28

5.5K 428 86
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

2️⃣8️⃣

Neehal jin kalaman Doctor yake yi tamkar al'mara, ko a mafarki,  ido kawai ya zubawa Doctor har ya dasa aya,
kafad'arshi Doctor ya d'an tab'a yace " kana ji na kuwa?

Cikin tashin hankali da zallar firgici Neehal ya d'agawa Doctor kai alamar eh,
duk ilahirin jikinshi na kerrrma, durk'ushewa k'asa yay had'i da d'ora hannunshi aka ya fasa rikitaccen kuka mai gunji tamkar mace,
" innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,  Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan min ha,
da sauri Nauman ya k'araso wajen yana tambayar abinda ke faruwa,
jikin likitan a sanyaye yayiwa Nauman bayanin komai, shi kanshi Nauman ya shiga firgici da jin abinda likitan ya fad'a,
cikin sanyin jiki ya durk'usa gaban Neehal,  muryarshi na rawa yace " kayi hak'uri Aboki....!,
" hak'uri fa kace Nauman,  wanne irin hak'uri zanyi?

"Shikenan bazan tab'a ganin kwai na ba,  bazan ga gudan jini na ba,  shikenan bani da rabon haihuwa,
na shiga uku Nauman wallahi ina cikin wani hali,  rayuwata tana cikin garari,
batare da Nauman yayi magana ba ya mik'ar da Neehal yakai shi office d'inshi,  sannan ya fito ya dawo wajen Doctor,
Nauman yace " yanzu babu yadda za'ayi, babu wata dabara da kake ganin za'a iya yi?

Kanshi ya girgiza cikin karaya yace " am sorry  Doctor Nauman amma gaskiya munyi iyakar yin mu,
dole sai anyi hakan, shiru Nauman yayi kanshi k'asa, yana tunanin mafita,
" kai zaka saka hannu ayi mata aikin...!?

"Wa ni?

Nauman ya fad'a yana zaro ido,  Doctor yace " eh ba naga kai ma Lagosa Family bane,
" eh cousin Brother mijinta ne,  amma ba ruwa na,  kada daga baya tazo tana kuka da ni,
tace ma had'a baki aka yi dani aka cuce ta,  " please Dr Nauman bamu da lokaci ka taimaka kayi signing,
Nauman ya fuzar da iska yana kallan Doctor yace " ana baka kana k'in karb'a,  ni fa bak'in saka hannu nayi ba, ina tunanin abinda zaije ya dawo gaba ne,
kai baka san halin matar nan ba wallahi tana iya bi na da wani sharrin,
dan haka ba ruwa, nayiwa su Daddy waya na sanar dasu yanzu zasu k'araso, Nauman na gama rufe bakinshi suka shigo,
cikin girmamawa Nauman ya tare su yayi musu bayanin komai,
" tayaya akayi hakan ta faru...!?

Daddy ya tambaya,  Nauman yace " wallahi Daddy ban sani ba,  "yanzu ina Neehal d'in yake...!?

"Yana office d'ina,  Daddy ya juya zai bar wajen, Doctor yace " please Alhaji ka saka hannu a paper da za'ayi mata aikin,
d'an jimmm Daddy yayi sannan yace " muje mijinta ya saka hannu,
Nauman ya kalli Doctor yayi mishi alamar ka gani ko,  k'asa suka iske Neehal zaune ya had'a kai da gwiwa,
saurin k'arasawa Daddy yayi yana cewa " Subhanallah,  Neehal lafiyarka kuwa...!?

"Daddy bani da rabon haihuwa,  bani da rabon ganin 'ya'ya na kamar yadda kuka ganmu,
wayyo na shiga uku Daddy Najwah ta cuce mu, cike da mamaki suka kalli Neehal  gaba d'ayansu,
Daddy yace " me ya faru?

Neehal zayyi magana Doctor yace " please Alhaji a saka hannu dan bamu da ishashshen lokaci,
karb'ar takardar Daddy yayi daga hannun Doctor ya mik'awa Neehal yace " kayi signing,
kanshi ya girgiza hawaye na zubo mishi yace " no bazan iya ba,  Daddy bazan iya saka hannu a cirewa Najwah mahaifarta ba,
idan nayi mata haka banyi mata adalci ba,  Daddy yace " hakan da zakayi shine adalci a gare ta,
dan idan baka saka hannu ba,  ba mahaifarta kad'ai za'a rasa ba,  ita kanta za'a rasa,  jin ance ana iya rasata yasa Neehal amsar paper da sauri ya saka hannu jin,
likitan ya amsa ya fita da sauri,  ba'a jima ba su Naufal suka k'araso,  tare da 'yan gidansu Najwah,
duk sukauyi jugum-juhum cikin jimami,  ba'a fito da Najwah ba sai bayan sallar ishaa, rest room aka wuce da ita su Neehal na biye da ita,
jikinshi na rawa ya zauna bakin gadon da take kwance yana shafa kanta,
sai wajen k'arfe 9:10pm na dare Najwah ta farka,  a hankali ta soma motsi tana yamutsa fuskarta,
hannunta me d'auke da cannula ta sanya ta dafe kanta, ta d'an jima a haka kafin ta bud'e idonta,
tana bin d'akin da kallo,  ganin gaba d'aya dangi a d'akin yasata ware idonta dake a kumbure,
Mamy, Daddy, Babanta,  Mamanta da yayyanta,  Umairah da Naufal, duk tabi kowa da kallo,  a hankali ta fara kalle-kalle tana neman Neehal,
hannunsa ya d'ora saman nata,  a fili ta sauke ajiyar zuciya, ganinshi kusa da ita,
ganin yanayinshi da kammaninshi,  da yadda tashin hankali da damuwa suka fito k'arara a fuskarshi,
yasa Najwah girgiza kanta,  tana k'ok'arin tuna abinda ya faru sannu a hankali komai ya dawo mata,
cikin rawar jiki takai hannunta ta shafo cikinta, jin wayam,  yasata saurin mik'ewa zaune,
ta shiga fisge k'arin ruwan dake jikinta,  tana fisge cannular jini ya soma zuba,
bata damu da jinin datake zubarwa,  ta sanya duka hannayenta tana shafa cikinta cikin tsantsar firgici,
jin cikin wayam bakomai yasata fasa gigitaccen kuka da kusan gaba d'aya asibitin sai da ya amsa,
kanta Neehal ya tallafe had'i da d'ora goshinshi kan nata hawaye na gangarowa daga rinannun idanuwanshi,
wad'anda tuni suka canja kala,  dakyar,  ya iya motsa lips d'inshi yace " shhhhhh,  cikin matsanacin kuka ta soma cewa,
" wayyo Allah na shiga uku na rasa ciki na wanda nayi shekara da shekaru ina faman nema,
cike da tsantsar tausayi Mamy ta isa gareta ta sanya hannu ta d'ago ta,  ta zaunar da ita ta shiga rarrashinta,
" wai meye asalin abinda ya faru...!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now