18

5.3K 333 45
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

*MASU SIYAR MIN DA NOVELS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA*

1⃣8⃣

Kallan Neelah Jauro yayi cike da zallar tausayawa yace " matsalar mutanen garin nan ce,
Abpa yace " dan Allah Jauro jeka inda kake san zuwa, ka fad'a min abinda kake san fad'a min mana,
kasa gaba na sai fad'uwa yake yi, ajiyar zuciya Jauro ya sauke,
tare da cewa " eh kan mutanen mu ne, kasan muddin suka fahimci abinda ya faru da Neelah,
ta shiga uku dan gaba zasu saka ta, bama ita kad'ai ba, har ku,
kai sanin kanka ne idan haka ta faru ga mace a karkarar nan sai taji tamkar ta bar garin,
saboda yadda za'a sako ta gaba daga ita har iyayenta, musamman idan suka gane GUDUWA MIJINTA YAYI YA BARTA....!,
a nutsu Abpa ya sauke numfashi had'i da kallan Neelah,
wacce tayi lamo a cikinshi tana mayar da numfashi, yace " bakomai akwai Allah,
Ubangiji yaga da niyyar da nayi ai, kuma Allah ya sani na bashi auren Neelah ne,
ba dan komai ba sai dan na taimake shi, na tsairar dashi, na kuma ceci rayuwarshi amma tunda shi haka yaga ya dace ya saka min dashi,
ai shikenan ya kyauta, Abpa ya k'arashe maganar hawaye na gangaro mishi,
" Abpa kuka kake yi....!?

Cewar Neelah cikin sanyin murya, ido ya k'ura mata batare da yayi magana ba,
hawayen na cigaba da gangaro mishi,
cikin sanyin jiki Neelah ta sanya hannu ta shiga goge mishi hawayen dake zubowa kan kumatunshi,
had'i da cewa " ka daina kuka Abpa ni ma na daina, nama warke na daina jin zafin,
k'ok'arin k'ak'aro murmushin k'arfin hali yayi ya mannawa fuskarshi,
yace " karki damu kinji Mamana...!?

A hankali ta d'aga mishi kanta tana murmushin itama,
sosai Jauro yaji tsananin tausayin su yayi mugun kamashi,
cike da tausayawa ya kalli Neelah yana murmushi yace " karki damu babu komai,
in sha Allah gobe zuwa jibi zaki warke garau, ki rink'a zuwa gad'a da wasa wajen k'awayenki,
amma kada ki sake ki fad'awa kowa abinda yayi miki kinji Bingel....!?

Cikin sanyin murya ta d'aga mishi kai had'i da cewa " to, "yauwa Bingel ki rink'a shan jik'on maganinki,
kanta ta kuma d'aga mishi, kana ya mayar da kallanshi ga Abpa yace " to Malam ni zan wuce idan da wani abun sai a kira ni,
" nagode sosai Jauro Allah ya saka da alkhairi, me za'a bayar na magani.....!?

Murmushi Jauro yayi had'i da cewa " ka barshi bakomai  nima ai 'ya ta ce,
" ashsha ayi haka....!?

"Amma yi, cewar Jauro yana fita daga bukkar, Abpa yace Allah ya bar zumunci,  Jauro ya amsa da " amin,
da sauri Dada ta had'a kara da k'irare ta kunna wuta, cikin k'ank'anin lokaci ta dafa ruwan ta juye takai bayan bukkarsu,
kana ta koma bukkar ta sanar da Abpa ta d'umama ruwan,
" Mama na tashi kije kiyi wanka, rau-rau tayi da ido kwalla na k'ok'arin zuba mata,
tace " Abpa bazan iya taka k'afa ta ba, da zafi sosai,  cikin tausayawa Abpa yace " yi hak'uri ki daure ki k'ok'arta,
ba musu ta soma k'ok'arin mik'ewa dakyar tana runtse ido had'i da cije leb'e,
bazata iya mik'ewa tsaye sosai ba, dole daga duk'e kamar me ruku'u ta d'an d'aga k'afar da nufin dakawa,
" wayyo Allah na tace tana fashewa da matsanancin kuka,
" Allah da zafi Abpa bazan iya ba, " sannu Mama na, ki daina kukan, bari na d'aukeki,
kafin tayi magana Abpa ya d'auke ta cak, ya kaita har inda ruwan zafin ke aje,
kana ya juya ya bar wajen, Dada da kanta ta cire mata kayan jikinta,
kana tace " to shiga ciki ki zauna, ido Neelah ta zaro a matuk'ar razane gami da cewa " cikin ruwan zafin Dada....!?

"Eh.. baki ga da magunguna a ciki ba, ki shiga ki zauna, kuka ta sanya tana cewa " Dada'am k'onewa zanyi idan na shiga fa,
batare da Dada tayi magana ba ta kama ta, ta zaunar cikin ruwan zafin,
tare da danna ta sosai, bak'ar azaba ce ta sanya Neelah kurma uban ihuuu,
had'i da fashewa da gigitaccen kuka tana cewa,
" Dada dan Allah kiyi hak'uri ban k'arawa, Allah da zafi sosai, dan Allah ki cire ni,
banza Dada tayi da ita har sai da taji ruwan ya wuce kana ta zubar dashi,
ta canja mata wani ruwan zafin, batayi kuka sosai kamar na farko ba,
sai da Dada ta canja mata ruwan zafi sau uku, duk suna hucewa kana ta kyale ta,
tun a cikin ruwan Neelah ta soma gyangyad'i, saboda taji dad'in jikinta sosai,
da kanta ta tafa a hankali ta shiga bukka ta canja kaya, kana Abpa ya bata abinci ta d'an ci kad'an,
shima sai da Abpa ya matsa mata sannan taci tasha magani, bata dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita.

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now