6

5.2K 405 49
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
       _JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_

'''DEDICATED TO'''
*AISHA ALIYU GARKUWA*

6⃣

Cikin tsantsar tashin hankali da zallar firgici Neehal ya d'ora hannunshi saman bakinshi had'i da zaro dadaran idanuwanshi waje,
bak'on al'amarin da Neesah taji ne yasa tsayawa cak a sunkuyen da take,
hannayenta duka biyun saman fuskarta cike da mamaki,
dan tunda Neesah take bata tab'a sanin zafin mari da duka a rayuwar ta ba sai yau,
dan haka ta diririce gaba d'aya ta fita daga hayyacinta,
cikin rawar jiki Neehal ya k'arasa ga Neesah ya sanya hannunshi ya d'oga ta,
cikin shagwab'a Neesah ta kalli Neehal had'i da sanya kuka,
kamar k'aramar yarinya haka Neesah ke kukan cike da shagwab'a,
" I'm very sorry Neesah....!, cikin zafin rai Najwah tace " au baku daddara ba kenan....!?

Bai kula da maganar da Najwah take yi ba yace " kiyi hak'uri Neesah please,
cikin kuka tace " please kai ni bedroom d'ina,
" kam bura uba wallahi baki isa ba, a gaban nawa kike nufin zai shigar dake bedroom,
ni kuma na tsaya sokoko ina kallanku ko me....!?

Daga Neesah har Neehal babu wanda ya kula Najwah, idanshi kan Neesah yace " ina ne bedroom d'in naki....!?

Da hannu Neesah ta nuna mishi, yana rik'e da ita ya nufi hanyar data nuna mishi,
gaba d'aya idan Najwah ya gama rufewa bak'in kishinta yakai mak'ura,
jikinta na rawa ta sha gabansu tana huci tace " wallahi sai dai idan bana raye ne zaka shiga bedroom da wata 'ya mace,
amma muddin ina raye hakan bazata tab'a faruwa ba,
pure red eyes d'inshi ya d'aga ya zubawa Najwah cike da zallar bak'i ciki,
da takaicin halayyarta yace " gafara Najwah.....!,
" wallahi bazan matsa ba sai dai idan gawa ta zaku fara tsallakewa ku wuce,
" I said move, ki matsa ki bani hanya, yayi maganar cikin d'aga murya,
kuka Najwah ta sanya tana cewa " Allah ko kashe ni zaka yi bazan tab'a bari ka shiga bedroom da wata 'ya mace ba,
cikin zafin rai yace " haka kika ce....!?

"Eh....! ta bashi amsa cikin matsanancin kuka,
" who is she please....!?

Neesah ta tambaye shi, cike da jin kunya yace " she is my wife,
sosai Neesah ta zaro ido had'i da cewa " what....! she is your wife....!?

"Yes, yace kanshi k'asa, d'an guntun murmushi tayi had'i da cije lips tace " ayya no karka damu,
kuje kawai mayi magana letter Neesah ta fad'a tana shafa k'irjin Neehal,
cikin ranta kuma tace " I will definitely tech her a lesson,
ganin yadda Neesah ke shafa k'irjin Neehal tana cije lips yayi masifar d'agawa Najwah hankali,
a haukace Najwah ta kuma yin kan Neesah da niyyar da cakume ta,
da sauri Neesah ta k'ank'ame Neehal  had'i da cewa " hey...! you idiot fuck your self,
waye ubanki cikin k'asar nan har da zaki shigo villa house ki mare ni,
na kyale ni sannan ki k'ara wani yunk'urin duka na,
ina tunanin kina hauka ne ko kuma kin samu tab'in hankali,
then...! get out from here ko in saka k'atti su fitar dake yanzu,
ta k'arasa maganar tana cusa hannunta cikin k'irjin Neehal,
da k'arfi Najwah ta runtse idonta cike da zallar bak'in ciki tace " mari kau na mari banza, ko kina buk'atar k'ari....!?

Cikin murmushi Neesah tace " oh! yeah karki damu ko mari nawa kike so kiyi min kiyi kawai kanki tsaye,
revenge day has come,
kana ta mayar da kallanta ga Neehal had'i dayi mishi kiss a baki tace " kaje mayi magana letter,
kanshi kawai ya iya d'agawa, ya taka da nufin d'aukar files d'in dayazo dasu,
Neesah tace " no ka barsu zamuyi magana,
bayyi iya cewa komai ba ya fita, da sauri Najwah tabi bayanshi har tana neman fad'uwa,
zuciyarshi na bugawa da k'arfi da k'arfi ya bud'e motarshi ya shiga,
yana ganinta tana nufarshi yayi saurin jan motar yabar wajen,
da sauri itama ta hau motar data zo da ita ta rama mishi baya da gudu,
a hankali yake jan motar idan ka ganshi sai ka rantse babu komai cikin ranshi,
amma can k'asan zuciyarshi Allah kad'ai ya san meke faruwa,
cikin nutsuwa ya bud'e motar ya fito batare daya rufe ta ba yayi shigewarta part d'inshi ya rufe,
dai-dai lokacin Najwah tayi parking jikinta na kerrrrma ta fita daga cikin motar tayi part d'inshi da gudu,
har tana yin tuntub'e,
jin k'ofar rufe yasa ta shiga bugawa tana kiran sunanshi,
Neehal kuwa dan kar yaji bugun k'ofarta da kukanta ya karya mishi zuciya,
yasa shi shigewa bedroom had'i da rufe k'ofa,
zama k'asa Najwah tayi tana rusa uban kuka had'i da bugun k'ofar da iya k'arfinta.

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now