunda nake dakai, tunda kake yanke hukunci akaina har Allah ya kawo mu ka fara yanke hukunci akan Neelah,
ban tab'a bud'ar baki nace maka komai ba, ban tab'a yi maka musu ko nayi jayayya da maganar ka ba,
ban tab'a fitowa na nuna maka hukuncinka akan mu bayyi min ba,
ko yayi min ko bayyi min ba ina hak'uri na amsheshi hannu bibbiyu,
a yau ina san nayi abinda ban tab'a yi ba a iya tsayin rayuwarmu,
ina san na saka maka baki a harkar gida da hukuncinka, ina san na rok'e ka alfarmar daka bar Neelah ta koma birni,
shiru Abpa yayi yana sauraren maganganun Dada harta dasa aya,
yau karo na farko a rayuwarshi daya ji Dada ta kira ainahin sunan Neelah,
haka ta saka baki akan maganar shi, ya d'an dad'e kafin ya d'ago ya kalli Dada yaga tayi mishi k'uri da ido,
a hankali ya mayar da dubanshi ga Neelah, yaga itama ta kafe shi da ido,
murmushi yayi had'i da cewa " shikenan bakomai,
duk da Neelah bata jin dad'i hakan bai hana ta yin tsalle ta fad'a jikin Abpa ba,
ya rungume ta yana dariya yace " kin fa girma yanzu Bingel,
cikin bukkarshi ya shiga ya d'auko takardar da Umairah ta rubuta mishi number,
lokacin da zata tafi ta bashi tace koda ya canja shawara ya kirata,
in sha Allah zata zo ta d'auki Neelah, bukkar Mani me waya Abpa ya nufa,
bayan ya isa sun gaisa da Mani kana Abpa ya mik'a mishi number yace " dan Allah kira min wannan number,
Mani ya amshi number tare da cewa " Malam Liman ka san cikin karkarar nan babu hanyar sadawar kira,
dole sai mun tsallaka rafi munje hayin dutse kana zaka iya magana,
Abpa yace " ashsha bakomai muje, suna tafe suna hira har suka isa,
batare da b'ata lokaci ba Mani ya kira number Umairah,
Umairah na kwance saman sofa kanta saman k'irjin Naufal, yana ta rarrashinta kan tafiyar Neelah,
sosai Umairah ta shiga damuwa tun bayan tafiyar Neelah,
jin wayarta na rori yasa Naufal mik'a hannu ya d'auko ya mik'a mata,
batare data amshi wayar daga hannunshi ba tace " waye....!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now