3

6.5K 440 28
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

_DIDECATED TO_
*AISHA ALIYU GARKUWA*

3⃣

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
Neehal ya fad'a yana durk'usawa gaban Umaima,
hannunshi na rawa yakai hannun jikinta da nufin ya d'ago ta,
gigitacciyar k'ara Najwah ta saki tare da cewa " karka kuskura ka soma tab'a ta,
wallahi idan hannunka ya tab'a jikinta sai na kashe ta,
sororo Nauman yayi had'i da zubawa Najwah ido cike da tsantsar mamaki,
ya kasa yin yunk'urin komai,
batare daya d'aga kanshi ya kalle ta ba, ya kai hannunshi jikin Umaima ya tallafo ta,
cikin k'unar zuciya Najwah ta dafe goshinta gami da runtse idonta da k'arfe,
kana ta bud'e idanta tare da jingina kanta jikin bango tana bugawa da d'an k'arfi,
had'i da taune lips d'inta, tace " baka ji ba ko....!?

Banza yayi da ita, yana jijjiga Umaima gami da kiran sunanta cikin tashin hankali ganin bata motsi,
"Umaima....! Umaima....!! a kid'ime ya kalli Nauman dake tsaye kamar an dasa shi,
yace " dalla Malam kayi wani abu mana kana ganin bata numfashi,
yayi maganar yana goge jikin dake zuba daga kan Umaira,
da k'arfi Najwah ta shiga buga kanta jikin bango,
yayinda data kafe idanta tarrr kan Neehal dake rik'e da Umaima,
kanta ya fashe jini ya shiga zuba, taji mugun ciwo amma bata daina buga kanta ba,
while idanta daya rine ya tamkar gauta yana kan Neehal tarrr,
ganin bashi da niyyar sakin Umaima yasa Najwah nufarshi gadan-gadan,
dan gaba d'aya idanta ya gama rufewa, hankalinta ya gushe,
ta fita fita daga cikin nutsuwarta, cikin masifa ta nufi shi tana cewa " baka ji ba ko....!?

Ganin bai motsa ba, bai kuma kalle ta ba, ya k'ara hasala zuciyar Najwah cikin matsanancin zafin rai tace " nace ka sake ta, karka sake bari ko farcanka ya tab'a ko...!?

Tayi maganar a haukace, cikin zafin rai da bak'ar zuciya Neehal ya d'aga jajayen idonshi ya kalle ta tare da cewa " idan nak'i me zakiyi....!?

Kwalbar ta kuma wawura tana ihuun kuka tace " wallahi sai na kashe ta, kai nawa ne ni kad'ai, babu wata 'ya mace data isa ta rab'e ka balle har tasan dad'in ni'imar jikinka,
tayi maganar tana nufar Neehal,
da sauri Nauman ya wuf ya shiga tsakiya yayi saurin amsar Umaima daga hannunshi,
ganin ta tafi luuuuu ya d'agawa Neehal da Nauman hankali,
cike da tsantsar firgici Nauman ya kara hancinshi kan nata jin numfashinta baya fita,
yasashi saurin mayar da hancinshi saitin zuciyarta,
cikin tsantsar tsoro Nauman ya d'ago idonshi ya kalli Neehal,
a kid'ime Neehal ya zaro kwala-kwalan idanshi waje ya zaro su kamar zasu fad'i k'asa,
abinka dama dame dara-daran idanu,
cikin tashin hankali yace " ba dai ta mutu ba.....!?

Yayi maganar out of sense,
da sauri Nauman ya mik'e ya danna kwararrawar kiran nurse, & emergency,
ba'a d'auki lokaci ba wani Doctor da nurse's biyu suka shigo lokaci d'aya,
da sauri Nauman da sauran suka sungumi Umaima aka shigar da ita Emergency room,
durk'ushewa Neehal yayi a wajen had'i da dafe kanshi,
yana sauraren bugun zuciyarshi,
shiru kawai yayi amma deep down shi kad'ai yasan ainahin abinda yake ji cikin ranshi,
yasan in banda yana matuk'ar san Najwah da tuni yayi maganinta ta yadda zata gane kuranta,
amma babu yadda zayyi ya iya hora ta saboda tsananin son da yake yi mata,
b'acin ranshi ma da yake nuna mata yana yi ne kawai, yana yin k'arfin hali ne,
amma bawai dan san ranshi yake yi mata hakan ba,
dan duk irin laifin data yi mishi daya kalle ta sai giyar santa ta kwashe shi har ya manta da laifin da tayi mishi,
ganin halin dayake ciki yasa Najwah durk'usawa cikin sanyin jiki da nufin ta tab'a shi,
da sauri ya mik'e tsaye dan karta tab'anshi,
balle har tayi galaba kanshi, dan yana san nuna mata kuskuranta,
ya dad'e yana kai komo gami da sunturi cikin office d'in Doctor Nauman,
kafin Nauman ya shigo da sauri Neehal ya tare cikin rawar baki yace " ya jikin nata...!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now