5

6.4K 429 66
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

'''Wattpad:-HauwaAUsmanjiddarh'''

_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_

5⃣

Cikin b'acin rai Najwah tace  " wallah.....!,
a zuciye Neehal ya daka mata tsawa ganin tana neman mayarwa da mahaifiyarshi magana,
" dalla malama dakata, tsaya da wannan banzan maganar taki,
ki rufewa mutane baki.....!, hannu Mamy ta d'aga mishi had'i da cewa " ina ruwanka....!?

"Itama 'ya tace kamar yadda kake d'ana, ni bana sarakunta da Najwah da Umaira,
dan haka karka k'ara shiga tsakanin mu idan muna magana,
" amma Mamy ai bai kamata kina magana tana magan......!,
" nace babu ruwanka, ka daiji abinda na gaya maka ko...!?

Kanshi k'asa cike da girmamawa yace " naji Mamy,
murmushi tayi mishi had'i da cewa " Allah yayi albarka, ya amfani rayuwa,
" amin ya Allah Mamy, " ina zuwa bari naje nasa a shirya abinci a dining,
dan muma bamu ci ba, sai muci gama d'ayanmu,
bata fi minti goma ba ta dawo tace " tom Bismillah,
batare da yayi magana ba ya mik'e ya nufi dining, har Mamy ta juya da niyyar  barin parlor'n,
taga Najwah bata ko motsa ba, Mamy tace " ke baki jin yunwar ne...!?

"Ina ji...! tace cikin shagwab'a, Mamy tace " to baki ji nace kuzo muje mu ci ba....!?

"Naji..! yanzu nake san tashi, " ok to maza tashi muje, a hankali ta mik'e tabi bayan Mamy,
saboda tsawar da Neehal ya daka mata yasa take fushi dashi,
dan haka bata zauna kujerar kusa dashi ba, ta zauna a wacce ke fuskantar shi,
wanda tuni yasan da hakan amma yayi watsi da ita,
gaba d'ayansu kowa ya zauna masu aiki sukayi service kowa abinda zai ci,
Mamy ta kalli Suhaila tace " ah'ah ina kuma UMAINA...!?

Da k'arfi gaban Najwah ya buga jin sunan wacce Mamy ta kira,
dakyar ta had'iye abincin dake bakinta,
cikin rawar murya tace " Mamy Umaina ta zo....!?

Kafin Mamy ta bata amsa Suhaira tayi karaf tace " ai tana nan tun last week,
dariyar yak'e Najwah tayi kana tace " ayya...!,
UMAINA cousin sister d'in Neehal ce 'yar k'anwar Mamy ce,
duka-duka bazata wuce 12 to 13yrs ba, amma dayake tana da jikin girma idan ka ganta,
sai rantse takai 14yrs, UMAINA yarinya ce k'arama amma saboda jahilin kishin Najwah,
ba k'aramin kishin Umaina take bala'in ji ba, kasancewar Umaina yarinya ce mai bala'in san jiki da san mutane, had'i da shegen surutu da hira,
yadda take lik'ewa Neehal ko su Suhaima basa shishshige mishi haka,
idan Najwah na k'aunar mutuwarta tana k'aunar ganin Umaina a rayuwar ta,
tayi mugun tsanarta fiye da kima, fiye da tunanin mai karatu,
muddin tasan Umaina tana gidan bata barin Neehal yazo,
ko da zaizo sai ta tabbatar da bata nan, sun fita dasu Suhaila,
yanzu ma harga Allah data san Umaina na nan da bazata tab'a yin gangancin zuwa gidan ba,
" wow....! happy family...!, Umaina tace tana k'arasowa wajen fuskarta d'auke da murmushi,
" Mamy shi ne ko a kira ni....!?

Tayi maganar tana diddira k'afa cike da shagwab'a irin ta 'ya'yan hutu,
" sorry daughter yanzu nake tambayarki,
" but Mam......!, bata k'arasa ba saboda ganin Neehal,
tsalle ta buga cike da murna tace " wonderful..!, YAYA NAH....!,
tayi maganar tana nufarshi, aiko numfashin Najwah ya fara sama-sama,
wanda yasa mak'ogwaronta sark'ewa, hakan yayi sanadiyyar kwarewarta,
da sauri da sauri ta fara tari tana haki,  cikin hanzari Suhaima ta zuba ruwa a glass cup ta mik'a mata,
hannu biyu ta saka ta amsa da sauri ta kai bakinta jikinta na rawa da kerrrrma,
hawaye ta hanci ta baki, idanta yayi jajir kamar wacce akayiwa hayak'in barkono,
" ayya...! sorry my in low, Umaina tace,
a hankali tarin ya lafawa Najwah amma har lokacin bata bar gumi da hawaye ba, while idanta jajir,
duk wajen Neehal ne kad'ai yasan dalili da sanadin kwarewarta,
amma ya basar yayi kamar bai fahimta ba,
Umaina tana murmushi ta k'arasa wajen Neehal, had'i da rungume shi ta baya,
tayi mishi kiss a goshi tace " I misses you my sweet Bro..!,
cike da tsokana yayi murmushi had'i da cewa " I missed you too sister like no other,
ido Najwah ta tsurawa hannun Umaina dake saman wuyan Neehal,
tana caccaka wuk'ar hannunta wacce take seti da cokulan cin abincin,
idanta k'am akan Umaina da Neehal, duk da sanyin AC dake wajen bai hana gumi jik'a mata jiki ba,
" Sweet Bro wai ina alk'awarin mu....!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now