13

4.6K 269 11
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*

*ZAN CIGABA DA YIN POSTING RABO AJALI IN SHA ALLAH, AMMA MATUK'AR AKA CIGABA DA SIYAR MIN DA NOVELS CIKI ABU HUD'U TABBAS ZANYI D'AYA, KO NA MAYAR DA NOVELS D'INA NA KUD'I, KO NA YI APPLICATION NA MAYAR DA NOVELS D'INA CIKI, DUK MAISO YAJE PLAY STORE YAYI DOWNLOADING KO NA MAYAR KAN YOUTUBE DUK MAISO YAJE CAN YA SAURARA, KO NA DAINA RUBUTUN KWATA-KWATA GABA D'AYA DAN BAI YIWA KURA DA SHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, NI INA NAN INA SHAN WAHALA WANI NA CAN NA AMFANI DA WAHALA TA, BASIRA TA BA*

_DEDICATED TO_
*AISHA ALIYU GARKUWA*

1⃣3⃣

Zuciyarshi ta soma tafasa tana suya cikin zafin rai da tuk'uk'in zuciya Neehal yayi kansu,
d'aga idon da Neelah zatayi suka sauka akan Neehal dake dumfarosu,
a zabure kamar mayunwacin zaki, a matuk'ar razane Neelah ta kurma uban ihuuun,
had'i da yunk'urawa da niyyar guduwa, ihuun da tayi ne yasa gaba d'aya yaran suka nutsu,
Neehal da suka gani ne yasa su soma kuka suna ja baya suka had'e waje d'aya suna kuka,
" dalla ku min shuru dan banku, yayi maganar cike da hargawa,
tsit sukayi suna zare idanuwa, Neelah yace " uban wa yace ku shigo min d'aki....!?

" Neelah...!, suka fad'a gaba d'ayansu,
" idan tace ku shiga wuta zaku shiga...!?

Ya kuma tambayarsu, gaba d'ayansu suka amsa da "a'a,
" ba nace karku k'ara shigo min d'aki ba....!?

"Dan Allah kayi hak'uri, suka fad'a cike da tsantsar tsoro ganin kwata-kwata,
babu alamar annuri a fuskar Neehal,
k'ara tsuke fuska yayi tamau yace " wallahi daga yau duk ranar dana k'ara ganinku a d'aki na,
sai kun gane kuranku, dan sai na kusa kashe ku da azaba,
shegu ibilisai shaid'anu kawai, daga yau duk ranar data kuma cewa ku zo,
d'aki na kuyi wasa kuka kuma zuwa sai na yanka ku da wuk'a,
cike da tsoro yaran suka zazzaro ido, yace " kun san yadda ake yanka kaza da saniya ko....!?

Babu wanda ya iya magana saboda tsoro, ya cigaba " daga yau kuka k'ara shigo min d'aki yanka ku zanyi kamar yanda ake rago da kaza dan ubanku,
" ta kwarankwatsi bazamu k'ara higowa ba, aradun Allah kotace mu zo bamu zuwa,
suka fad'a cikin k'auyenci suna k'ara ruk'unk'ume junansu,
cikin tsawa yace " get out...!, yayi maganar yana nuna k'ofar fita,
aiko kamar sunji abinda yace suka fara turereniyar fita, suna tattake junansu,
Neelah ta yunk'ura da sauri zata fice, cikin zafin nama Neehal yayi wuf ya rik'o ta gam,
tana jin ya rik'e ta ta soma kuka tana kiciyar kwacewa shiko yayi tsaye yana kallanta,
har yaran suka fita kaf kana yayi jefa da gefe ta buge kai k'um da bango,
taji buguwar sosai amma saboda tsoran da take yasa ta kanne,
ya isa inda take duk'e ya zuba mata kyawawan marika gudu biyu,
saboda tsananin azabar marin bata san sanda ta saki fitsari ba,
dan tunda Neelah take babu wanda ya tab'a ko dungurinta balle duka,
aiko ta gigice sosai tsoronshi ya kamata,
" kafin inje in dawo ki tabbatar kin gyara min d'akina tsaf kamar yadda yake,
wallahi idan kika sake na gama abinda nake baki gyara ba,
saina nad'a miki na jaki, nayi miki tsinannan dukan da sai kin kasa tashi,
kwala-kwalan idanuwanta ta zuba mishi tana kuka batare data ce komai,
" dan ubanki baki ji na...!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now