26

6.2K 502 124
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*        

RABO AJALI...!

HAUWA A USMAN
      JIDDARH

2️⃣6️⃣

A steps d'in bene Daddy da Mamy suka yi kacib'us ya dan ya jiyo kiran da take yi mishi,
a zatonshi ma ko ba lafiya ba,  " lafiya Taheerah?

Batare data kula da tambayar da yayi mata ba ta rik'e hannunshi tana ja zuwa bedroom d'in,
suna shiga bedroom d'in ta saki hannun Daddy ta nufi inda yaran ke kwance,
Nailah nata faman kuka jikin Mamy na rawa ta d'ago Nailah da Neelmah tace " Alhaji kalli irin rowar nan dake jikinka,
irin ta Naufal da Neehal dasu Suhaima, kai da bakinka ka sanar dani mahaifinka nada irinta,
haka duk wanda ya had'a jini da irinku yana da irinta,  kuma wannan itace babbar shedar da kuke gane jininku,
murmushi Daddy yayi irin na manya yace " au wai ke har yanzu kina kokontar kasancewar su jininmu...!?

"Ko kuwa kina tamtama ne kina raba d'aya biyu...!?

"Wallahi Taheerah tun ranar da aka haifi yaran nan jiki na bani jini na ne,
" to amma Alhaji meye abin b'oye mana kamar bamu ne muka haife su ba...!?

Ta k'arasa maganar tana rushewa da kuka, " in banda abinki meye abun damuwa da d'aga hankali..!?

Hawaye Mamy ta goge muryarta na rawa tace " wato baki suka had'a da matarshi,
aka kawo Neelah bayan yayi mata cikin ya bayyana shine suka kawo ta da sunanta taimako,
" kinga yaron yanzu sai anayi ana d'auke musu kai,  in sunyi abu ayi kamar ba'a sani ba,
shine ake zama dasu lafiya, ki saka musu ido idan Allah ya ara mana rai da lafiya koma meye muna zaune zamu ji, za mu gani,
kamar yadda nayiwa Neehal,  " Neehal!  me kuma Neehal d'in yayi....!?

Numfasawa Daddy yayi kana ya kwashe duk abinda ya faru a Dubai ya fad'a mata, har yadda suka nemi makaranta a America suka koma,
cike da mamaki Mamy tace " what?

"Amma Alhaji kayi shiru ka zuba musu ido meyasa baka yi mishi maganar ba...!?

"Shi ya kamata yayi min maganar tunda shi na haifa ba shine ya haife ni ba,
kuma shine a k'ark'ashin ikon na,  tunda bai fad'a min ba yana ganin hakan ya dace me zance ni?

Zatayi magana yace " karki damu muna zaune cikin ruwan sanyi zamu kama su a hannun mu, nasan yadda zanyi da Neehal,
ajiyar zuciya Mamy ta sauke tace " to Allah ya kyauta,  Daddy ya amsa da " Amin, bayan kwana biyu tafiya ta kama Daddy zuwa Dubai tare suka tafi da Mamy,
suna zaune a masaukinsu Daddy ya ciro wayarshi yana dannawa yace " bari na tsoka ni d'anki,
cikin rashin fahimta Mamy tace " wanne?

"Neehal ya bata amsa yana dialing number shi,  bugu d'aya Neehal yayi picking,
cikin girmamawa ya gaida da Daddy,  ya amsa cike da kulawa,  Daddy ya d'ora da cewa " Son kana ina ne..!?

Batare da kawo komai cikin rashin ba yace " ina Dubai mana Daddy,
Daddy yace " gani a Dubai d'in ai ni da Mamy,  rass gaban Neehal yayi muguwar fad'uwa,
da sauri ya kalli Najwah dake zaune saman cinyarshi tayi filo da kafad'arashi,
cikin tsoro ta d'ago kanta ta kalle shi suka had'a ido,  " kuna ina nazo na same ku son?

Cikin in'ina Neehal yace " am uhnnn ina... ina...  Daddy yayi saurin cewa " ka fad'a min mu da kanmu zamu zo mu ganku dan munyi missing d'inku sosai,
Mamy ta k'agara ta ganka tun daga Airport tace mu wuce wajenku dan a matse take taga d'anta,
ido suka k'ara had'awa da Najwah sai zazzare ido suke cike da tashin hankali,
Daddy yace " son kodai bakayi missing d'inmu bane dan naga kamar baka san ganin mu?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now