23

5.1K 316 52
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...! 300*_
_*ABU A HUDU...!*_
*_DA KAMAR WUYA...!_*
_*SAKI NA DAFE...!*_

2⃣3⃣

Sai lokacin hankalin kowa yakai kansu Neehal har suka lura da abinda ke faruwa,
cikin kad'uwa Neehal ya sanya duka hannayenshi ya toshe bakinshi,
tare da kwalalo dararan idanuwanshi waje kamar zasu fad'o k'asa,
gaba d'aya mutanen dake hall d'in suka d'ora hannu aka had'i da bud'e baki,
cikin sanyi Basrah ta sanya hannu ta shafo jinin dake zuba daga jikinta,
had'i da kallan jinin, muryarta na rawa tace " it's my blood, tayi maganar tana zubewa k'asa a sume,
cikin zafin nama Neehal ya sanya hannu ya tare ta, cikin k'ank'anin lokaci Ambulance da motar police suka iso wajen a tare,
batare da b'ata lokaci ba aka d'auki Basrah aka sakata cikin motar,
gami da manna mata Oxygen dan sun lura bata numfashi,
yayinda police suka fara cikiniya da Najwah wajen kama ta,
sosai ta shiga turje-turje tana tujewa, wai ita baza'a kamata ba,
ganin ana k'ok'arin tafiya da Najwah yasa Neehal saurin mik'ewa,
ya isa wajen police d'in yana yi musu magana amma ko kallanshi babu wanda yayi,
da k'arfi Najwah ta rik'e Neehal had'i da sanya kuka tana cewa " dan Allah kayi musu magana karsu raba ni dakai please,
wallahi zan iya mutuwa idan suka ce zasu raba ni dakai, suna janta, while Neehal yana binsu,
d'aya daga cikin mutanen dake wajen ne ya isa ga Neehal ya rad'a mishi,
" kayi mata magana, kuma kaima ka nutsu, wallahi in banda ma ita mace ce sun san daraja da k'imar mace da tuni sunyi maganinta,
kayi mata magana ta nutsu ta bari a kamata dan tuhumarta ake yi da laifin kissan kai,
kasan wannan k'asar ba irin k'asar ku bace, ko d'an sarkin Dubai ne yayi abinda tayi sai an kamashi an hukunta shi,
dan haka kayi mata magana karta k'arawa kanta laifin sa'insa da hukuma,
cikin sanyin jiki Neehal ya saki Najwah, yana ji yana gani tana ihuuu tare da mik'o mishi hannu aka dannata cikin motar 'yan sanda,
suka tafi da ita, jikinshi na kerrrrma ya nufi mota, driver na ganinshi ya taso,
gabanshi na dukan uku-uku dan kallo d'aya zaka yiwa Neehal kasan babu lafiya,
batare da yayiwa driver magana ba, ya mik'a mishi hannu, kamar driver yasan abinda yake nufi ya mik'a mishi key d'in mota,
Neehal ya shiga had'i da figar matar kamar wanda zai tashi sama yabi bayan su Najwah.

Lokaci d'aya suka isa police station d'in, da sauri Neehal ya bud'e motar ya fita baiko tsaya rufewa ba,
cikin cell aka saka Najwah, tana ta kuka duk da bata yi danamar abinda ta aikata ba,
hannu ta shiga mik'owa Neehal ta tsakanin k'arfunan cell tana cewa " please heartbeat ka fitar dani daga nan,
bazan iya kwana anan kai kana can ba, kada wata ta bika ku kwana tare,
halin da Neehal yake ciki bai hanashi jin zafin kalmar Najwah ta k'arshe ba,
ido ya kafe ta dashi na d'an lokaci kafin yace " ke kin fi kowa sanin ni ba fasik'i bane,
ba kuma mazinaci bane, wallahi irin abubuwan nan da kike yi suna k'ona min rai Najwah,
da wanne kike san naji yanzu, da k'ok'arin fitar dake daga nan....!?

"Ko da Basrah da kika cakawa wuk'a, ko kuwa da ciwon kan da kike bani....!?

" Allah ya sani kina bani ciwon kai Najwah I'm very tired,
yayi maganar cike da k'osawa, zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu,
had'i da cewa " enough..! enough Najwah, yayi maganar yana kawar da kanshi gefe,
dan be iya kallan kwayar idonta yayi mata fad'a, cikin nutsuwa ya isa gaban DPO dake zaune yana kallansu,
babu irin rok'o da magiyar da Neehal bayyi kan abashi belin Najwah ba amma DOP ya hanashi,
yace " kayi hak'uri bani da ikon baka matarka saboda laifin data aikata yana da girma a dokar k'asar nan,
dole sai an jira anga abinda ya samu Basrah Al-shamry,
babu wani abu da za'a iyayi har sai an jira anga warkewarta,
kana daga baya kuje kotu, idan kuka yi sa'a Basrah Al-shamry ta yafe mata,
ces d'inta zaizo da sauk'i laifinta zai ragu, sai dai kawai kuyi magana da Human Right ta k'asa,
kasancewar tana da hakk'i kan kowanne d'an k'asa, idan aka yi abu koda mutum ya yafe dole Human Right tana da hakk'i,
dole tasa Neehal hak'ura dan duk inda ya buga babu sauk'i, baibar police station d'in ba sai 12:30 na dare, Najwah na ganin zai fita ta fasa kuka, tana kiran sunanshi,
batare daya juyo ba yayi ficewarshi, daga police station direct hospital ya nufa wajen Basrah, ya iske kusan gaba d'aya ahalinsu a hospital d'in,
cikin nutsuwa da sanyin jiki Neehal ya k'arasa wajen ya mik'awa mahaifin Basrah da sauran mazan dake wajen hannu suka gaisa,
suka amsa mishi ba yabo ba fallasa, cikin harshen turanci ya shiga basu hak'uri,
a tak'aice mahaifin Basrah yace " please ka bari ta farfad'o tukunna,
Neehal ya bud'e baki zayyi magana Abbun Basrah ya d'aga mishi hannu,
batare daya kuma magna ba ya koma gefe dasu ya zauna, baibar wajen ba sai da aka kira sallar asuba,
kana yayi musu sallama, ya fita, a masallacin dake cikin hospital d'in yayi sallah kana yayi gida,
duk da yana matuk'ar cikin b'acin rai da damuwa hakan bai hana shi missing Najwah ba,
a parlor saman sofa ya zube had'i da d'aga kanshi sama idanuwanshi lumshe,
kasancewar bai samu bacci ba yasa bai jima ba bacci yayi awon gaba dashi,
cikin baccinshi yayi mafarkin Neelah tsaye cikin mawuyacin hali,
dakyar ta d'ga hannunta ta shiga mik'o mishi hannunta cikin matsanancin kuka,
tana cewa " ka taimake ni, ina buk'atar taimakonka, dan Allah ka taimake ni,
tana daga kwancen tana mik'o mishi hannu yaga wasu irin mutane masu wasu irin halitta,
sun zo kanta suna tuntsura dariya had'i da cewa " taimakon wa kike nema....!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now