8

6.3K 386 91
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_

*DEDICATED TO*
'''BEST FRIEND FOR EVER'''
*ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA*
_~(UMMU AMAAN)~_

8⃣

Saboda tsantsar tsoro da zallar tashin hankali Neehal kasa motsi yayi,
ya tsaya tsaye cak had'i da zuba mata ido tana k'arasowa gareshi,
cikin zafin rai da ta d'aga wuk'ar da niyyar burmawa Neehal k'irjinshi da ita,
bayyi yunk'urin guduwa ko matsalawa ba yana nan tsayen cak yadda yake,
idanshi kanta, had'a idon da Najwah tayi da Neehal ne yasa ta tsaida hannunta cak,
a dai-dai k'irjinshi a firgice ta kalli hannunta da wuk'ar ke rik'e kana ta kalli Neehal zuwa k'irjinshi,
sai a lokacin hankali da nutsuwarta suka dawo jikinta,
ta fuskanci abinda take da niyyar yi wanda yasa ta saurin yin jifa da wuk'ar gefe,
tana yarfe hannunta had'i da durk'ushewa k'asa ta toshe kunnenta da duka hannunta,
duk ilahirin jikinta na rawa gami da tsuma, ta sanya wani irin kuka mai cin rai tana cewa " why...! Neehal why....!?

Ido ya kafe ta dashi batare dayace komai ba, ganin yadda jikinta ke kerrrrrrma,
yana tsuma duk ta furgice yasa take yaji tsananin tausayinta ya lallub'e duk ilahirin jikinshi,
cikin sanyin jiki ya sunkuya kusa da ita had'i da mik'a hannunshi da niyyar ya tab'a ta,
a firgice ta ture hannunshi tare da ja baya a kid'ime tamkar ya d'ora mata bakin wuta,
tana girgiza kanta had'i da kallan tafin hannayenta tace " me nake shirin yi....!?

" Da wad'annan hannayen nayi k'ok'arin kashe farin cikin raina....!?

" Ni da kaina da hannaye na nayi k'ok'arin kashe ka...!?

"Zanyi sanadiyyar tsinkewar rayuwar wanda nafi son ya rayuwa sama da kowa,
nafi so da k'auna sama da kowa, nafi san kasancewa tare dashi sama da kowa,
ni da kaina nayi k'ok'arin kashe kai na da rugujewar farin ciki da annurin rayuwata....!?

Cike da tsantsar tausayawa yasa hannunshi ya jawota jikinshi ya rungume ta tsam,
had'i da shafa kanta yana bubbuga bayanta, batare daya iya furta koda kalma d'aya ba,
" wallahi ba abinda nayi niyyar yi ba kenan, bada sani na nayi hakan ba,
bana cikin hayyacina sanda nayi attempting kashe ka but am very sorry,
kayi hak'uri ban k'arawa in sha Allah I promise,
bayyi magana ba ya cigaba da shafa kanta yana lallashinta,
a hankali ta zame jikinta daga cikin nashi ta fuskance idonta cikin nashi,
bakinta na rawa tace " please abinda na gani a waya yanzu gaskiya ne ko mafarki ne....!?

Tayi maganar tana nuna wayar cike da tsoro, sai da gabanshi yayi gigitacciyar fad'uwa,
kana yace " hu....ummm..... unnnn..... da...ma...!,
cikin k'araji Najwah tace " what....! kana nufin da gaske ne....!?

"Yes..! but I.....!, cikin masifa ta fizge data cikinshi tace " but what Neehal.....!?

"Please calm down I will explain everything to you now,
" explain what....!?

"You have nothing to say,
" please relax an listing to me, idan baki yadda da abinda zan fad'a miki ba na baki damar d'aukar duk matakin daya dace kai na,
" what Neehal bayan abinda ido na ya gani...!?

"Ka zaunar da mace akan cinyarka kana kayi mata alk'awarin aure,
bayan ina duniyar.....!?

Tayi maganar k'asa-k'asa tana nuna kanta,
a hankali ya mik'e tsaye had'i da mik'a hannu zai tab'a ta,
cikin masifa tace " don't dare you touch me,
" wallahi mutuwa zanyi Neehal, mutuwa zanyi, rayuwata tazo k'arshe,
bazan iya rayuwa da kishiya ba, bazan tab'a iya sharing d'inka da wata 'ya mace ba,
kai nawa ne ni kad'ai Neehal, dan ni kad'ai aka halicce ka ba'a halicce ka dan mu biyu ko wata mace ba,
tayi maganar cikin k'araji da wutar ruwan bala'i tana harguwa,
kana a haukace ta isa gareshi taci kwalarshi " wallahi kai nawa ne ni Najwah ni d'aya,
Neehal kai mallaki na ne, kama sawa ranka haka, matuk'ar kana neman zaman lariya da kwanciyar hankali,
karka soma gigin yiwa Najwah kishiya idan ba haka ba dukkan mu zamu mutu,
danna gwammaci mutuwar mu kan rayuwa da wata tsakiyarmu,
Neehal bana san kishiya bana san kishiya, tayi maganar da k'arfi tana jijjigashi,
ganin yak'i cewa komai ya tsaya kawai yana kallanta ya k'ara hasala ta,
tace " da gaske kenan auren zakayi....!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now