21

4.8K 294 61
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...! 300*_
_*ABU A HUDU...!*_
*_DA KAMAR WUYA...!_*
_*SAKI NA DAFE...!*_

2⃣1⃣

Kallan juna Naufal da Umairah sukayi cike da mamaki, batare da sunyiwa juna magana ba,
suka bi bayanta, a harabar gidan suka iske ta ruk'unk'ume da jakar kayanta,
a hankali Umairah ta k'arasa inda take rakub'e ta sanya hannu da d'ago Neelah,
jikinta Neelah ta fad'a tana tana sakin kuka tace " na yarda dake sosai nasan bazaki tab'a cutar dani ba,
dan Allah kada ki bari ya k'ara yi min abinda yayi min, dan Allah ki nisanta ni dashi,
cikin mamaki Umairah ta mayar da kallanta kan Naufal suka d'an kalli juna,
kana ta d'ago Neelah tace " kin san shine...!?

Bakin Neelah na rawa cike da tsoro tace " eh shin.....! ganin Neehal ya nufo su fuskarshi d'auke da murmushi,
yasata tsayar da maganar ta, had'i da kafe shi da ido cike da mamaki,
ta jima tana kallanshi tana san tantancewa Neehal ne koba shi bane,
dan taga d'an bambamci a tsakanin su, dan Neehal yana da dimples shi kuma wannan da yayi murmushi bataga kumatunshi ya latso ba,
haka fuskar Neehal akwai gashi (kasumba) a fuskarshi wacce ta kwanto har zuwa hab'arshi,
amma wannan bashi dashi,  ganin yadda Neelah ta kafe Naufal da ido yasata maimaita mata tambayar " kin san shine...!?

Ajiyar zuciya Neelah ta sauke had'i da mayar da kallanta ga Umairah,
tace " a'a yayi min kama da wani bak'in mugu azzalumi ne, sai yanzu na gane bashi bane,
cikin mamaki Umairah tace " mugu...! azzalumi kuma...!?

"Eh...! Cewar Neelah, Umairah bata kuma magana ba ta kamo hannun Neelah suka koma cikin gidan,
ta bayanta Naufal ya zura hannunshi ya rungume ta yana kissing kumatunta, k'uri Neelah tayi idonta kan Naufal bata ko k'iftawa,
dan ganin Naufal tayi tamkar Neehal saboda tsananin kamar da suke yi, ganin yadda Neelah ta saki baki tana kallan Naufal,
yasa Umairah tsammanin ko  dan taga sunyi hug & kissing d'in juna ne,
rolling ido Umairah tayi had'i da sakin Naufal ta kalli Neelah tace " wannan shine miji na sunanshi Naufal Bilal Lagosa,
daga yau ya zama Uncle d'inki, kasa magana  Neelah tayi dan har lokacin tana zaton Neehal ne,
d'an murmushi Naufal yayi yana kallan Umairah yace " k'anwa kika samo mana ne...!?

"Yes..! we will talk letter tayi maganar tana rik'o hannun Neelah,
murmushi Naufal yayi tare da nufar inda Neelah take tsaye yace " ya sunanki....!?

Shiru Neelah tayi ta kasa furta koda kalma d'aya, kallan Umairah yayi yace " ya dai ko k'anwar ta mu bata magana ne...!?

" Tana magana a dai tsorace take ne, kasan akwai rashin sabo, sai a hankali,
kasancewar gidan babban ne yasa ta bawa Neelah tank'ak'amen bedroom,
me d'auke da bathroom & toilet, an k'awatashi da Italian bed complete set, & sofa bed,
cikin bathroom harda tub bath, sosai d'akin ya k'awatu, ta dafa kafad'ar Neelah tana murmushi tace " daga yau nan ne d'akin ki nan zaki rink'a kwana, waccen k'ofar band'aki ne,  ta fad'a tana zaunar da Neelah saman bed,
saurin mik'ewa Neelah tayi cike da tsoro jin gadon ya lotsa tana zama,
" lafiya..!?

Cewar Umairah, cikin k'auyauci tace " yo locawa yayi,
taso tayi dariya amma saita kanne tace " ai haka yake, sunanta kafita, karki ji tsoro ki zauna kinji,
kiyi wanka, idan kin gama ki fito parlor mu ci abinci, Neelah ta amsa da to,
fita Umairah tayi ta nufi bedroom d'in Naufal, Neelah kuma ta mik'e ta nufi k'ofar da Umairah ta nuna mata tace ban d'aki ne,
tsaye tayi sororo tana bin ko'ina na bathroom d'in da kallo had'i da tantamar anya nan ban dak'i ne kuwa,
ganin kwata-kwata bayyi mata kama da makewayi ba, yasa ta rufewa ta koma ta zauna,
har Umairah ta gama wanka ta shirya ta dawo parlor ta zauna tana jiran Neelah amma shiru bata fito ba,
jin shiru yasa Umairah mik'ewa ta shiga bedroom d'in Neelah, koda ta shiga iske tayi zaune k'asan carpet,
" au wai bakiyi wankan ba...!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now