32

9.1K 470 123
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

3️⃣2️⃣

Najwah dake tsaye tamkar mutum mutumi numfashinta ya soma sama da k'asa yana k'ok'arin d'aukewa,
cikin wahalallan yanayi ta dafe k'irjinta da hannunta d'aya while tana nuna Neehal da d'ayan batare data ita furta koda kalma d'aya ba,
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,  Mamy ta fad'a tana tafa hannu, idonta kan Neehal,
shiru Daddy yayi kanshi k'asa ya kasa d'ago kanshi ya kalli Nauman da Neelah,
bakin Neehal na rawa yace " wai me ke faruwa ne?

Cikin matsanancin kuka Neelah tace " Allah ya isa tsakani na dakai,  yanzu in banda su Mamy sun zo da tuni ka cuce ni kayi min FYAD'E A KARO NA BIYU,
"What?

"Ni?

"Lalle kin cika bak'ar munafuka annamiya,  ni zaki yiwa sharri Neelah?

A zuciye Nauman ya shak'e shi yana huci kamar mahaukaci,  yace " k'arya kake d'an rainin hankali,
bayan abinda idonmu ya gane mana har kana da bakin magana,
tsohon munafuki kawai,  wallahi dama na dad'e ina zargin akwai wani k'ulli dake ranka game da matar da zan aura,
a hasale Neehal ya hankad'a Nauman baya zuciyarshi na tafasa yace " ga ka nan munafuki,
wanda bai tsoran Allah, kana neman auran matar wani bayan da auren wani akanta,  naushi Nauman ya kaiwa Neehal a fuska,
had'i da kamashi da kokawa yana cewa " karya kake yi, sai dai idan kaine baka tsoran Allah,
tsohon kwarto d'an iska kawai da gani ka dad'e kana b'ata 'ya'yan mutane sai yau Allah ya toni asirinka,
maganar da Nauman ya fad'a tayi mugun b'atawa Neehal rai, jikinshi na rawa shima ya naushi Nauman a ciki, 
ya cakume shi suka kaure da kokawa tututur-tututur,  Neehal na cewa " wallahi idan baka fita harkar ta ba sai na ga bayanka,
idan ka k'ara shiga rayuwata sai nayi ajalinka......,
tassssss tassssss Daddy ya kwad'awa Neehal mari, kafin Neehal ya gama dawowa hayyacinshi Daddy ya shiga dukanshi tako'ina ido rufe,
" ka bani mamaki Neehal, ashe dama mutumin banza ne kai ban sani ba?

"D'an iska,  mazinaci, fasik'i,  Ina maka kallan na Allah, ashe kura ce da fatar akuya?

"Muna yi maka kallan biri kana yi mana kallan ayaba, muna yi kallan dankali kana yi mana kallan rogo, yau iskancin naka ya wuce ko'ina yazo har cikin gida?

"In my own house, under my rupe?

Dukan da Daddy keyi mishi bai damunshi kamar maganganun da yake fad'a,
ji yake tamkar yana watsa mishi wuta, ganin Daddy na neman islata Neehal yasa Nauman rik'e shi yana bashi hak'uri,
dakyar Daddy ya daina dukan Neehal, ya juya zai fita, har ya kai bakin k'ofa ya juyo ya kalli Neehal yace " ka kwashe inaka-inaka ka bar min gida na yanzu-yanzu,
bazan zauna gida d'aya da mazinaci ba,  ya k'arasa maganar yana ficewa fuuuu, Mamy ta tallafo Neelah tana k'ara rufe mata jikinta da bedsheet,
suna gaf da fita ta juyo ta kalli Neehal ido ciki ido, ta sakar mishi shu'umin murmushi, had'i da kashe mishi ido d'aya, ta d'age gira d'aya,
kululun bak'in ciki ne ya sanya Neehal zubewa k'asan tiles, ya dafe kanshi da duka hannayanshi,
zuciyarshi na tafarfasa, ji yake kamar ya shak'e kanshi ya mutu, " yanzu shikenan ta jawo min zubewar mutunci a idon iyaye na?

RABO AJALI...!Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum