31

7K 426 101
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

3️⃣1️⃣

Cike da mamakin mik'ewarshi tsaye ta kalleshi baki bud'e tace " what!  dama ka warke?

"Ina tambayarki kina tambaya ta?

" I said su Neelam yaran waye?

Yayi maganar cikin hargowa da d'aga murya,  hannayenta ta sark'e a k'irjinta idonta cikin nashi,
tana girgiza kanta tace " me hali dai baya tab'a canja halinshi,  ka warke sumul amma ka barni ina yi maka wahala kaje kai da Allah,
a hasale cikin bak'ar zuciya yayi yo kanta tamkar zai yagi naman jikinta d'anye,
" answer me!  yaran waye?

Saurin shiga tsakiyarsu Nauman yayi had'i da sanya hannu ya tokare k'irjin Neehal yana tura shi baya,
kallan hannun Nauman yayi dake saman k'irjinshi yana tura shi baya cike da tsantsar mamaki,
" no!  Neehal don't even think so!, are you forget she's my wife to be?

" I an her we are going to marry so karka kuskura ka soma ko'a mafarki ne,  dan wallahi duk ranar da kayi sake hannunka ya tab'ata a ranar zaka gane waye Nauman Sa'eed Lagosa,
yayi maganar yana huci, hannun Neelah ya rik'e tare da hannun yaran ya fice daga parlorn,  Neelah tabi shi ba musu, 
cikin tashin hankali Neehal ya biyo bayan su yana ihunnn " ki bani amsa su Nailah yara na ne?

Ko kallan inda yake batayi ba,  kafin Neehal ya k'arasa garesu tuni sun shige mota Nauman yaja,
da k'arfi Neehal ya naushi gini yana huci,  saurin komawa cikin gidan yayi ya canja kayan jikinshi a gurguje ya nufi airport,
batare da b'ata lokaci ba ya hau jirgi ya nufi Abuja dan yasan suma can suka nufa,  
Mamy na zaune a parlor Nauman da Neelah da yaran suka shigo,  kallan mamaki Mamy tayi musu tace " to!  lafiya na ganku gaba d'aya,
jiki a sanyaye Nauman ya zauna yana kallan su Nail yace " ku shiga ciki,
gaban Mamy Neelah ta zube had'i da fasa gigitaccen kuka ta rik'e kafafun Mamy tana cewa " am so sorry Mamy,
kiyi hak'uri ki yafe min I know I made mistake but I'm sorry, cikin rashin fahimta Mamy ta sanya hannu ta d'ago Neelah daga durk'ushen,
yayinda gaban Mamy ya shiga fad'uwa dan a zatonta wani mugun abun Neelah tayi, "lafiya meke faruwa Neelah?

"Please Mamy kiyi hak'uri ki fahimce ni kiyi min uzuri please,  " what's going on here?

Cewar Daddy yana shigowa parlor,  " ban sani ba, nima abinda nake san sani kenan,  kallan Neelah Daddy yayi dake ta faman kuka kamar ranta zai fita yace " meya sameki Daughter?

"Kuyi hak'uri Daddy abisa cutar da zuciyoyinku danayi,  kallan juna Daddy da Mamy suka yi, fuskokinsu d'auke da zallar mamakin maganganun Neelah,
" kin san me kike cewa kuwa Daughter?

"Wanne irin cutar da zuciyoyinmu kika yi!?

Muryarta na sark'ewa tace " na.....! d'an shiru tayi sannan tace " na... b'oye.... muku Neehal da....  k'in.....  sanar..... daku.... halin da... yake... ciki....!, ta fad'a muryarta na rawa, 
kallan juna Daddy da Mamy suka yi a karo na biyu, sosai mamaki ya k'ara fitowa k'arara kan fuskokinsu,
kallan Nauman Daddy yayi yace " Nauman yi min bayani yadda zan gane please,
cikin girmamawa Nauman ya kwashe komai tass tun daga farko har k'arshe ya sanar dasu Daddy kamar yadda Neelah ta sanar dashi a Lagos,
" Mamy kin tuna ranar da aka kira ni daga Lagos aka ce min akwai patient inje!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now