1

14.4K 553 43
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

_Am back again Alhamdulillah Allah yayi min dawowa, na dawo muku da sabon labari na mai k'unshe da abubuwa da dama, Allah yasa zai nishad'antar daku ya kuma fad'ar daku_

'''Ina k'ara mik'a sak'on gaisuwa da godiya ga masoya na masu bibiyar littattafai na a koyaushe, ina matuk'ar godiya sosai nagode da Addu'o'inku'''

1⃣

*LOKACI NE*
_Masoya masu goyan bayanmu a da yaushe, masu san shek'e masge kwarkwatar idanunsu, da san kwakwale damuwarsu, da sanya bak'in cikin su facewa, su kwamaso sink'i-sink'in dariya, annashuwa da sassanyan murmushi kan fuskarsu, su antayawa ruhinsu salama, su sanbad'awa zuciyarsu yalwa, masu san farin ciki wajen karatun littattafan Hausa? to ku matsu kusa, dan nesa tazo kusa, ga shahararriya, hazik'a, fasihiyar, mai san kasancewar ku cikin annuri, wacce ta saba kawo muku nagartattun litttattafanta masu dad'i, wacce ta kware wajen rubuta dad'ad'an labaru tun daga kan wanda ya k'unshi nadama, kuku,tausayi, cin amana, da nagartacciyar soyayya mai yalwa mai sanya tsoho ko tsuhuwa su tuna da jiya samartakarsu da 'yan matancinsu ya motsa,_
_ta sake dawo muku da wani sabon salon littafinta mai k'unshe da abubuwan mamaki, al'ajabi, kala-kala, wa'azantar da ban tausayi gami da sanya zuciya tsinkewa, wanda zai nishad'antar daku, ya d'ebe muku kewa ya sanya masu hawan jini, sauka, masu ciwon zuciya darawa,_ _*LOKACI NE* shine sunan littafin, wanda *ZUWAIRAT UMMU MARYAM* tayi bajakulin fasaharta da basirarta wajen antayo muku dashi, *LOKACI NE*_
_zaku biyu naira d'ari biyu (200) kacal domin samun labarin da karantashi akan 200 kacal domin samun k'arin bayani sai ku tuntub'i wannan number +2348106102727_

*LOKACI NE*
*ZUWAIRAT UMMU MARYAM*

Zundumemiyar mota k'irar Land Range Rover evoque 2020,
tayi parking a harabar shoprite dake garin Abuja Nigeria,
a k'alla anyi wajen minti biyar da fakawar motar kafin cikin isa,
tak'ama, izza gwarjini da haiba matuk'in motar ya zuro santala-santalan kyawawan fararen k'afafunshi,
wanda suke cikin takalmin Berluti Oxford,
cikin nutsuwa ya zuro su waje,
an d'auki minti biyu zuwa uku kafin ya fito gaba d'ayanshi,
" masha Allah, shine abinda na iya furtawa ganin santalelen matashin saurayi,
mai cike da tsantsar haiba da kamala,
wanda da gani bazai wuce 25yrs a haife ba,
idanshi ya lumshi ya shak'i daddad'ar iskar duniya mai cike da nagarta,
sanye yake cikin sky blue na d'anyan farin men boyel material,
hannunshi sanye da expensive watch, takalminshi na world men, sai hular kanshi kalar takalminshi,
hannuwanshi zube cikin aljihun wondanshi,
ya taka cikin takunshi mai tafiya da hankalin ma'abocin kallanshi,
zuwa d'aya b'angaren gaban motar fuskanshi cike da k'ayataccen murmushi,
ya sanya kyakkyawan hannunshi ya bud'e murfin motar,
had'i da mik'a hannunshi na dama ga wanda ke zaune cikin motar,
kyakkyawan hannu na gani na mace sanye da zubunan diamond,
ta d'ora saman hannunshi kana ta fito tana kallanshi ido cikin ido kyakkyawar fuskarta k'unshe da yalwataccen murmushi,
kai da ganin irin kallon da suke aikawa junansu ko ba'a fad'a maka ba,
kasan sun jima cikin tafkin so da k'aunar junansu,
kasan suna matuk'ar son junansu,
hannunta ta sak'ala cikin nashi kana suka taka zuwa cikin shoprite d'in,
duk wanda yayi musu kallo d'aya sai yayi sha'awar k'ara yi musu kallo na biyu,
idan kuma kayi musu kallo na biyu sai kayi sha'awar dauwama kallan zak'ak'uran masoyan har abada.

B'angaren kayan kwalliya suka fara nufa still suna sak'ale da junansu,
tamkar wani zai kwace matashi, koya kwace masa ita,
yaran dake binsu da basket na zuba kaya shi kanshi mamakin zallar son da suke nunawa junansu yake,
sai da ta jidi kayan shafe-shafe da goge-goge,
san ranta kana suka nufi b'angaren k'ananan kaya da kayan bacci,
yadda kasan zasu bud'e shago haka take jidar kayan kamar ba gobe,
cikin so da k'auna ya kalle ta da rikitattun idanuwanshi masu kama dana mashaya,
cikin zazzak'ar muryarshi mai kamar ana busa sarewa,
yace " meye saura my Queen?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now