10

5.6K 376 47
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_

*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*

_DEDICATED TO_
*AISHA ALIYU GARKUWA*

1⃣0⃣

Dai-dai lokacin da aka shafa fatihar D'AURIN AUREN NEEHAL DA NEELAH,
Najwah ta farka a firgice daga bacci had'i da kurma uban ihuuuu,
cikin tsantsar tashin hankali ta duro daga kan tamfatsetsen gadon da take kwance,
ta zube k'asa batare data kula da fad'uwar datayi ba ta mik'e zambur,
ta nufi k'ofar fita daga bedroom d'inta while tana cigaba da ihuuuun cike da tsoro jikinta nata kerrrrrma yana b'ari,
kacib'us sukayi da Mamah (mahaifiyarta) wacce ta nufo d'akin jikinta na rawa sakamakon jin ihuuuun Najwah!,
ganin Najwah bata kula da ita ba tana k'ok'arin fita yasata saurin rik'ota,
had'i da cewa " ke lafiyarki kuwa....!?

Bakin Najwah na rawa ta fara k'ok'arin yin magana had'i da yin nuni da hannunta zuwa saman bed,
kallan gadon Mamah tayi taga bakomai kana ta mayar da kallanta ga Najwah,
ta kuma tambayarta a karo na biyu,
" lafiya!  meke faruwa dake....!?

Cikin kerrrrrma Najwah tace " Mamah Nee....Nee....  ha...l, tayi maganar a rarrabe,
ido Mamah ta zaro waje cikin rashin hankali tace " meya same shi, wani abun ne ya same shi....!?

Ta jerawa Najwah tambayar a lokaci d'aya, cike da tsoro,
still kasa magana Najwah tayi, illa Neehal!.... Neehal...!  datake ta faman fad'a,
gumi ya jik'ata sharkaf duk da sanyin AC dake d'akin,
ganin yanayin da Najwah ke ciki yasa gaban Mamah ya shiga fad'uwa yana dukan uku-uku,
dan a zatonta wani mugun abun ne ya samu Neehal,
cikin tsawa Mamah tace " wai dan ubanki bazaki fad'a min abinda ya samu Neehal d'in ba...!?

Bakin Najwah na rawa tace " ma.. far.... ki na... yi...,
tsoki Mamah taja had'i da cewa " aikin banza kawai,
tayi maganar tana k'ok'arin fita da sauri Najwah ta rik'eta gami da sanya kuka,
tana cewa " wallahi Mamah mummunan mafarki nayi akanshi,
kuma kinga tunda ya tafi fa bai kira ni ko sau d'aya ba,
k'uluwa Mamah tayi sosai dan kwata-kwata ta tsani halayen Najwah,
" dalla can ni gafara ki bani waje, mara kunya kawai, dan mijinki ya tafi kwana d'aya bai kira ki ba shine kike wannan abun...!?

"Banza sakarya mara wayo, kwana d'aya kawai da tafiyar miji, shine kike hauka....!?

Tayi maganar a zafafe,  jin abinda Mamah tace yasa Najwah k'ara marairaicewa tare da k'ara sautin kukanta sosai,
ta kuma rik'e Mamah gam "please Mamah ki fahimce ni mana,  ba yadda za'ayi Neehal yana lafiya,
ya tafi harya kwana wani daren ya k'ara yi batare daya kira ni koya kira wani ba,
yadda Najwah tayi maganar yasa jikin Mamah yin sanyi ta d'an yi shiru tana tunani,
Najwah ta cigaba da magana " kuma haka nan naji gaba na na fad'uwa,  jiki na yana bani tabbacin wani mummunan abu yana shirin faruwa dani koma ya faru,
jiki na yana bani kamar yana tare da wata mace, tayi maganar cikin sanyi tana kallan tails  while bata bar kukan ba,
d'a da mahaifi sai Allah, take Mamah taji tausayin Najwah ya kamata, a hankali ta d'ora hannunta saman kafad'arta,
kana ta soma magana cikin sanyi,
" kiyi addu'a dan itace maganin komai da duk wata masifar dake tunkaro mutum,
walau ya sani walau bai sani ba, ki kuma kasance mai kyautatawa mijinki zato a koda yaushe,
Najwah zatayi magana Mamah tayi sauri cewa " no! jeki yi alwala kiyi sallah ki sanar da mahaliccinki, majib'ancin lamuran mu, mai yaye mana k'unci da damuwarmu matsalarki,
cikin sanyin jiki Najwah ta d'aga kai, Mamah ta shafa kanta had'i dayi mata murmushi tace " good girl, kana ta fita,
maimakon Najwah ta shiga bathroom tayi alwala kamar yadda mahaifiyarta ta sanya ta,
sai ta koma saman bed ta zauna tana sharar hawaye had'i da sak'a da warwara.

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now